Part 15

197 10 2
                                    

*GUDUNA AKEYI*


*NA*

_MUNEERA_

PAGE 15




Jikin ta har kyarma yake tace masa mamy na mamy ta motsa
   Ba tare da ya tsaya ba ya sake ta ya nufi Dakin
  Ita Kuma ta Kira Dr, wanda Yana zuwa yayiwa mamy allurar Se gashi ta koma bacci
  Nasir da Abubakar a tare suka rungome juna yayin da ita Kuma ilham tana gefe tana sakar musu murmushi
  Nasir da Abubakar a lokaci daya suka fice Dan yin wurin Dr Dan Jin Karin bayani game da jikin mamyn
   *WANENE ABUBAKAR*

alhaji sani Abubakar mai turare shine da daya tilo da me Marta sarkin katsina ya Haifa Matan sa hudu Amma fa sani kawai ya Haifa Matan sun hada da hajiya zubaida (giwar sarki) Se hajiya Kareem (mama) Se hajiya Suwaiba Se Kuma hajiya Amina(fulani) fulani itace amarya Bayan mai martaba ya dade Yana rokon Allah ya bashi haihuwa Allah be bashi ba
   Rana daya Allah ya nufi fulani da samun ciki wanda wanan ciki ba karamin murna mai martaba yayi dashi ba yayin da sauran Matan sarki suma suka nuna sunyi murna Amma fa ta ciki na ciki Dan dukan su haka suka hadu suka dinga yin asiri Akan cikin banda Suwaiba itace Sam ba ruwan ta sedai duk wani asiri da akewa ciki cikin nan yaki zubewa har ya cika wata Tara fulani ta haife kyakyawan Dan ta namiji wanda Hakan yasa hankalin wasu a masarautar ya Kara tashi ba iya Matan sarki ba harma da kanen sarki saboda yanzu me martaba ya samu magaji
  A idon me martaba kuwa kowa nuna kaunar sa yake da Taya murna Amma a Bayan ido kowa harin rayuwar Dan yake, ranar suna anyi budirin da ba'a taba yin sa ba a cikin masauratar d'a yaci sunan mahaifin mahaifiya sa wato Muhammad ake masa lakabi da sani

  ***

Shekarar sani biyu a duniya wanda duk Wata kulawa hajiya Suwaiba mutuniyar arziki ke bashi fulani ta 'Kara samun wani cikin wanda Hakan ya Kara dagawa kowa hankali ciki na cika wata Tara fulani ta santalo kyakyawar y' arta mace wace da ta haife ta kallo daya ta samu damar yi mata ta furta Allah yayi Mata albarka, Allah ya dauke ran abinsa mutuwar ba karamin jijiga me martaba tayi ba saboda ya dauki son duniya ya dorawa fulani da take Haifa masa Yara.
  Bayan shekara biyu da rasuwar fulani Suwaiba ce ta cigaba da kula da yaran biyun sani da Kuma kanwar sa Fatima.
  Ana haka itama Suwaiba ta samu ciki wanda hatta me martaba Bata fadawa ba Se daga cikin yayi kwari saboda tasan halin cikin masarauta itama Suwaiba ta haifo yaran ta y'an biyu hassan da usaina.
    Shekarar sani 15 a duniya Amma gata Yana ganin sa wurin me martaba da suwaiba wanan lokacin ne me martaba ya kwanta ciwo wanda wanan ciwon ne yayi ajalin sa har lahira sedai muce in Tamu tazo Allah yasa mucika da Imani

   Bayan rasuwar me martaba da sati biyu aka Bawa 'kanin sa rokon kwaryar sauratar har Se sani wato Dan sarki ya girma Se ya mika masa abunsa
   Ganin ana yawan kawo musu hare hare a cikin gidan yasa suwaiba ta tatara yaran guda hudu tayo kano dasu Kuma bawanda ya hanata hasali ma wasu dama haka suke.
   Suwaiba tabawa sani da Fatima tare da hassan da husaina kyakyawan Tarbiyya wanda yasa suka tashi kan su a hade lokaci zuwa lokaci suna zuwa Kai ziyara masaurautar *wanan kenan*

Sani Bayan Gama makarantar sa ya fara sana'a Seda turare wanda ta hanyar Seda turare Allah ya Buda masa ya zama hamshakin me kudi a Africa Bama iya Nigeria yanada gidajen mai da company Kala kala
   Sani ya Gina babban esatate a jahar kano me suna me turare estate
   Wanda estate yayi gari guda Dan harda titina bangaren sa da ban haka na hajiya suwai ba Daban wace suke kiranta da ammi yayin da na Fatima da husaina daya ne sena hassan Shima Daban, Fatima da husaina ma da sukayi aure basu bar estate din ba anan sani ya basu Suda mazajen su haka hassan ma da yayi aure anan ya cigaba da zama Kuma har lokacin suna zuwa ziyara katsina Kuma har lokacin Ammi ta hanasu yin magana game da mikamin su.

  Sani ya auri Mata biyu wace ta farkon hajiya Salima yar kanin mahaifin sa ce aka aura masa wato sarki me rikon kwarya, yayinda ta biyun hajiya khadija y'ar galadima ce itama yar cousin din mahaifin sa ce aka aure masa ita shekara su kusan goma da aure Amma dukan su ba wace ta taba batan wata Aikuwa ammi ta matsa masa kan ya Kara aure.
   Yaje Somalia wurin wani aminin sa khalid anan ya hadu da Fatima wato mamy Mata me mutunci karamci da Kuma addini.
   Soyaya ta shiga tsakanin Fatima da sani basu wani jima ba kuwa ya aure ta ya taho da ita Nigeria inda taga karamci a wurin dangin sa har ma da ammi sun nuna Mata kauna fiye da tsamanin me tsamani watan Fatima biyu da aure ya samu ciki Kar kuso kuga murna wurin sani da ammin sa da ragowar y'an uwan sa banda Matan sa Salima da Kuma da khadija sosai suka nuna Bakin cikin su ga wanan cikin na Fatima wata ciki Tara cif Fatima ta haifo santalelen Dan ta namiji me kama da ita aka saka masa sunan me martaba kenan baban sani  Abubakar sadik Aikuwa yaga gata tunda ga Kan mahaifin sa har y'an uwan da ammi sosai suke son mamy saboda kyawawan halayar ta Bayan shekara biyu ta Kara haihuwa ta haifi Dan ta namiji akasa masa Nasir Bayan shekara hudu ta Kara haihuwa ta haifi Dan ta namiji again akasa masa Habib Bayan shekara bakwai ta Kara haihuwa ta samu yarinya ta mace me suna Amina sunan mahaifiyar Abubakar ana Kiran ta da Ammal wace suka dauki son duniya suka Dora Mata

    Kenan sani yanada Yara hudu yayin da hassan keda biyar Se Fatima nada Yara biyu mace da namiji Se Kuma usaina nada bakwai
   Sanan sani duka ya basu Jari d company daya
   Ammal maganin gata kasancewar tun daga kanta a gidan gaba daya ba'a Kara haihuwa ba duk da kasancewar halin khadija da Salima da suke nuna musu tsanar su a fili Hakan be hana yaran gidan duka zuwa gaida su ba.

   Abubakar yayi karatun sa ne a India inda ya karanci bangaren zuciya wato(cardiologist) yayin da nasir ya kasance soja Se Habib da yake makaranta a U. S Se Kuma Ammal dake secondary school wace bazata Gaza shekaru 16 ba

   Wata ranar asabar da dangin mai turare gaba daya suka tashi da mumunan labari shine batan Ammal wace aka neme ta Sama ko 'kasa aka rasa sunfi wata suna neman Ammal Amma ba'a ganta ba kafafen yad' a labarai kuwa su social media babu inda ba'a sa cigiyar Ammal ba Amma fa ba'a ganta ba tashin hankali kuwa sun shige shi duk wani bincike da za'ayi anyi shi har suka fawwala Allah.
    Bayan shekara da batan Ammal gaba mamy ta yanke jiki ta fadi aka kaita asibiti wanda duk wani gwaji da ya Kamata Ayi mata anyi Mata Amma babu wata cuta dake damunta.
Har waje an fitar da ita kasa she Daban Daban an kasa gane cutar dake damun mamy haka suka hakura suka dawo gida sunan jinyar mamy ga batan Ammal ga kuma gaba daya dangin sun juyawa mamy har dasu ma baya alhaji sani kuwa mantawa ma yake da mamy yayinda sauran daginsa ma gaba daya suka manta da ita a babin rayuwar su wanda Hakan ya Bawa Y'a'yan matukar mamaki.

   Se y'an uwanta ne na somalia suke zuwa duba jikin ta tare da Mata fatan waraka

Sukuma gaba daya rayuwar su Abubakar kullum cikin Kai musu Hari ake za'a kashe su.

*CIGABAN LABARIN*

*FADIMATOU*

GUDUNA AKEYI Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz