Part 5

219 12 1
                                    

Idan kinsan bazaki iya jurar karantawa ba ko Kuma bakida hangen nesan fahimtar ina labarin ya dosa toh na hutar shi ki base kin  Karanta ba

Inshaa Allah daga wanan page dinan nadena posting a WhatsApp duk me bukata ya duba Wattpad ze samu user name dina na Wattpad @muneeraahh
Nagode 😊

Zaka auri y'a ta barde ya maimaita masa tambayar da yaji duk ya rikici wanan wace iriyar jarabta ce ta kawo shi kauyen nan Seda mahaifin sa ya fada masa kan ya tafi gurd wanda ze tsare shi Amma taurin kai ya hanashi yau ga a inda ya Kare wani da ba mahaifan sa yan so ya masa auren dole Innallilahi wa'ina illahi rajiun yake maimaitawa a cikin ransa kafin ya tsinkayi muryar barde daga Sama Yana fadin "ku shiga dashi wancen Dakin" ya nuna Dakin da hannu "kuyita jibgar sa har Se ya yarda ze auri ilham sanan ku Kyle shi".

A ransa Ji yayi duk dukan da zasuyi masa baze taba yarda ya auri yar mutumin nan ba sanan inya aure ta ma me ze ce da iyayen sa Akan ta ko kashe shi zasuyi shikam baze taba auren yar Dan daba ba mugu ma irin wanan mutumin.

Ilham ce ta sauka daga machine din daya karasa shigo da ita cikin kauyen su Dan idan sun sauka a d'anja Se sun Kara biyan kudi a shigo dasu kauyen nasu Dan daga d'anja zuwa cikin kauyen Seka biya 30naira za'a karaso dakai.
      Kamar yarda ta saba tafiya take cike da nutsuwa fuskar ta Sam ba fara'a sedai duk inda tazo wuce dattijai ko Kuma wanda tasan su girme ta takan tsaya ta gaida su kafin ta wuce.

    Daga inda masu babir ke tsayawa zuwa wajen gidansu da akwai Dan Nisa hakan yasa take danyi Sauri dan ta karasa domin ranar da akeyi yau har cikin tsakiyar kanta take jinta wayar ta ta dauko Dan ta duba lokaci Se taga har 12:00 na Rana tayi maida wayar tayi ta cigaba da tafiya

     A haka har Allah yasa ta karaso kofar gidan nasu Kallon inda mahaifin ta yake Se Kuma ta kalli inda wani bawan Allah ke tsugone fuskar shi tamau gefen sa Kuma mutanen mahaifin ta ne a gefensa kowa Dai hankalin sa nakan bawan Allah, a ranta Taji ya Bata tausayi Amma ba yarda zata iya temakar sa domin duk son da mahaifin ta ke Mata ya kan taka Mata burki Akan shiga al-amuran sa.

    Gaida mutanen wurin tayi har takai kofar da zata sada ta da cikin gidan su ta jiyo ta kalli bawan Allahn da a lokacin sun mikar dashi zasu shigo dashi cikin gidan, Kallon sa tayi caraf Se suka hada ido.
     Gabanta Taji ya fadi ta juya da Sauri ta fada cikin gidan nasu tana me tausayin bawan Allah nan ko Meyayiwa mahaifina ta ohoo, Amma mutumin ya Bata mugun tausayi.
     A zaune ta tarar da mahaifiya Tata Akan kujera wace ake Kira da kujerar zaman tsakar gida ko Kuma wasu sun kace da ita y'ar tsugono.
       Tsintar wake takeyi a fara tin silver ilham Tai Mata sannu da aiki kafin daga bisani ta shige daki ta cire hijab dinta ta dawo inda ta bar mahaifiyar Tata.

    Tambayar ta tayi ya me jiki tace Mata ai jiki alhamdullilah daga nan bawanda ya Kara cewa da kowa komai Dan ita yau gaba daya wani iri takeji ga gaban ta da yake ta faduwa akai akai, innallilah kawai take amBata a cikin ranta.

  Baba ne ya shigo dauke da Leda a hanunsa ilham ta masa sannu sanan ta fara yunkurin tashi ya Kira sunan ta

    Ta jiyo ya mika Mata wata leda dake dauke da farar shada a cikin ta, ta karba tana godiya ta karba zata juya yace.
     "yanzu nake so Kisaka ta Dan nan da karfe  biyun Rana zan daura miki aure"
     Cike da firgici ta zare manyan idanuwan ta sanan ta hadiye wani miyau me daci ta kalli baban tace
   "Baba aure fa kace" ta maimaita tana zare ido sanan cike da firgice a idon ta.

      Eh ilham aure nace na zaba Miki mijin aure Kuma yau dinan za'a daura Miki aure kishirya kafin Jama'a su fara taruwa Dan nasa a sanar a gari a ko ina sanan ya dubi mahaifiyar ilham wace itama gaba daya a rude take wani irin aure ne wanan barde yake fada haka kawai take maimaitawa cikin ranta seta tsinka yi muryar shi Yana fadin ungo wanan kema ki shirya Kisaka zuwa karfe biyu za'a daura aure be Gama magana ba aka fara shigo da kayan abinci gidan gefe Kuma gwaggon barde ce ta shigo.

    Tana fadin a fara Dora tukane mana Se jama'a sun taru ba'a yi abinci ba daga ilham har mahaifiyar ta hawaye ne ke sintiri a kumatun su a wanan lokacin Kam sun tabbatar da maganar barde na aurar da ilham zeyi.

   Hauwa wato mahaifiyar ilham itace taja ilham da ta sandare ta zama kamar status daki, duka su biyun suka Kara fashewa da kuka bame rarashin daya a cikin su.
    Mama ce ta kali yar Tata, ta tuno da mahaifin ilham wanda da Yana tare da y'arsa da Tasha gata miji Kuma Se wanda ta zaba Amma tirr son barin Wahalar gidan kawu yasa yau ta fada mumunan hannu irin na barde, yau gashi zeyiwa ilham auren dole ga mutumin da ko sanin sa basuyi ba saboda rashin y'anci da suke dashi a wurin barde


Bangaren Abubakar kuwa ya daku Bayan dukan da sukayi masa suka barbade masa ciwon da gishiri duk juriya irin ta Abubakar Amma Seda yayi kuka da azaba, ji yayi azabar tayi yawa Dan haka yace musu ya yarda ze auri koma wacece suka she'ke da dariya suka sanarwa da barde Shima dariyar muguntar yayi yace watace dashi borno gabbas take.

Karfe 2:00 na Rana

Kofar gidan barde ta cika makil da mutanen kauye harda me gari cikin gidan kuwa Mata sun cika shi anata hidindimu.

Bangaren ilham da mahaifiya ta kuwa haka suka sha kuka suka rarashi kansu suka shiga cikin jama'a aka fara harkoki dasu.

   Ilham ce Dai idon nan jajir ba annuri a ta tare da ita bale Alamun wani Abu waishi fara'a

    Abubakar yayi danasanin zuwa kauyen d'anja Dan ganin ya gonar mahaifin sa take gashi wayar sa ma a Mota ya Barta bale ya sanar da y'an Sanda ko y'an gidan su halin da ake ciki.

      Barde ya fito da Abubakar daga Dakin da aka kule shi kowa Kallon kyau irin na Abubakar yakeyi sedai Shima fuskar nan tamau ba annuri me gari shi ya zama waliyin ango yayinda liman ya zama waliyin amarya akace Abubakar ya miko sadaki ya zura hannu a aljihu ya zaro kudin da suke ciki duka ya mika aka kirga kudi dubu Dari nan fa aka daura auren ILHAM BARDE Da ABUBAKAR SANI Akan sadaki dubu Dari

Pls vote and comment thank you

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now