Part 18

188 9 0
                                    

*GUDUNA AKEYI*

*NA*


*MUNEERA*

PAGE 17

*AYI MIN AFUWA NAYI MISTAKE WURIB NUMBERIN WANCEN PAGE DIN NE ZE KASANCE PAGE 16 NASAKA 17 DAN HAKA YANZU ZAMU TASHI A 17 NE FATAN KUN FAHIMTA*

*ADAI KARA MIN HAKURI NAJINA SHIRU KWANA BIYU NA SHIGA RUBUBI NE*

*WANDA SUKAYIWA MAHAIFIYATA ADDU'A NAGODE SOSAI ALLAH UBANGIJI YA BAR ZUMINCI*

Tafiya sukai ta kusan 39mnt tsakanin kauyen sayaya zuwa kauyen birin birin sedai fa a hanya sunga abubuwan ban al_ajabi wanda addu'a ce kawai ta iso da su Garin me suna birin birin
   Da kyar da kwatance suka karasa Garin

*

Babar tarba akayi musu saboda sun sanar da zuwan su gashi Kuma malamin  tsoho ne Amma abokin Baba ne na sosai
    Mamy kuwa tuni an kwantar da ita a Dakin amaryan malam wace har yanzu Bata farka ba.
   Nasir kuwa iyayen surutu an gaji
Hadadiyar shinkafa da wake aka kawo musu mai da yaji Taji salak da tumatir da cocumber.
  Malamin Kam Se kwantar musu da hankali yake

Bayan sun Gama cin abinci sun huta.
  Sanan Dan dattijon da sukaji ana cewa baffa ya kali Abubakar saboda yaga kamar shine babba
  Yace ya sunan ka Abubakar y
   Abubakar ya bashi amsa sanan ya tambayi Nasir Shima ya sanar dashi

"Toh menene silar ciwon nan na mahaifiya ku?" baffa ya fad'a Yana Kallon su

     Abubakar ne da idon sa ya ciko kwala ya masa bayanin yarda ciwon mamyn ya fara sanan ya sanar dashi yarda sukayi ta neman magani har zuwan su nan.

Tsohon ya gamaji sanan yayi magana cikin gida aka kawo mamyn wani daki
 
  Har lokacin da aka shigo da mamyn Dakin Bata farka ba yakai hanun sa Saitin hancin ta sanan ya mikawa Abubakar wani magani kamar mai ja yace a shafe Mata a jikin ta zuwa gobe

  Ya tashi Yana fadar yanzu ze turo musu ilham din seta shafa Mata

*** *** ***

Zaune suke da baffa

   "Abubakar yace baffa nikam menene ke damun mamy?

Baffan ya kale shi cike da kulawa yace
  " bakin aljani ne  Allah madaukakin sarki acikin suratul Baqara yana cewa, "LIYUFARRIQUUNA BIHI BAINAL MAR'I WA ZAUJIY" ليفرقون به بين المرع وزوجه. Wato (sai sun Raba tsakanin mace da mijinta). Ko sai sun raba tsakanin saurayi da budurwar da zai Aura, Burinsu hana aure ko raba aure ta hanyoyi da dama

  Amma da izinin ubangiji zata warware

Nan fa aka fara yiwa mamy magani da adduoi sosai mamyn ta fara warwarewa Dan a yanzu hannu yakan motsa Kuma tana magana Kuma tana motsa komai na jikin ta Abu daya ne ya rage Mata shine taka kafarta kullum kuwa godewa Allah da ilham takeyi, su Abubakar da Nasir harma da ilham tun suna Jin wani iri a Garin saboda su basu saba zuwa kauye ba har suka saba da y'an Garin Matan baffa kuwa daukar su suke kamar iyayen su, duk rashin san magana irin na Abubakar Shima Seda yayi abokai mudi da tanko tare suke fita yawo yayinda Nasir kuwa kusan abokan sa biyar tare suke tafiya da yaran malam gona sosai rayuwar kauyen take musu dadi babu wata fargaba babu tunanin wani ze kawo musu Hari haka suke rayuwar su sun shafe wata guda kenan a Garin.

*

Yau da dare kamar duk Wata ranar laraba y'an Mata da samari sukan taru a wani fili a kauyen suna Raye Raye da wake wake.

Yau dukan su har Abubakar Yana wurin y'an Mata na satar Kallon shi yayinda ita Kuma tana kusa da Nasir suna yar hirar su
  Wata yar budurwa chocolate color ba lefi yarinyan nada Dan kyau ta karaso wurin Abubakar wanda hankalin sa gaba daya ba Akan wurin yake ba hankalin sa Yana kan tarin aiki da ya bari na yau kusan sati biyu kenan Amma ai ze iya hakura da komai saboda samu warakar mahaifiyar sa.

'Dan samari yarinyan ta fada tana wani kwarkwsa a gaban Abubakar ya kale ta ya dauke kan sa gefe
   Se Kuma ya kali inda ilham take yaga gaba daya hankalin ta Akan su yake kawai Se ya kali yarinyan yayi murmushi
   "y' an Mata" ya furta Yana Kallon ilham wace gaba daya hankalin ta Yana kansu.
   Ilham kuwa ta kali Nasir tace" Yaya Nasir tashi mutafi yau Kam kaina ciwo yake" Nasir yace "subhanallilah sannu kinji ko mu tafi gida ne" tace eh suka Mike kuwa

   Gefe guda Kuma wasu tatatun y'an iskan kauye ne d'aya ya kali d'aya yace ga mutuniyar Chan zata wuce yakama ta ace yau mun gudanar da kudirin Akan ta
   Dayan da aka Kira da lado yace bakaga tana tare da Dan Uwa ta ba
   Baka tsoro ne dayan yace haba lado  baka San su yan birni nan basuda wani karfi ba Shima Se mu Gama dashi
Kasanfa yan birni nan bawani karfi ne dasu ba mu mai duka ita Kuma mubiya bukatar mu da ita.
  Tanimu yace "Kuna ganin baza'a samu matsala ba nidai tsoro nakeji"
  Lado Yaja wani shegen tsaki yace toh si Seka zauna ku wuce muje Kar suyi mana Nisa
  Wajen su biyar suka bi Bayan su Nasir wanda har sun Dan fara kutsawa cikin Daji Dan wurin yanada Nisa da cikin gari Amma ba sosai ba.

    ***********
Hajiya Kareema ce matar alhaji sani me turare ta farko take ta sintiri tsakanin Dakin ta tana fitar da yar iska me zafi daga Bakin  ta rasa me yake Mata zafi dafe kanta tayi tana yar safa da marwa.
     Waya ta dauka ta Kira salima a waya Mata ta biyu kenan a wurin alhaji sani me turare
  " Kiyi maza maza kizo"

Shine kawai abunda ta iya furtawa idon ta ya kad'a yayi jajir da alama Dai a matukar baccin rai take.
   

   Salima ce a gaban ta, "Yaya meya faru ne"
   Hajiya Kareema tace "baky ganin abunda nake gani Yana shirin faruwa ne a gidan nan" hajiya Kareema ta karashe maganar tana me tsurawa salima ido

     "A'a Yaya ni banga komai ba bansan meke shirin faruwa ba"

    "Baky ganin yau kusan wata biyar kenan Fatima da yaranta basa gidan nan"
      "toh Yaya meye abun damuwa Bayan boka ya tabbatar mana da cewa indai bashi ya karya asirin nan da muka Mata ba kowa ya manta da ita Kuma ta kwanta ciwon nan indai bashi ba bame iya karyawa Dan haka menene abun damuwa may be ma sun gaji da harin kashe su da y'an gidan ku ke musu shiyasa suka gudu Inaga ma sun koma kasar su Fatiman da zama kowa ma ya huta " salima ta fada tana nuna halin ko in kula da rashin su a gidan Dan dama ita haka take so.
   " nidai salima tun satin biyu da suka wuce nake Jin hankalina a tashe game da barin Fatima gidan nan gani nake kamar asirin mu ne yake shirin tonuwa " Kareema ta fada cike da jimami a fuskar ta
"Kinga fa ki kwantar da hankalin ki Yaya Kuma indai batun sarauta ne ma itama ai ta riga ta dawo gidan ku duk da ance rikon kwarya aka Bawa mahaifin ki Amma har yau shi sani wato me gidan nan be taba magana Akan a dawo masa da sarautar sa ba haka ma hassan din bale dama wadancen usaina da Fatima da suke Mata kawai ku kwantar da hankalin ku kudena kaiwa yaransu Hari da zumar kashe su musamman ma Dai yaran sani din. "

   *TOH FA ANA WATA GA WATA 😳*

*FADIMATOU*

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now