Part 21

179 8 2
                                    

*GUDUNA AKEYI*

Na

MUNEERA



Wanga page naki ne our next bride Anjali sa'adatuwa tsowa

Page 21

Yarda ta cukwakwaye shi tana masifa ne ma gaba daya tasa shi yin yar dariya saboda bawani iya masifa tayi ba domin kuwa Bata saba yi ba.
     Tsuke fuska yayi Yana hade Gira ya ture ta daga jikin sa domin wani sabon yanayi yake ji data masa haka
   "Dalla malama nutsu ki kama kanki saki ne ance baza'a yi ba sanan kishiya Se anyi Miki"
Yana Gama fadin haka ya fice daga Dakin ita Kuma ta zube kan gadon tana fashewa da sabon kuka me tsuma rai.
   Fitowa shi Tai Dai Dai da zuwan wucewa Nasir wurin ganin daga Dakin daya fito yasa Nasir tsayawa Yana mai Kallon tsaf da tunanin me ya kaishi Dakin Se Dai Kuma babu damar tambaya saboda yasan halin yayan nasa Se kawai Yaja Bakin sa yayi shiru shi Kuma Sadiq ya wuce shi ba tare d yace komai ba.
   Ta mugun gajiya sosai saboda tafiya da sukayi ga Kuma aikin da tayi gashi batayi sallah magriba ba har isha'e Nason tararda magriba din.
   Tashi tayi ta fada toilet din dake cikin dakin tayi alwala ta yi sallah da nafilolin ta tayi addu'a sosai kafin ta Mike ta kwashi kwanukan data ci abinci dasu Dan kaiwa kitchen.

   A hanya suka hadu da neehal wace ta banka Mata harara itama ilham ta Rama  dan ita kawai haushin neehal din takeji tarasa me yasa neehal din tayi murmushi tana kwafa tare da fadin zamu hadu ne.

*************

Kwanaki na tafiya makoni na wucewa watani na karewa kwanakin mu na karewa
   Gaba daya ilham seta Kara komawa ilham din ta, tada Bata magana Se da kyar Yayinda ganin Abubakar ma wahala yake Mata Dan da sasafe yake fita Kuma Se dare sosai yake dawowa Nasir Kuma ya koma Bakin aikin sa Amma kullum cikin Kiran ta yake duk da ba dauka take ba Amma baya gajiya da Kira da tura mata sakonin yarda yake son ta yakeyi ta waya.
Ita Kuma neehal ashe suma suna part din su a cikin gidan Amma kullum a part din mamyn take wuni tana kokarin takurawa ilham Yayinda ita Kuma ilham kallo ma neehal Bata ishe ta ba.
Shakuwa kuwa me karfi ta Kara shiga tsakanin ta da mamyn zaman ta da mamyn yasa ta Kara koyan abubuwa da yawa irin su girki, gyran jiki da iya zama da me gida domin mamy Bata wasa da kula da mijin ta duk da kasancewar sun fara tsufa, kuma bawani aiki take sosai ba kasancewar yanzu an wadata gidan da y'an aiki wani sa'in seta wuni a daki ma Bata fito ba wani lokacin tana karatun qur'ani wani lokacin bacci Se Kuma waya da take da maman tare da Baba akai akai suna Jin lafiya ta Hankalin su na kwanciya
Mamy Kuma sun shirya da mijin ta sanan ya saki hjy Kareema da Salima an tatara su an maida su ma sarauta Yayinda hjy Kareema hauka take tuburan Se kule ta akayi a daki ita kadai (Allah ya bamu ikon shuka alkhairi Allah Kar yasa mu nufe kowa da mugun nufi ko sharri domin shi sharri Dan aikeni duk inda ka aikashi wata Rana ze dawo) 

Mamy ce ma ta samata dokar zuwa ta dinga gaida manyan gidan su Ammi da hajiya Fatima duk time din da taje suyi ta Jan ta da hira tanajin kunya sosai suke son ilham din saboda Tarbiyya ta ga girmama manya da take dashi y'an gidan kowa na sonta Se wadanda ba'a rasa ba da Bata birge su (saboda a duniyar nan duk yarda kakai ga kyautawa wani duk halin ka me kyau baka taba birge shi).

   Yauma kamar kullum mamy ta fito dauke da Leda a hanun ta tana mikawa ilham wace da alama dama ita take jira tace gashi nan ki kawai hjy Fatima kice Kuma ina gaida ta ilham ta karba cike da girmamawa tace tohm mamy sena dawo mamy tayi Mata a dawo lafiya
  Ita Kuma ta fice
Sanye take da hijabin ta har 'kasa tana tafiya kanta a' kasa tana tunanin girma irin na wanan gida Dan kullum aka aiketa setayi tunanin girman gidan babban gida ne wanda aka Tsara ginin sa aka fitar da part part wato bangare bangare a Kala in ka tsaya cewa zaka irga bangare nawa gidan yake dashi tabbas zakasha wahala tana wanan tunanin harta karasa bangaren hajiya Fatiman wanda Shima yasha tsari domin kuwa ya hadu, tun daga farkon gate din part din kamshi ke tashi haka ta gaida me gadin gidan ya amsa ta shige.

   Palon bakowa a cikin sa ko ina tsit tayi sallama wani d'an saurayi da baze wuce 25yrs ba ya amsa Mata ta nemi gefen carpet din ta zauna batare da tace komai ba.
   Chan Sega wata yarinya ta fito daga wata kofa da alama kofar kitchen ne Dan gidan Se tashin kamshin abinci yake
  "Aa ilham kece yau anan sannu da zuwa" yar budurwar ta fada tana me karasa shigowa cikin Palon
  Ilham tayi murmushi tace Aikuwa Dai nice sannu ya gida
  "Se lokacin Dan saurayin ya dago ya kale ta da fara'a yace dama kece ilham din da yusra tabani labari Akan mamy
  Ilham ta danyi murmushi ta daga masa Kai
  Yarinya da aka Kira da yusra ce tace
" ka ganta nan Yaya Khalifa ba bakuwa bace Amma na fuskaci bakuwa ce a gidan nan saboda na fuskaci Bata son mutane Taki sakin jikinta"
  Wanda aka Kira da Khalifa ne yace "Aikuwa Dai yakama ki zage ki zama yar gida" ya karasa maganar Yana me mikewa tsaye yayi ciki.

  Ki tashi ki zauna Dan nasan wurin mommy kikazo Kuma sekin Dan jirata saboda tana wurin daddy in Kuma tana Chan ba'a kirata.
  Ilham murmushi kawai tayi
Yusra Kuma tayi ciki ta kawo Mata ruwa da lemo tace dole setasha 
Ilham murmushi tayi ta Mata godiya sanan yusran ta koma kitchen

"Aa ilham ce a gidan namu Amma Dai baki dade ba ko"
Ilham ta jima sosai tana jiran Amma setayi murmushi tace "ban dade ba ina yini" hjy Fatima ta amsa ilham ta mika Mata ledar tana Wai gashi inji mamy
Hjy fatima ta Bude tana duduba abubuwan da ilham din ta kawo Mata duk da cewar ita batasan menene
Yauwa tohm ni zan tafi ilham ta fada tana mikewa tsaye
Daga kitchen Taji yusra na fadin
"zadai ki gudu hjy ilham"  yusra ta fada tana Kara fitowa daga kitchen.
"Aa nadai bar aiki ne a gida" ilham ta Bata amsa
Toh Se yaushe zaki dawo kodai sena zo ilham tace Allah ya kawo ki lafiya yusra ta amsa da amin tana juyawa
Takai Dai Dai kofar barin Palon ne Taji tayi Karo da Abu ilham ta dago a hankali tana fadin subhanallilah sedai me ita ji tayi anja wani uban tsaki
Bakowa bace illa neehal Sanye take cikin wata dingilaliyar doguwar riga wace Bata karasa Mata ko gwaiwa ba kanta kuwa babu Dan kwali gashin ta ne yaci uban ado Se Kuma fuskar taci uban heavy make up
Kallon up and down neehal din ta Mata tare da Jan wani uban tsakin tayi ciki
Ilham Kuma ta karasa ficewa tana mamakin hali irin na neehal da girman Kai yayiwa yawa itafa ta bigeta Amma me makon ta Bata hakuri shine taja Mata wanan uban tsakin.
Itada tasa hijab har kasa gani take kowa Kallon ta yakeyi Amma ita neehal ko a jikin ta haka ta taho duk masu aikin gidan na Kallon ta, ta tabe baki hardai ta karaso gidan

Wanan watan Kuma shine watan bikin Abubakar da neehal gaba daya gidan kowa ya fara shiryayen bikin saboda ansan biki ne za'ayi wanda may be ba'a taba irin sa ba a 9ja katsina da kano ana ta shiryaye Yayinda ilham Se ramewa take ita kadai an rasa dalili mamy tayi mata tambaya duniya kan abun da yake damun ta Amma Taki fada Mata tace bakomai.

    Zaune take Akan daduma tana karatun alqurani ya turo kofar ya shigo batare da ta sani ba ya Kura Mata ido Yana sauraran zazagar muryan ta tana ratsa dukan sasan jikin ta Jin tayi shiru yasa shi Bude lumsasun idanun sa Akan ta.
 

   Itama din Kallon shi take cike da masifa tace "malam da fatan Dai Takada ta ka kawo min koo?

Murmushi yayi kawai tare da ta kowa har inda take ya hade........


*fadimatou*🌹
   

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now