Part 23

175 12 8
                                    

*GUDUNA AKEYI*

NA

*MUNEERA*

PAGE 24

. *Mrs mubarak ga naki page din ina godiya da comment dinki*



  Tashi tayi da salati a Bakin ta tana fatan Allah yasa duk abunda yafaru mafarki ne ba gaskiya ba daga idon ta tayi Sama ta kali ledar da kuma yar allura dake jone a hanun ta
   Abubuwan da suka faru ne suka fara dawo Mata wato Dai da gaske Nasir din ta ya rasu ya tafi gidan da ba'a dawowa
    Wata yar nurse ce ta shigo ta kalli ilham tace sannu ko ilham ta amsa da kyar game da kikewa zaune jiri na dibar ta nurse din kokarin yi mata allura take ilham ta dakatar da ita tace ta Barta Dan Allah ita gida zata tafi suyi sallama da Yaya Nasir din ta kan a kaishi gidan sa na gaskiya.
   Babu yarda nurse din batayi ba Dan ilham ta zauna Amma ina haka ta fito ta Tari napep tayi gida kukan ma kwata kwata ya Dena zuwa idon ta a yanzu.

  Tun daga farkon layin har gidan cike yake da jama'a da suke jira a fito da Nasir su sallace shi akai shi gidan sa na gaskiya mutane sun taru sosai kasancewar Nasir mutum ne na jama'a kowa nasane talaka da me kudi me lafiya da mara lafiya Duk Nasir Yana yi da su ga far'a da Allah ya bashi da iya mu'amala da mutane
   Haka ilham ta kutsa cikin mutanen ta shige cikin gidan

   An fito da Nasir an saka shi cikin makara mamy na Duke Akansa hawaye na fita daga idon ta Yayinda Abubakar na gefen ta Shima Yana nasa kukan

   Karasawa ciki tayi itama wasu zafafa hawaye na zubo Mata tana tuna farkon haduwar su da Nasir din da sukayi a asibiti lokacin mamy ba lafiya yarda ya dinga kwasar ta da tsokana.
   Mamy ce ta lura da ita ta Mata nuni data karaso ciki gwaiwa a sanyaye jiri na dibar ta haka ta karaso cikin

Alhaji sani me turare ya shigo Shima Yana Kallon d'an nasa wanda yake matukar so domin kuwa abun nasu kamar rabawa akayi mamy na son Abubakar da Ammal sosai Yayinda shikuma duk cikin yaransa bawanda yake kauna sama da Nasir da Habib musamman ma Nasir wanda yake yaro me biyyaya wanda d'a wuya ka fada masa Abu ya tsalake me son iyayen sa me Kuma kin bacin ransu segashi alhaji Nasir Yana kuka sosai Yayinda aka daga Nasir din Dan tafiya dashi makwancinsa na gaskiya.
   Nan y'an uwa da abokan arzikin suma kowa ya fara kuka (wanda a badini mu da in anyi mutuwa muke kuka kanmu mukewa kuka domin kaima duk dadewarka a duniya akwai lokacin riskar wanan Rana Allah ubangiji yasa muje a sa'a)

   __________________________

Haka rayuwa ta fara shudewa Nasir har yayi kwana uku a makwancinsa Yayinda su barde da maman ilham suka shirya zuwa bakwai (7) Kuma Shima Abubakar din ranar ya kudiri sanar da kowa wacece ilham din a wurin sa.

  Neehal kuwa Bakin cikin da tayi na mutuwar Nasir shine na wargatsa bikin ta da zaayi yanzu gashi dole Seda aka d'aga banda haka Bata wani damu da mutuwar ba saboda dama bawani Shiri take da Nasir ba a cewar ta halayar shi ba irin tashi bace.

Babanta kuwa ya sanar Mata ranar bakwai din Nasir zasu koma duka Somalia saboda ayyukan sa da ya bari da ya zauna Ayi biki dashi Amma Abu ya canza dole su koma wanda Sam ita Bata so haka ba.

   _____________

Yau kwana biyar da rasuwar Nasir kenan saura kwana biyu iyayen ta suzo Se so take taga Manan ta ko Allah zesa zuciya ta tayi sanyi.

. Ilham gaba daya ta rame ta Kara zama wata silent in kuwa ta kebe wuri guda ita kadai ba abinda take Se kuka da tunawa da kalaman Nasir da irin soyayar da Nasir din yake Mata, ga Kuma Lamarin Abubakar da yake wani Bata caring yanzu a gaban kowa Kuma baya kunyar kowa Dan wasu in yayi a gaban su Se ayita mamaki wasu Kuma ayita gulma ana shida baya kula Mata, cikin yan Matan da suke kwana a gidan kuwa masu so Abubakar in sukaga yarda yake wa ilham ji suke kamar su mutu a haka Dai har zance yaje kunen neehal ta kuwa dura wani uban ashar tare da fadin zata ci uban ilham Dan ko ita Abubakar be damu da ita ba shine yaje Yana damuwa da wacen bagidajiyar yar kauye irin ilham gata yar yarinya wanda da tana kanwa ko Kani ilham sa'ar su zata zama.

Shikuwa Abubakar tausayi da son ilham din ne ke ratsa zuciyar sa a wanan lokacin ga Kuma maganganun Nasir da wani lokacin har Hana shi bacci yake in ya tuna yarda yake fada masa ya bar masa amanar ilham din Se yake ganin in ya bari wani Abu ya faru da ilham din Nasir baze yafe masa.

  Zaune ilham take ta zabga uban tagumi tana Kallon mutanen da ke ta hidima a cikin gidan kamar ma wasu su manta da mutuwar Nasir din dama haka mutane suke da saurin mantawa da mutum in ya mutu ta ai Yana Hakan a ranta Dan wasu ma su ta cikin su da yarda zasu ci abinci sukeyi.

  Neehal taga ta doso inda take wace sanye take ta riga da wando wanda sun Dan Dame Mata jiki kanta sanye yake da p-carp tafiya take cike da izza da gadara kallo d'aya ilham din tayi Mata ta maida hankalin ta wani wurin tana mamakin hali irin na wanan neehal din anyi mutuwa ma mutum baze yi cikakiya shiga ba ta kyabe baki tare da mikewa Dan barin wurin ta koma ciki

"hey you" taji muryan neehal ta daki dodon kunen ta

"stupid bastard how dare you ki dinga kula min Abubakar are you mad" Neehal ta fada cike da fushi da kunar rai tana wani irin jin tsanar ilham din Kuma fatan ta shine ilham din ta kulata ta ci Mata mutunci

ABUBAKAR kuwa Yana Kallon su ta sama Yana mamakin karfin hali irin na Neehal Yayinda ya lumshe idonsa ya Kara sauke su Akan Ilham wace idonta yayi lufu lufu alamun kuka Tasha Kuma yanzu Neehal take Kara neman sata wani kukan.




*_kowani marubuci ko marubuciya in ya fara rubutu beda burin da ya wuce na yagama wanan littafin da ya fara Dan sauke nauyin Kansa toh makaranta ku dinga kokarin yi mna adalci ta hanyar yi mana uzuri idan bamu samu damar yi ba ngde_*

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now