Part 13

203 10 0
                                    







DIYAR KITIBI GA NAKI ❤️WANGA PAGE NAKI NE I LOVE YOU


Kwantar da hankalin ki ilham mami na Raye bata mutu ba kinji.
    Amma mamy na bukatar addu'a mu

Yanzu kizo insa a kaiki gida ki shirya koo
  girgiza masa Kai ta yi kafin tace "bazan iya tafiya nabar mami a wanan halin ba sorry sedai Kai ka tafi"

    Wai ina labarin barde ne

Tunda ilham ta tafi abubuwa suka Kara taazara bame kwabar sa a Garin babu me saka shi bale Hana shi
   Sosai ya Kara Tara Yara da suka zama y'an barandan sa
   Y'an  Garin Kuma suna Jin dadin barde domin kuwa saboda shi yan siyasa na tuna wa da kauyen Ayi musu yan rabon abunci
   Mama kuwa dama Chan tana nuna halin ko in kula din ga ilham Dan ma barde na taka Mata birki ne Amma da ko kula da ilham din bazata dinga yi ba
   Barde wani lokacin in ya zauna yakan ta tunanin ilham din sa Dan a duniya son da yakewa ilham ko kanshi baya yiwa
   Abunda yasa be kirata ba yasan har yanzu yasan ilham Bata huce bane fushi take dashi
*

Yau sati daya da faruwar abunda ya same su Amma ilham taga ko Sau daya babu wanda ya taba zuwa duba mamyn abun ya Bata mamaki.
  Sedai lokaci zuwa lokaci takanga Abubakar Yana vedio call da wasu mutane kamar larabawa Yana nuna musu mamy dake kan gado wace har yanzu Bata budi ido Sedai a yarda kullum Abubakar yake fada Mata shine ana samun cigaba da gane da jikin mamyn wanda itadai Bata gani
   A wanan halin ne Abubakar kawai ya Nemo malamin da sukayi magana dashi Akan mamy
Yake zuwa Yana Mata addu'a kullum ana sauke Mata karatun al qur'ani shi Kuma Abubakar ya dage dayi Mata sadaka

   Kwance tashi ba wuya sun shafe kusan wata biyu kenan suna jinyar mami Amma har a lokacin Bata Bude ido ba
  Sedai Abubakar da ilham sunyi wata iriyar sha'kuwa duk da cewa ta gane wasu halaye na Abubakar din murdaden hali ne dashi Kuma botse ne Amma Kuma yanada tausayi da temako.

    Shima Kuma ya gane ilham din miskila ce batada hayaniya Sam Allah ya zuba Mata nutsuwa komai nata a nutse takeyi
   Zaune take ta zubawa mamy ido tana tunanin rayuwar ta wayarta ta hau ringing dubawa tayi setaga an rubuta babana da Dan emoji a gaba

    Bata San time din murmushi ya subuce Mata ba ganin wanda yake Kira ta dauka hankali kwance
    Abubakar Yana Bakin kofa Yana kallon ta da mamakin murmushin da take
   "Amincin Allah ya tabbata a gareka ya abun kauna ta"
  Haka kawai Abubakar yaji ga ansa ya fadi wa takewa kalamai haka kardai ace da auren sa take kula wani

*

Nisawa tayi tace babana tabbas Kam fushi nakeyi dakai Baba Se Kuma ta fashe da kuka tace Babana Amma bakomai duk abinda ya faru kaddara ta kenan Baba
  Seda yaji ta ambaci sunan baban ta sanan hankalin sa ya kwanta
  Ya cigaba da Kallon yarda take ta zubawa mahaifin nata shagwaba.

   "Baba Amma Dai ka Dena shaye shayen nan ko baban ilham"
   Wayar tasa a hands free ganin cewa ba kowa ai a Dakin daga ita Se mamy wace har yau Bata Bude ido ba.
   Baba kuwa yace ilham ana Dai kokarin denawa Amma maganar gaskiya kinsan Bana Miki karya ko to ban Dena ba.

Sanan ilham wallahi kibi gidan nan da aka kaiki a hankali domin wani yazo min nan ya bani makodan kudi kan cewa na kashe shi wanan miji naki da mahaifiyar sa wace take kwance a asibiti koo?
   Ilham ta ware ido tace toh Baba Kai ya akai kasan shi ake nufi
  Ya nuna min hotan sa da sunan sa ilham so ake a kashe shi sosai ake farautar rayuwar saIlham cikin sanyin jiki tace toh Baba yanzu menene abinyi sanan ga mahaifiya sa ma kwance har yanzu Bata da lafiya.
  Baba yace Abu na farko da Zaki nemi sani shine kisan meya faru ta kwanta ciwon menene silar ciwon nata
  Kinga in kika sani seki sanar Dani saboda kinsan in harkar aljanu ce wanan abune me sauki da zan iya maganin sa da kaina Se mu San abinyi Kinga Se muma mu temaka
   Ilham tace toh Baba ina mama dasu harisu da ragowar kane na
   "duk suna lafiya Lau ina koma gida zan hadaki dasu duka ku gaisa"

Toh Baba ka kula min da kanka Kuma yau Karka sha komi kaji Baba yace toh a dakile shifa dama abinda yasa yake kin kiranta ma yasan ilham zata dinga hanashi abubuwa da yawa.
  Babana kayi min alkawari inba haka ba sena kashe auren nan nadawo gida.
   Namiki alkawari yau bazan sha komai ba Se sigari Kara d'aya kawai

   Abubakar dake Bakin kofa Seda tayi dariya

  Naji Baba Kara d'aya inma kasha fin haka zan sani babana Se anjima idan na kiraka
    Yauwa ilham na turo Miki dubu ashirin d'azu ki duba zakiga ni ki siya abubuwan duk da kike Dan bukata banda yawan yiwa miji bani bani
   Ilham tace toh
Baba yace nida nice kema Dan zobon nan zan dinga kulawa ina siyarwa y'an unguwa ilham tayi dariya tace toh Baba yanzu abinda zamu fara shine zan fara gudanar da bincike a cikin gidan domin na lura koma waye yake kawo musu Hari Dan cikin gidan nan
   Sanan baban yace Karki manta da horon da nabaki ke har bindiga in kina bukata zan aiko Miki da ita

    Aa Baba kaima Seka Taya ni binciken ta wurin shi mutumin da ya baka kudin ka kashe su Baba yace toh sanan sukayi sallama ta kashe wayar

Tunani ta fara yi Wai wanene ma Abubakar sanan tana mamakin irin arzikin su saboda kodaga gidansu zaka tabbatar da arzikin su meyasa ake so toh a kashe su a shafe ba in su a doron duniya suwaye Kuma sadik yake waya dasu kamar larabawa toh Shima Dai Yana Mata kama da larabawa shida mamyn sa suwaye su me sukayiwa mutane ta dade Kai kafin ta furzar da wani irin numfashi abun na damunta ita Kam zata tambayi sadik wanene shi.

    Wanan wace iriyar rayuwa Baba ya jefa ta dama suma masu kudi haka suke ji dama suma basuda kwanciya hankali
   Komai na more rayuwa Allah ya Bawa su sadik sedai Kuma Abu daya ne yayi tangarda a rayuwar su wato kwanciya hankali subhanallilah.



Yau kunji no shiru Bana Jin dadi ne sanan ba Lalai gobe nayi typing ba nagode

MUNEERA

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now