Part 20

174 7 2
                                    


*GUDUNA AKEYI*


*NA*


*MUNEERA*

*PAGE 19*

Gaba dayan su sukayo cikin Dakin da mamyn take sukaga yarda baffan ke tamata addu'a
   A haka Dai har mamyn ta fara kwarara Wani irin amai wanda ba kyan gani tana rike kanta tana ambaton "wayo kaina kaina zan mutu Kaina"

Sosai tayi amai wanda tsaf Aman ba kyaun gani🤮
    Tana Gamawa ta sume ilham ba tare da nuna kyama ba tayi kan mamyn a haka tana jijiga ta Kallon baffan tayi tace
   "baffa meke faruwa ne"

"Bakomai jikata zata dawo Dai Dai insha Allah yanzu Dai ki fita kinemo abinda Zaki goge Mata jikin ta"

   Haka kuwa akayi ilham ta goge wurin ita da su Abubakar tare suka gyra wurin ilham Kuma ta canzawa mamyn Kaya sanan ta kwantar da ita.
 
    Har akayi sallah azahar mamy Bata Mike ba Kuma lokaci zuwa lokaci baffa na lekowa ya duba ta sanan yace da ilham ta kwatar da hankalin ta mamyn bacci take zata farka.

   Wurin la'asar mamyn ta farka dauke da salati a Bakin ta
  Ilham ta karaso inda take tace
  "sannu mamy"

"yauwa y'ata kema sannu da dawainiya kinji yar albarka"

Ilham tayi murmushi

Mamyn tace Dan sa min ruwan wanka kinji, ilham tayi 'kasa dakai tace dama na saka Miki mamyna saboda nasan Zaki bukata.
   Kokarin daga ta ilham tayi abun mamaki Sega mamyn ta tsaya da kafafun ta kamar ba ita ba.
   Ilham ta kwala wata uwar Kara tana ambaton alhamdullilah.

Ihun da tayi Shiya jawo hankalin mutanen gidan Dakin da su ilham din suke harda Abubakar daya shigo yanzu Jin Ihun ilham din ya dauka wani mugun abune ya samu mamyn  ilham take ihu seya ga Sabanin haka
  Da murnar sa kuwa ya koma waje ya Kira Nasir

   Duk farin ciki sukayi na warkewar mahaifiya tasu, ilham kuwa ji take a ranta yanzu zata rabu da kaddaran aure Abubakar sadik da ko me yake ji dashi seya saketa (ni muneera nace toh fa😒)

************

Mamy kuwa ta Kara samun karfin jikin ta sosai sati d'aya suka Kara a Garin Abubakar yace tafiya zasuyi haka suka salami malamin nan da makudan kudi Amma Sam yaki karba yace shifa Dan Allah yayi ba Don kudi ba sunyi sunyi yaki karba.
   Motarsu kuwa haka aka cikata da kayan tsaraba iri iri Dai abokan su sadik da Nasir harda yar kwalar su na Sabo da akayi kwana biyu.
  
Tunda suka dauki hanyar kano babu me cewa komai kowa yayi shiru kowane cikin su da irin tunanin da yake yi
  Mamy ta kali gefen ilham wace ta lula cikin tunani tace "y'a ta yau keda Nasir din mutumin naki duk Kunyi shiru kamar Baku ba" ilham tayi murmushin yake tace mamy kaina ne ke ciwo
   Nasir kuwa dake tukin Mota yayi caraf yace "mamy yau kusan sati biyu kenan ilham tadena kulani da mun gaisa shikenan seta dauke min Kai" Abubakar ya juyo ya kali inda ilham take suka hada ido ya sakar Mata murmushi setayi saurin yin 'kasa da kanta sakamakon kwayar idon sa da Bata iya jure gani.
    Mamyn ta kali ilham wace har lokacin kanta na' kasa tana tunanin sadik itadai tasan ba son sadik take ba Amma ta rasa meyasa take tunanin sa sanan take mugun ganin  kwarjinin sa wata zuciyar ta kawar Mata da tunanin abun tare da 'Kara ayanawa a ranta ayau fa base gobe ba zata sa ya saketa seya saketa ma dole sa

   Sun sauka a kano lafiya suna shigo da motar su cikin gate din Sega motar su hajiya Kareema itama ta shigo gidan sun dawo daga yawon gidan bokansu ya tabbatar musu dashi ba abinda ze iya yi Kuma ya sanar musu asirin su ya karye in Kuma suka Kara kokarin taba lafiya Fatima zasu iya mutuwa sanan karsu yarda su hada ido da Fatiman in kuwa sukayi za'a samu matsala haka suka juyo sukayo gidan hankalin su a tashe da maganar boka.

    Packing space gaba daya suka samu sukayi parking su hajiya kareema basu San suwaye cikin motar kusa dasu ba saboda tint ne a motar dasu mamyn ke ciki sedai a lokaci d'aya suka fito daga Mota hajiya kareema suka hada ido da mamy.

    Ihu hajiya kareema tasaki ganin mamyn da tayi kawai seta fara zabure zabure tare da cire dankwalin ta ta yarda wayar hanun ta fa fara rawa tana yagar gashin kanta, Abubakar sunyi kokarin riketa Amma ina tafi karfin su
   Security suka kan sun Kamata a kule ta tare da yin bangaren Ammi da ita tana ta fizge fizge ita kuwa hjy Saleema tana ganin abinda kareema tayi ta zura a guje tayi cikin gida
   Ammi segani tayi an shigo da kareema tana fizge fizge a lokacin gaba d'aya y'an gidan suna Palon Ammi din ana meeting kan ba cewar su mamy ciki kuwa harda Dan uwan mamy Khalid da matar sa kubura tare da yarsa Neehal.
   Dan gaba daya kowa ya dawo hayyacin sa game da dauke hankalin Su da akayi daga kan mamyn sukaga an shigo da hajiya kareema tana fizge²

Nan fa hajiya Kareema tafara tonawa kansu asiri itada salima kan abinda sukayiwa mamyn yayin da mamyn dasu ilham ke gefenta suna rafka salati.
  Alhaji sani ne ya nunawa securities din wani daki yace su kule hajiya Kareema sanan su mamy suka shigo cikin Dakin suma kowa da tunanin abunda ya faru yakeyi
  Alhaji sani wato mahaifin sadik Yana ganin mamy beji kunyar y'an uwansa  da Ammi dinsa haka ya tashi ya rungume mamyn Yana hamdala yayin da ita Kuma ta tureshi tana hararsa Dan duk da abinda ya faru asiri ne aka musu Amma tanajin haushin sa.
  Nan fa yaran gidan sukayo kan mamyn suna Mata barka da zuwa
  Yayinda neehal wato yar yayan mamy ta taho direct wurin Abubakar tayi ta rugome shi tana fadin Yayana nayi missing dinka.
  Murmushi kawai Abubakar yayi ya janye ta daga jikin sa Yana me Kallon inda ilham take wace ta nuna gaba d'aya hankalin ta ba akansu yake ba Amma fa a badini hankalin ta nakan su shi Kuma Nasir hankalin sa na kanta (nace toh fa)
   Bayan sun huta ne Nasir ya Bawa gaba d'aya y'an uwan nasu labarin abinda ya faru da irin kokarin da ilham ta dinga yi da mamyn duk ya basu labari babu wanda be girgiza da Lamarin ba
   Babu wani Bata lokaci suka fara shararawa ilham din godiya da temakon da tayi musu.

   Anan Khalid wato mahaifin neehal Shima yace
  Ilham dagowa tayi ta kale shi kawai setaji gaban ta ya fadi data hada ido da mutumin nan.
    Duk wani me Kallon kurila idan ya kali ilham ya kali Khalid ze hango tsamanin kamar su.
    "nagode ilham da temakon yar uwata da kikayi Allah ya Miki albarka"

   Ji tayi duk duniya bawanda ya taba saka Mata albarka Taji dadin ta irin ta wanan bawan Allahn
  Sanan ya Dora da fadin
   "dama abinda ya kawo ni shine batun auren Abubakar da neehal tunda ga kowa anan Kuma already ankai kudin aure yakamata musaka Rana auren nan Ayi shi Dai kafin nakoma Somalia"


Wani irin muguwar faduwar gaba ce ta riski ilham ta runtse idon ta



*fadimatou🌹*

   

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now