Hafsah tace"Allah zan gayamai kina mishi Labe in yana Waya da Matarsa.."Da Sauri Subai tace"Rufamin Asiri Don Allah..Kada ki kara jamin wani Fadan Bayan wanda dazu nasha.."Dariya ta kama Hafsah itama Subai din Tana Tayata Kwanciya suka gyara Lokaci Daya Suna Cigaba da Hira Cikin Hiran ne Hafsah ke tambayan Subai Labarin yayar Mijinta nan take Fadamata Tunda Ummi tazo ta bata Hakuri kuma tace zata jama Uwanin kunni Shikenan Daga Lokacin ko Haduwa sukayi Sai dai Harara Daga nesa Hafsah ta gyada kai tana Fadin hakan yafi Gwara kowa ya zauna iya matsayinsa,Suna Cikin Hirar ne Barci ya kama Hafsah ganin haka yasa Itama Subai din tayi addu"ar Barci ta kwanta.

Washegari Tun  wajen 10am na Safe su Hafsah da Zannira da Subai sai Jamila da wasu Jama"ar suka Tafi malumfashi,Wajen azahar suka isa Dama anyi Danki wasu kaya ne suka Tafi dashi na kitchen sai akwatunan amarya da Sauran Kayan amfani Sun iske Su Umman Sadiq sunyi wanka suna ma Ta Shirin dawowa ne,Nan suka Hadu suka kara gyaran gidan Amarya Bayan sun gama Manyan su Umman Sadiq da Wasu Daga Cikin Dangin Babanta suka mikata gidan Surukanta Dayake ba Nisa da Gidan Da yaron ya gina chan suka Barta Daganan Tashar Mota suka kara samu zuwa Danja,sai Dare suka iso Goggo Habiba sai Hamdala take tana kuma Fatan Yadda komai ya gamu Lafiya yasa Baki su koma Gida Lafiya.

Washegari Tun 11pm na safe yan Zaria suka taso wajen 1saura na Rana suka iso Gidan Mama suka yada Zango Daman nan ne Daba,Yara suna ma iyayensu oyoyo,Sun Sauka ba Dadewa Zannira Auwal ya Rakata Tasha tayi Tashan Golf zuwa Kaduna taso ta bari sai gobe ammh Mijinta ya Hana Dole ta koma aranar,subai da Hafsah ne suka kai Dare,Inna Abu kuma Suna Sauka ta karisa Gida.

Da daddare Bayan Abdullahi ya Taso Daga wajen aiki ya Biyo,akuma Lokacin ne yace Mama ya yanke Hukunci aure zai yi ma Jidda sai Lokacin ya gayamata Abunda ya Faru Ranar da sukaje Daurin Aure,Jin Haka yasa Mama ta goyi Bayansa Umman Sadiq ne kadai tace A"a kada ayi gaggawa abari ta ida karatunta,jidda na Jin haka ta Fara kuka tana bama Abdullahi Hakuri sai da aka kai Ruwa Rana da Taimakon Umman Sadiq ya yarda zai barta ta Zana WEAC DA NECO dinta wanda sun kusa Farawa ammh da Sharadin in ya kara ganinta da wani Saurayi batare da Wa'adin Daya Dibarmata ya Cika ba wlh ko Shawaran su Mama bazai Nema ba sai dai taji Ya bada ita Sadaka ga koma waye kuwa Jin haka yasa ta Tsorata sanin Halinsa kaifi Daya ne, in yayi mgana baya Chanzata kuma in yace Eh toh eh din ne Har Abada.

Subai ta Fara Tafiya Gida Mijinta yazo ya Dauketa ita da yara Hafsah kuwa sai wajen 11pm na Dare Abdullahi ya kwasheta ita da yara zuwa Gida,Duk da Ranar ta gaji gata gajiyan tafiya gata Zirga zirga ammh Abdullahi bai Daga mata kafa ba sai da ya nuna mata yadda yayi kewarta kamar yadda yake Fadi,Washegari kuma Goggo Habiba ta kira kowa tamai Bangajiyan Biki tace kuma Tana nan zuwa Tamusu Bangajiya Dama kuma sun zo da Sakon Su Cincin dasu Dubalim wanda tace abama Mama ta Rabama wanda ya dace.

******

*After 3 Month..*

"Zuwa Lokacin Dai haka Abubuwa sukayi ta Gudana Da Dadi ba Dadi,Bangaran Hafsah da Abdullahi kuwa komai yana Tafiya Daidai Kusan dai yanayin na Abdullahi Watarana Dadi Watarana kuma Madaci Dayake Hafsah Ta Riga ta gama Saninsa Bata Biyemai ta Riga ta san Halin mijinta Baya son Raini yana son abashi Girmansa Shiyasa ta zama mai Biyayyah da Sadda kai,komai Cikin Taka TsanTsan take bata kaunar Taga tayi Abunda zai batamai Rai Ballatana Har wani Fada ko karafinsa ya Shiga Tsakaninsu.

Bangaran Sakina kuwa da Nazifi Babu Chanji sai Abunda ma yayi Gaban Nazifi ya Riga ya gama Fita Sha"anin Sakina ya ijiyeta a onesite,Ya kama Harkan gabansa ,Mganar neman Auransa kuwa Tunda sukeje Gidan Salisu Engr,bai kara komawa wani waje ba,Bawai ya hakura Da karin Auren bane a'a yana so sai zuwa gaba in yaga wacce zata iya Rikesa Ba kamar sakina Datayi ma Rayuwarsa Rikon Sakainar kashi ba,Yana son in zai kara Aure yayi Shi Don Allah da kuma yarda sunnar Manzo ta tanadar Baya son ya kara Tafka irin kuskuran Daya Tafka a Baya.

Ganin Ginin Abdullahi nata Nisa yasa Shima Nazifin ya Fara Gina Filinsa na Gaskiya tare da Taimakon Shawaran Abdullahi Data Baba wada,Sai kuma sukayi Tunanin gwara su koma Masters dinsu,kafin abubuwa su sake yi musu yawa Abdullahi dama Tun Tuni ya Turama Office dinsu Takardan yana so ya karo karatu kuma An Riga anyi approving din Requesting nashi shi bai maida kai ba,ammh mganar Nazifi yasa ya maida kai kan Karatun Dukkansu atare suka yanke Shawaran zasuyi,Tunda Dama Shi karatun Masters ba kamar Digiri bane ba koda yaushe kake Shiga makaranta ba,Wani Lokacin ma sai kayi Sati baka Shiga ba, Tunda Daman ga  ayyukansu da kuma iyalansu,Abdullahi ABU Zaria ya nema Shi kuma Nazifi sai ya nemi Kasu Kaduna State University  kuma Cikin ikon Allah Dukkansu suka samu kowa kuma abangaran Daya karanta kafin kace me har sun kamallah Registration sun Fara Karatu.

MASIFAFFAN NAMIJI..!Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ