GIDAN MIJINA

351 10 0
                                    

GIDAN MIJINA.
🚨🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨🚨

Short story

Story &written by

MAMAN AFRAH
 

  

Marubuciyar

RAYUWAR MARYAMU

AND NOW

GIDAN MIJINA


Alhamdulillah I am back again🤗

     Page 1_2


Kwance take akan gadonta tana ta zubar da hawaye kuka take sosai amma ba mai fitowa ba,ji take gaba daya gidan ya mata Zafi,kai bama gdn ba jin duniyar take ta mata mugu mugun zafi,sbd irin kuncin da zuciyarta.wasu hawayen ne masu zafi suka kara kwaranyo mata,tunani take lokaci yayi da zata nemi saukakewar wannan kaddararren auren tunda abin ya fara zuwa da tozarci da kuma cin mutuncin iyaye.lallai anzo wajen da zuciyarta bazata taba dauka ba bare har ta jure,wannan zagin da kabeer ya mata tabbas yayi muni da yawa,shin mesa wasu mazan basu dauki mata a bakin komai ba? Shin mesa suka maida matansu kamar wata shara ko ma in ce bola gaba daya? Sake juyi tayi ta koma daya gefen hannunta dayan tayi filo da hannunta,tana cigaba saka a zuciyarta tana jin yadda hawayenta ke gangarowa akan hannun da tayi filo dashi.yau tsawon shekaru goma tana gidan nan amma bata taba yin dawwamammen farinciki ba,rabonta da farinciki mai dorewa tun tana amarya. sunyi hannun riga da farinciki in ma ta fara farincikin to tabbas ba dorarre bane,domin kwa bazata taba samun hakan ba daga wurin mai gidanta ba.dan dk yadda taso suyi zaman lpy irin na ma,aurata tokwa zai sanya kafa yayi fatali da hkn.ta kasa gane manufarsa ko dalili akan hkn,ko kadan baiso tayi walwala gashi dai auren soyayya sukayi,bare tace ko lika masa ita akayi shisa yake mata irin wannan wulakancin.tabbas zata dauki komai amma banda cin zarafin iyaye ta daure tare da wulakanci kala kala amma kuma bazata dauki zagin iyaye ba ,iyayenta ba wadanda sukayi wahala da ita ba tun tana yarinya, har kawo yanzu da mahaifinta ya  koma ga Allah Sai mahaifiyarta.tabbas dole ta dauki mataki daya a Cikin biyu ,ko dai ta daina ragawa kabeer kamar yadda take masa,kawai tayi fito na fito dashi ,ko kuma ya sawwaqe mata  taje gaba Allah ya bata wanda ya fishi.

"Mama kukan me kike"fauzy ta fada itama tana hawayen.
Saurin  goge hawayen tayi dk da tasan fauzy din ta gani,tana juyowa tayi tana mika hannu ta kamo hannun yar tata yar kimanin shekaru tara a duniya.

"My fauzy wa yace miki kuka nake idona ne yake ciwo shine yake ta zubar ruwa"aysha ta amsa mata  cikin shakekkiyar muryarta da taci kuka ta koshi.

"A ah mama tun dazu fa nake tsaye ina kallonki kina kuka kodai baki lpy?"fauzy ta fada tana tsare mahaifiyar tata  ido.

"Haba fauzy ba,aso yarinya ta gari mai son shiga aljanna bata musawa babba idan yayi mgn"aysha tace tana shafa kan fauzy"

"Yi hkr mama nima inason shiga aljanna,kawai dai naga abbanmu yana miki fada,kuma har naji yayi zagi bayan kin hanamu zagi kuma a islamiya ma malam ya hana zagi amma shi abbanmu ya.....

"Ya isa haka fauzy abbanku subutar baki yayi Amma ba zagi yayi ba,maza kije kuyi alwala keda yan uwanki yanzu za,a kira sallah,nima gani nan fitowa kinji yar albarka"aysha ta fada tana mikar da fauzy tsaye tare da shafa kanta.

"Toh mama"fauzy ta fada tana fita daga dakin da gudu abinta.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji,un" aysha ta fada tana komawa ta kwanta akan gadon wani tsoro yana rufeta na yadda taji yarinyar ta rike cewa abbansu ya zageta ,ita da ko kadan bata yiwa yaranta tarbiyar zagi ba,sai dai ta cewa yaro "gidanku"amma yanzu kabeer yazo yana zaginta a gaban yayanta wannan wace irin rayuwa ce? Tabbas ba karamin bata tarbiya bane ace yaro mahaifinsa ya zagi mahaifiyarsa a gabansa ,kai ko ba mahaifiyarsa aka zaga ba lallai zagi na zubar da kima.yanzu meye mafita a gareta shin koda kabeer ya saketa dole dai  zata bar masa yayansa a gidansa kenan tabbas tarbiyarsu na reto tunda shi bai damu da Ya basu tarbiya ba ,kullum itace mai kokarin basu tarbiya sanyasu suyi abu mai kyau ko hanasu suyi abu mummuna.amma shi ba ruwanshi da wannan kawai abinda ya Sani ya ciyar dasu shayar dasu da dauke dk wani nauyi da yake kansa amma bana tarbiya ba dan wannan ya sakarwa  mahaifiyarsu, bayan kuma shima suna da hakkin ya tarbiyantar dasu.

"Mama munyi alwala ina cayyayata?"ta jiyo muryar amira akanta tana tambayarta.

"Mama nima ina cayyayata"amir shima da shigowarsa dakin kenan ya fada yana tsalle.

"Ku bari auntynku tazo ta dakko muku ita ta linke muku dazu bansan inda ta aJiye ba"ta fada tana mikewa tsaye daga kan gadon domin shiga bayin dake cikin dakin,dan tasan yanzu ne yaran zasu dameta da tambaya.

"Yawwa aunty fauziy ki dakko mana abin sallarmu inji mama"ta jiyo muryar yaran suna fada lokacin da take kokarin tura kofar bayin.domin gabatar da sallar magriba.


   Da daddare bayan ta yiwa yaran shimfida ta kwantar dasu,itama bayi ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta dauki riga marar nauyi ta sanya,turare ta dauka body spray ta feffesa.fitowa tayi ta nufi kitchen domin dakko abinci taci sbd yunwa da take kwakular yayan hanjinta,amma kuma jin bakinta take kamar madaci domin gaba daya bata jin dadin jikinta.dan har ji take kamar zazzabi na neman rufeta ga wani ciwon kai da take ji kamar kan zai rabe biyu dk da tasan hakan bai rasa nasaba da kukan da tashayi.

  Bubbude food flask dn tayi amma kuma sai taji bazata iya cin abincin ba, kofi ta dakko da tea spoon ,dawowa falonta tayi ta dauki kayan shayi ta hada mai kauri tasha ,sannan ta dauki paracetamol guda biyu ta hadiya ,komawa dakin yaran tayi ta kara tottofa  musu addu,a ,sannan ta leka dakin hinde mai aikinta ta fada mata take yawan leka yaran sbd zata je ta kwanta,amsa mata tayi da toh,sannan ta juyo ta koma,bedroom dinta ta nufa ta je ta kwanta.amma a maimakon barci yazo ya dauketa sai kawai maganganun kabeer suke ta mata amsa kuwwa take taji ranta ya baci wani kululun bakin ciki ya tokare mata makoshi,nan da nan wasu hawaye suka gangaro daga idanunta,tunowa da tayi da irin wahalar da tasha wajen nakudar yayanta tabbas haihuwa akwai ciwo nakuda nada wahala bai dace ba kuma bai ma kamata ba ace an wulakanta iyaye .dk wanda zai zagar maka iyaye ba masoyinka bane ,iyayenka dk rintsi iyayenka ne,dk kaskancin iyayenka sunansu iyaye,kuma matukar ka cika dan halak bazaka taba bari a wulakanta maka su ba.dk da wanda ya zageka kansa ya zaga amma tabbas yayi hkn ne dan ya nuna maka iyayenka basu da kima ko daraja a gunsa.

"Yama zaki yarda kabeer yake ciwa iyayenki mutunci ta hanyar zagi bayan iyayenki su suka sha wahalarki ,sukayi dawainiya dake har kika isa abar sha,awa kabeer ya ganki yace yana sonki har kika aureshi??  Mutumin daya ganki da hakoranki talatin ya aureki,amma yazo ya wulakanta miki wacce tasha wahala wajen wankin kashin hakorinki?? Toh kema mesa kika ki ki rama zagin daya miki?tunda ay uwa batafi uwa ba kuma ubama bai fi uba ba kuma shima dole zai ji ciwon zagin idan kn mishi hkn zaisa ya shiga taitayinshi ya kuma fahimci menene zagin mahaifa.......

"Bazan taba rama zagi ba,domin ni ba irin tarbiyar da aka min ba kenan,idan na rama mun zama daya kenan,sannan nima na zagi iyayen nawa kenan,kuma me zan cewa yaranmu idan nima na zageshi,kinga kenan zasu dauka zagi abu ne mai kyau suma sukeyi tunda ga iyayensu suna zagin juna a Gabansu,wlh ba tarbiyarmu daya ba ni
Kabeer"ta fada da karfi tana kara fashewa da kukan takaicin abin daya mata tabطدbas idan ya dawo sai ya san yau ya mata abinda ta kasa jurewa, abinda bazata ma taba jurewa ba dan sai ko ya san zasu fara zaman bariki a gadn koma dai ya Sawwaqe mata baki a daya ta koma gdn iyayenta yaje ya auro wacce ya zageta a dalilinta.

  Ku biyoni domin jin yadda zata kaya,ina ftn littafin zai samu karbuwa domin zai zo muku da sabon salo.ng

GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now