ADAM da BIE mata da miji ne da suka yi auren soyayya, kamar kowanni aure TOGETHER FOREVER suka yiwa junansu alƙawari, sai dai bayan shekara goma Bie tana son su rabu, shi ma kuma Adam yana ganin kamar akwai yiwuwar TOGETHER FOREVER fa a mafarki ne ba a gaskiya ba. Sai dai yayinda su ka yanke hukuncin rabuwa da junansu, iyayensu sun yi biris da wannan zance. Ko Adam da Bie za su yarda da zaman sulhu na wata 6 da iyayensu suka sa su na dole? Anya abin da bai gyaru ba a shekaru goma zai iya gyaruwa a watanni shida? Ku biyo alƙalamin Azizat domin samun labarin Mr and Mrs MAIDOKI. Na muku alƙawarin wannan labarin daban ya ke. It's going to be a BLAST. Kada ku bari a baku labari