05

82 2 0
                                    


*MR & MRS MAIDOKI*

                    

©AzizatHamza2023

                                   05

                                ***

ADAM SALIHU MAIDOKI ɗa ne ga Alhaji Salihu Adamu Maidoki, wani Attajiri mutumin Zaria mazaunin Abuja. Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗabbaka kasuwancinsu da wuri a garin Abuja a farkon lokacin da aka maida Abujan Federal Capital Territory na Nigeria. Hakan yasa kasuwancinsa ya haɓaka sosai cikin shekaru.

Alhaji Salihu mutum ne kaifi ɗaya. Baya magana biyu, kuma bashi da tsoro.  Gidansu gidan yawa ne kaman yadda aka san gidajen Sarauta a ƙasar Hausa da tarin iyali.  Sarautar Maidoki sarauta ce da suka gada iyaye da kakanni.
A  gidansu shine ɗa na biyu a jerin 'ya'ya maza. Kuma lokacin da mahaifinsu ya rasu shi aka bawa sarautar ba yayansa ba.

Alhaji Salihu Maidoki irin mutanen nan ne da tun asali basu da ra'ayin zama da mace ɗaya. Tsakanin uwargidansa da ta biyu shekara huɗu ne kawai.

Hajiya Aminah ita ce matarsa ta farko. Ta haifa masa 'ya'ya bakwai amma biyu sun rasu saura biyar.
'Yayanta yanzu sune, Kulsum, Hadiza da suke kira da Lala, Fatima, Abdullahi, da kuma Auwal.

Matarsa ta biyu sunanta Khadija ta haifa masa 'ya'ya biyu Allah ya karɓi rayuwarta. 'Ya'yanta sune Adam da suke kira da Babangida da kuma Aisha.

Ta ukun ita ce Hassanah da yara ke kiranta da Umma. 'Ya'yanta sun haɗa da Hafsah, Aliyu, Batul da kuma Yusuf.

Sai Anty Hindu wacce ya aura bayan rasuwar matarsa Khadija. Ita kam 'ya'ya biyu ta haifa ta bar gidan. Ta haifa masa Zainab da Munnirah.

Amaryar gidan a yanzu ita ce Anty Madina. A lokacin da ya aureta ne ma shi da Anty Hindu suka dinga samun matsala daga ƙarshe zaman ya ƙi daɗi har suka rabu.

Ɗa Anty Madina ta haifa a gidan wato Kabir. Sai dai tana da 'ya'ya biyu a gidan tsohon mijinta.

Yaran Alhaji Salihu su goma shauku ne. Shi mutum ne mai son 'ya'yansa sosai. Dan akan 'ya'yansa ko matan gidan zai iya ɓatawa da su. Ko abinci ne basu yi da wuri ba ya dawo ya ga yara basu ci abinci ba ya dinga faɗa kenan dan Alhaji bai yarda da girkin masu aiki ba.

Adam shine ɗansa na shida kuma gaskiya yadda Allah kan ɗaura soyayyan wani ya fi na wani a zuciyar mutum haka Allah yasa masa son ɗansa Babangida sama da sauran. Lokacin da mahaifiyarsa ta rasu ya damƙa amanarsa ne a hannun uwargidansa da kowa ke kira Hajiya. Ita kuma ƙanwarsa Aisha dake da kaɗan ta fi shekara ɗaya a lokacin sai ya bawa ƙanwarsa Maryama da suke kira da Hajiyalle, shekaranta takwas da aure a lokacin amma Allah bai bata haihuwa ba. Har yanzu Hajiyalle da ake kira Ummi bata samu haihuwa ba Aishar ce kawai a hannunta  shi yasa take mata fitinannen so. Mijinta na da 'ya'ya da sauran matansa biyu da ya aura amma ita kam Ummin Aisha ce.

Babangida ya tashi cikin 'yan'uwansa babu tsangwama ko banbancin 'yan ubanci. Idan akwai abinda babu ko kuma Alhaji Salihu bai yarda da shi ba to maganar 'yan'ubanci ne. 'Ya'yansa duka ɗaya suke a wajensa babu banbanci. Wannan yasa ma Hajiya bata banbanta 'ya'yan data haifa da kuma Babangida ba. Musamman saboda sun yi zama mai daɗi da marigayiya kafin ta rasu. Dake ita Allah bai bata haihuwa da wuri ba, su Kulsum da Lala duk ita take yaye su.
Kafin Khadija ta haifi Adam sai da ta yi ɓari a lokacin da Hajiya ta haifi ɗanta na huɗu wato Abdullahi.
Tsakanin Abdullahi da Babangida shekaru biyu ne ba wata ɗaya.

Babangida ya kasance yaro mai kaifin basira da kuma shiga rai. Wannan yasa ko sau ɗaya mutum ya shiga gidan zai ji yaron ya shiga ransa.

Tun yana yaro ya ke bin Alhaji suke zuwa kasuwanni da gidajensa wannan yasa ya tashi da sha'awar irin abinda Alhajin ke yi, wato harkan gidaje da shaguna da filaye. Wannan ne ma yasa a masters ɗinsa na farko ya yi shi a ɓangaren Estate Management.

MR and MRS MAIDOKIWhere stories live. Discover now