04

82 2 0
                                    


*MR & MRS MAIDOKI*

                    

©AzizatHamza2023

                                   04

                                ***

Sati ɗaya kenan da zuwansu wajen counselling. Babu wanda ya sake yiwa ɗan'uwansa magana da suka dawo. A  ranan Adam ne ya fara ficewa daga office ɗin Dr Mansur bayan Bie ta nuna masa hotonsa da ƙawarta Labiba suna kissing junansu.
A zuciyar Bie ta san an riga an gama magana dan kuwa ba therapyn da zai gyara abin da ya riga ya ruguje. 
Adam ya cuceta. Kuma ba zata taɓa yafe wannan cutar ba.
Labiba ta turo mata hoton ne  bayan ta kirata ta zazzageta akan ƙoƙarin shiga rayuwar Adam da take dan a chats ɗinsu da Adam babu komai sai hotunan da ta tura masa da gajeren rubutu da  ta ce *'i'm waiting for you'* ƙila kuma Adam ɗinne ke goge chats ɗin ya bar hotunan.

In his defence Adam ce mata ya yi shi bai san da hotunan ba kuma ba abinda ya haɗa su. For a while ta ɗan ji zuciyarta yana ƙoƙarin aminta da bayanansa. Ba zata iya shaidar Labiba akan bin maza ba dan tunda aurenta ya mutu kusan shekaru biyar da suka wuce  bata sake aure ba. Kuma ta san yadda maza ke sake mata kuɗi tunda da bakinta take gaya mata Alhaji wane ko celebrity wane ya bata miliyan kaza.

Lokacin da Labiba ta turo hoton nan her first instinct shi ne kawai ta ɗaura hoton a twitter ta dragging ɗinta, amma data tuna fiskar Adam ne ya fi fitowa kuma koba komai Adam uban 'ya'yanta ne sai ta haƙura da saka hoton a media ta barshi a matsayin evidence.

Mutum biyu ta nunawa hoton. Ya Jamal da kuma Abbie. Ta yi mamaki da Abbie ya ƙaryata hoton da cewa photoshop ne, ya kuma gargaɗeta da ta bar maganar zuwa lokacin za a yi bikin anniversary na aurensu da kuma na kamfaninsu.
To ga shi dai abin da ake gudun ne ya faru.

Bie tana zaune a office ɗinta tana duba sales report da aka kawo mata text ya shigo wayarta. Tana dubawa ta ga Dr Mansur ne wai tana da session da shi gobe, da ƙarfe goma na safe.
Girgiza kai ta yi ta ajiye wayar. Wannan duk ɓata lokaci ne, aurenta da Adam ya riga ya ƙare ba abunda ya rage sai tone-tone, kuma ta sani shi ne zai sha kunya.
Ta maida hankalinta kan sales report ɗin. Kafin annivesary ɗinsu sun yi tallen wasu kaya da suka fitar sabbin designs da suka cire 10% na kuɗin suka tallata a matsayin *Anniversary Sale*. Tun daga lokacin da suka fara tallata kayan suke samun sales amma bai kai irin cinikin da aka yi daga ranan da bikin anniversary ɗinsu ya kwaɓe zuwa yau ba. Duk da an janye 10% discount mutane sai placing order suke. Kusan yadda maganar aurensu ya trending ya karaɗe duniyar social media sai ya zamana kamar dan gulma mutane ke son siyan kayansu.  Haka nan da page ɗinta na Mrs Maidoki a instagram da na brand ɗinta AdBie sun samu followers sama da dubu goma a cikin sati ɗaya.

Ta ɗauko wayanta ta shiga instagram. Har yanzu hotonta dana Adam ne a profile ɗin. Ta shiga edit profile ta fara neman hoton da zata saka. Hoton Anwar da Adnan da ta ci karo da shi suna sanye da pyjamas suna wasan bindiga ta zaɓa ta ɗaura as profile ɗinta.

Ta koma wajen suna. Wajen name dama Bie Imran El-Sayed ne a wajen amma username ɗinta Mrs Maidoki ne. Ta goge Mrs Maidoki ta ƙurawa wajen ido ta rasa me zata rubuta. To me za ta saka? Tun lokacin data fara instagram sunan da ta sa a wajen kenan, shi yasa mutane da dama suka fi saninta da hakan. She has always being Mrs Maidoki. Ko a twitter ma sunan da take amfani da shi kenan. A duniyar social media an santa ne da Mrs Maidoki ko kuma Bie Maidoki.
Ta danna B sai kuma ta fasa ta typing *simply Bie*

Wani abu ne ya tokareta. Lokaci guda hawaye suka fara zubo mata. Shi yasa aka ce ba za ka iya canja uba ba amma zaka iya canja miji. Bata taɓa kawowa wai akwai ranan da za ta tsani sunan Mrs Maidoki ba. A da yadda take ji da sunan ko a lahira za ta so a kirata da Mrs Maidoki.

MR and MRS MAIDOKIDär berättelser lever. Upptäck nu