01

132 3 0
                                    

               *MR & MRS MAIDOKI*

                    

©AzizatHamza2023

                                   01

                                ***

*Date 03-03-2018*

Mr & Mrs MAIDOKI ne rubuce ɓaro-ɓaro a bangon ƙaton hall da ke cikin shararren hotel ɗin nan na Transcorp Hilton da ke Abuja, sannan HAPPY 10yrs ANNIVERSARY ya biyo a ƙasan sunan. A gefen rubutun kuma ƙaton hoton mata da miji ne cikin shiga na alfarma. Namijin dogo ne, baƙi mai haske, yana sanye da babban riga na shadda fara da ta sha aikin hannu da zare mai kalar ruwan gwal. Sai kuma ita macen, fara ce, tana sanye da farin designer wedding gown haɗe da farin turban da ya matching gown ɗinta. Daga hoton za ka gane cewa su ɗin 'ya'yan masu ƙumbar susa ne.
Ah! To! Wa zai kama katafaren hall ya kira mutane don kawai a taya shi murnar cika shekaru goma da aure a 2018 idan ba ma su naira ba.

Hayaniyar mutane ya cika ko ina domin mutane sun fara hallara dan gudanar da wannan bikin ANNIVERSARY.
A can wani ɗaki kuma duk dai a nan hotel ɗin wata mace ce zaune kan gado wata make up artist na tsantsara mata kwalliya. A wannan hotel aka yi dinner aurensu shekaru goma da suka wuce, shi ya sa suka zaɓi yin bikin Anniversary a hotel ɗin saboda ya tuna musu cewa a nan ne mafarin komai.
Duk da dai a masallaci aka ɗaura auren bana tunanin sun yi tunanin komawa masallacin da aka ɗaura auren dan su ba da abin sadaka bisa tunawa da cewa a fa nan aka shafa musu Fatiha.
Amma dai kowa da irin tunaninsa.
Wasu mabiya addinin kirista su kan yi bikin vow renewal, wato bikin sake maimaita alƙawurran da suka ɗauka yayin ɗaurin aurensu a coci. Za a sake ɗaukan alƙawarrin together forever, till death do us part. Duk da dai babu irin wannan al'adar a musulunci kaman dai Mr and Mrs Maidoki suna ƙoƙarin koyi ne da al'adar vow renewal.

Shi bikin Anniversary kaman bikin Birthday ya ke. Al'ada ce da ta samo asali daga turawa. Amma kasancewar boko ya ratsa ko'ina a duniya musamman ƙasashen Africa, da bikin Birthday dana Anniversary duka 'yan Africa suma sun ara suna yi.
A Nigeria dai bikin Birthday ya zama ruwan dare a cikin mutane amma kuma bikin Anniversary sai 'ya'yan wane da wane da kuma gogaggun wayayyu ke girmama bikin.

Mr and Mrs Maidoki gogaggun 'yan boko ne sannan 'ya'yan masu faɗa a ji ne a ƙasar dan haka babu wanda zai ɗaga murya na cewa me yasa za suyi bikin anniversary.
Kusan tun kafin su kai shekara goma da aure suke tanadin zuwan wannan rana. Sukan yi bikin Anniversary duk shekara amma bikin yana ta'allaƙa ne a iya cikin gida kawai, wani lokaci kuma a lokacin Anniversary ɗin sai su tafi turai vacation su je su yi murnan bikin a can.
Sai dai wannan karan akwai banbanci. Shekara ɗai ɗai har goma kenan da aurensu dan haka dole su girmama wannan rana, su kuma celebrating bikin tareda ɗaruruwan mutanen da suka gayyata.

Wacce ake yi wa kwalliyar ita ce Mrs Maidoki, wato mata ga *Adam Salihu Maidoki*.  Ana yi mata kwalliyar ƙawayenta uku da ke wajen na kambama ta da cewa ita ɗin fa Amarya ce dan har yanzu da ƙuruciyarta babu abin da ya chanja daga shekaru goman da suka wuce.
Idan babu banbanci a fiska akwai banbancin shekaru akwai kuma banbancin kasancewarta uwar 'ya'ya biyu.

"Bie wai ina Labiba ne?, ita ce ya kamata ta yi chief bridesmaid yau fa?" Ɗaya daga cikin ƙawayen Mrs Maidoki ta faɗa.

Sunan Labiba da Bie ta ji ya sa ta tuno da abinda ta gani wata biyu da suka wuce wanda ya ruguza duk wani sauran farinciki da ta ke da shi a cikin aurenta.

Labiba babbar ƙawarta ce da su ka yi makaranta tare kuma ita ta mata babbar ƙawa a lokacin bikinta.
Labiba ce dalilin da ya sa a yau ta tsani mijinta Adam.

Wannan anniversary da za a yi shine abu na ƙarshe da zai haɗata da Adam.

"Ina Amaryanmu, ba ku gama ba, tun ɗazu ku ake jira fa, Ango ya shigo"

MR and MRS MAIDOKIWhere stories live. Discover now