RAMUWAR GAYYA

By Feedohm

1.5K 91 3

Revenge More

02
03
04
05
06
07
08
09
010
01
11
012
013
014
015

016

218 10 2
By Feedohm

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*016*

     **Cikin dakiya Baffa ya amsa sallamar, tare da basu umarnin shigowa ciki, kai tsaye suka kuwa kutso kai har cikin ɗakin sa, suka samu waje suka zazzauna, yayin da suka yi musabaha da juna.

Kallon ɗaya zaka ma ladan sani ka tabbatar da baya cikin hankalin sa, ya rusuna kusa da Baffa kan sa a ƙasa, tashin hankali soma faɗin "Sunana Malam Sani ni ne mahaifin Jafar.!

Baffa ya gyaɗa kai yana faɗin " Maraba, ya iyali.?

Wani takaici haɗe da bakin cikin furucin Baffa ya sanya hawaye masu zafi fitowa daga idon ta, ta juyar da kai haɗe da sakin wani ɗan siririn tsaki. Yayin da Abban Ilham ya miƙe tsam ya bar ɗakin, shi kan shi wani irin tuƙuƙi zuciyar sa ke masa, bare da ya fahimci gaskiyar abunda ke faruwa, da ya gane wancan la'anannen Jafar ɗin ba ɗan ladan bane ba, domin basu baro Unguwar ba sai da suka je gidan iyayen bogin da ya turo, yayi ƙwafa, Sam surukin sa bai cancanci wannan cin amanar ba, bai cancanci wannan rashin mutuncin ba, yayin da ya ɗauki alwashin hukunta Jafar dai dai da laifin da ya aikata, don haka direct daga nan gidan police station ya nufa, suka je aka ƙwashe iyayen bogin da ya turo, sannan aka tasa ƙeyar ɗaya har gidan su Faisal, da zumar duk gidan uwar da yake idan aka kama Faisal ɗin shi zai nemo shi, tunda babu wanda ya san asalin inda Jafar yake zama.

  A gida kam cikin matsanancin tashin hankali Ladan Sani ya ƙara rusunawa saboda darajar Baffa ya ke gani yana faɗin "Alhamdulillahi, Malam wani batu nake ji mai matuƙar mamaki da tashin hankali, wancan bawan Allah da ya fita yazo yana shaida mani, irin ɗibar albarkar da wani yaro ya maka, wanda wai ni na aiko da ƴan uwana nemawa yarona Jafar auren ƴar ka! Wallahil Azim ban san da zancen ba, ban kuma aiko da ƴan uwana ba, kuma sannan wancan saurayin ban san shi ba, ba yarona bane ya turo a neman aure, yanzu haka maganar da mu ke dirowar Jafar kenan daga gurin aikin sa garin zaria, bai san zance ba, kuma na kira sa yana hanyar zuwa nan gurin domin ku shaida da idanun ku, ban san komai ke faruwa ba, sai da wannan bawan Allah ya zo gurina yanzu, sannan na ja shi har gaban ƴan uwana, kuma a gaban sa suka faɗi kuɗi aka basu su zo su nemar wa wani jafar din auren ƴar ka, dan girman Allah ka yi hakuri, Malan ba kai suka wulakanta ba ni suka wulakanta, kuma insha Allah zan sanya a hukunta waccan yaron da ƴan uwana na abunda suka aikata.!

  Baffa ya girgiza kai cike da takaici ya ce "Shi wancan ba ɗan ka bane.?

" Wallahil azim ba ɗana bane, amma zan sanya a kamo shi gaban ka, ka ji da bakin sa, sannan a hukunta shi dai dai da abunda ya aikata.!

Ya gyaɗa kai tare da dakatar da Umma dake shirin magan ya faɗin "Ba buƙatar haka, babu wanda za a hukunta a cikin su, ni na yafe masu duk abunda suka mani, don haka ka je babu komai, aikin gama ya gama.!

Ladan ya ƙara rusuna cike da takaici ya ce "Ka gafarce mu Malam.!

"Allah ya gafarta mana baki ɗaya.! Baffan ya faɗa yana murmushin yaƙe.

Ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da faɗin "Mungode, Mungode Malan.!

"Ba komai.! Baffa ya faɗa cikin ƙosawa da zancen sa, domin har ga Allah duk juriyar sa, ransa yayi masifar ɓaci bare ma da ya ƙara sanin yaudarar da Jafar ya mashi.

  "Dan girman Allah Malan, tunda har abun ya zamana haka, ni ina roƙan ka da darajar fiyayyen halitta, da ka taimaka ka bawa yarona Jafar auren wannan ƴar taka, saboda duk abunda ya faru, ta dalili na ya faru, dan Allah kar ka ce mani a'a, ka dubi girman Allah malan, ni ina nemawa ɗana auren ƴar ka, domin babu wanda bai zai yi ƙwaɗayin haɗa zuri'a da kai ba, ina roƙan da ayi komai yadda aka tsara, na sani ɗana ba zai taɓa ƙin aminta ba, domin abun alfahari ne a ce ya auri ƴar ka.! "

Kai tsaye Baffa ya ce "Bazan iya ba ɗan ka auren Aminatu ba."

Ya ɗago da sauri yana tambayar "Me yasa.?

Baffa ya ce "Ba sauri nake ba! Ban kuma gaji da Aminatu ba, ina nufin ba neman kai nake da ita ba, ka bar mani ƴa ta har zuwa lokacin da Allah zai kawo mata miji nagari."

"Ba haka nake nufi ba Alaramma, ka dubi girman Allah ka duba wannan lamarin.!

"Ka je zan yi shawara.! Baffan ya faɗa jin yana neman ɗaure sa da igiyoyi.

"Shi kenan, anjima zan sake dawowa tare da yaron na wa."

Bai ce mashi komai ba, ya miƙe ya fita, sai dai baya jin zai iya bada auren Amina a wannan lokacin.

Dakin yayi shiru baka jin motsin kowa na ƴan mintina, sannan Baffan ya juyo ga Umma ya ce" Idan babu wani abu zaku iya tafiya, Allah ya tsare gaba.!

Umma ta ce "Dan Allah ka aminta ayi auren ta da ɗan wannan ɗin tunda shi ya roƙa, wallahi auren shine rufin asirin mu baki ɗaya.!

" In aurar da ita da ciki.? Ya kafe ta da ido.

Yaya ta yi karaf ta ce "Baffa yanzu zan je a zubar dashi, zan kai ta asibiti."

"Da kin yi kuskuran da zaki jima nan dube ki ba Salima, babu wanda zai zubar da ciki."

Su duka suka zuba mashi ido cikin tsananin mamaki, kafin Umma ta share ƴan guntayen hawayen ta ta ce "Idan ba'a zubar ba me za a yi dashi? Haba dan Allah, wannan wace irin magana ce.?

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Karuwai su kan yi cikin shege su haife yaran su, su raina, sai ni da ƙaddara ta faɗa kan ƴa ta zan zubar? Shin me yasa zan kashe rai? Kin san wanene a cikin nata? Kin san wa zata haifa? Baƙya tunanin na yi ma mutane asara babban malami? Aminatu zata haifi ɗan cikin ta da yardar Allah, sannan zai raine sa kamar yadda na rai ne ta, wannan ƙaddarar gidan nan ce, Salima ki dawo mani da ƴata gida, ki faɗa mata babu inda ya fi gidan Baffan ta sirri da gata.!"

Umma ta ce "Ƙaddara? Wannan wace irin mummuna ƙaddara ce? wallahi yaron nan ya zalunce mu, kuma Allah ba zai bar sa.!

"Ya dai zalunci kansa..! Ya bata amsa tare da miƙe wa tsaye ya kabbara sallah, alamun ya gama da zancen.

Da kuka Umma ta bar ɗakin, ta sani sarai tun da har ya ce bazaa zubar ba, ta zauna, kuma babu wanda ya isa ya zubar dashi, ta ɗaura alwala sannan ta shige ɗaki ta shinfiɗa abun sallah ta cigaba da kai ma Allah kukan ta, yayin da yaya ta bi ta ta samu gefen katifa ta zauna ta tallabe kumatu, ai kam Umma na sallame raka'a ta biyu ta cilla mata harara tana faɗin "Za ki bar mani ɗaki ko sai na ci mutunci ki? Wai har da ke zaki munafunce ni salima.?

Ta fashe da kuka "Umma abunda nayi shine ko wacce yaya zata yi ƙanwar ta, dan Allah ki yafe mana, na yi don rufa wa ƴar uwata asiri.!

"Asirin banza? Yanzu ya rufo? Na ce asirin ya rufo? Da tun farko kun sanar damu da abun bai kai haka ba, wallahi ki bar mani ɗaki tun kafin in rufe ki da duka.!

Ta miƙe jikin ta na ƙyarma ta bar ɗakin, yayin da ta fita daga gidan gaba ɗaya ta nufi gidan ta, zuciyar ta na wani irin tuƙuƙi, ita kanta zata dawwama tana roƙa wa Jafar fitinar duniya, sai ya tabbatar da ya taɓo ƴar gidan masu gemu kamar yadda ya furta, yayin da wani sashe na zuciyar ta ke addu'ar Baffa ya aminta da auren Aminatu da aka bi ɗa yanzu, domin gani take hakan zai fi ƙwanciyar hankali.

***

   Shima kam Jafar suna juyawa ya ƙwashe kuɗin sa ya sanya aljihu, yayin da yake jin kaf burin sa ya gama cika, ya yi abunda ya ke so a banza ga kuɗi sun dawo a wofi, don haka kai tsaye ya nufi shagon sa yake zaune, ya tattara kayan sa cikin traveling bag, ya zuba komai da komai ya kulle, ya fito ya bada wani yaro makullin ya ce ya miƙa cikin gidan, ya tsayar da machine, ya haye ya nufi tasha mota, in da ya hawo motar da zata kai shi Zaria gida, kuma cikin sa'a bai fi minti biyar ba motar ta cika, yayin da wani daɗi ya ratsa sa lokacin da suka fita daga ɗanɗagoro, yana jin gaba ɗaya yayi banƙwana da Katsina har abada, ba zai kuma dawowa ba, ya saki lallausan murmushi ya buɗe marfin wayar sa, ya zare sims card ɗin dake ciki, ya jefa a baki ya taune yana dariyar mugunta.

A fili ya ce "Meenari, Faisal, bye bye forever, ba zaku ƙara ganin Jafar ba har ƙarshen rayuwar ku.!

Ya buɗe wallet ɗin shi ya fiddo sabon sim card ya sanya a wayar, ya kunna, sannan yayi dialing number da yayi saving da Yaya Habib.

Ringing ɗaya a na biyu ya ɗauka, cikin sanyin murya mai ratsa zuciya ya ce "Assalamu Alaikum.!

Jafar ya ce "Wassalaikassalam, Yaya, ya gida? Ya aiki.?

"Alhamdulillahi.!

"Dama zan faɗa maka ne ganin nan zan dawo gida.!

"Lafiya.?

Jafar ya fashe da kuka cikin motar, ba tare da la'akari da mutanen dake ciki ba yana faɗin "School ne aka koro mu.! Maƙaryanci bayan ya fi shekara biyu da kora, bai faɗa ba don kar a hana shi kuɗin registration.

"Garin yaya Jafar? Me kayi.? Ya Habib ya faɗa cikin taushin muryar sa.

Ya ja majina ya ce "Idan na zo zan faɗa maka komai."

"Alright, Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi, but ka sani bazan ƙara sanya kaina a sha'anin karatun ka ba.!

"Dan Allah ka yi hakuri.!

Yayi banza dashi, Jafar ya kuma fashewa da kuka yana faɗin "Wallahi ba laifi na bane, abokina ne aka kama yana satar amsa, kuma kusa dani yake zaune.!

"Bara yiyu don na kusa da kai yayi laifi ba, a kore ka, ka ga ni yanzu na shigo Katsina, ka jira idan na gama abunda nake zan neme ka, gobe da safe sai muje school ɗin, koma menene na ji."

Cikin sauri ya ce "Yaya ai na riga na tafi gida, yanzu haka na wuce hunƙui.!

"Ok.!

"Amma me ka zo yi Katsina.? Jafar ya tambaya domin ya san Ya Habib bai da wata alaƙa da garin, hasalima bai taɓa zuwa ba.

"Tare da Jafar muka zo amsar wani saƙo.!

"Jafar.? Ya tambaya a sanyaye.

"Yeah, baka san shi ba, friend ɗi na ne, ɗan Katsina."

"Amma yaushe zaka dawo.?

"Yau na so, but suddenly wani case ya taso daga gidan su, I have to wait sai ya ƙare sannan mu juyo tare."

A take ya ji gaban sa yayi mummunar faɗuwa, yana so ya tambayi Habin wanene Jafar ɗin, wane kuma irin case ne, amma sam babu fuskar haka, don haka ya yi ma shi sallama ya yanke wayar tare da jingina kan shi jikin glass ɗin motar kamar mai ƙirga bishiyoyin da suke wucewa.

*RAMUWAR GAYYA Feedohm.*
*RAMIN MUGUNTA Slimzy.*

Mai buƙatar tagwayen littafai biyu. 300 ne kacal gaba ɗaya, mai son guda ɗaya zai biya 200.
Payment.
👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank.
Amina Jibril.
Shaidar biya.
07042277401.

Or

Katin Mtn
08036953516.
Shaidar biya ga ɗaya daga cikin waɗannan lambobin.
08036953516 ko 07042277401

*FEEDOHM.💞*

Continue Reading

You'll Also Like

439K 6.2K 32
Rajveer is not in love with Prachi and wants to take revenge from her . He knows she is a virgin and is very peculiar that nobody touches her. Prachi...
1.2M 95.1K 40
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
672K 35.6K 20
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...
369K 11.5K 35
The Sokolov brothers are everything most girls want. Intimidating, tall, broody, they are everything to lust after. Not that they... particularly car...