02

386 15 1
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM💞.*
Wattpad@Feedohm.

*2*

    **Kalmar lagwani ta mashi ciwo ba kaɗan ba, ya kalle ta cikin ɓacin rai lokacin da yake niyyar bar mata tabarmar, ya ce "Ni kike kira da lagwani Fadila.?

Ta rafka mashi harara ta ce "Ashe ma ka ji me na ce? Yo ba lagwanin bane? Abu yi ɗaya ta lauye sai ka ce ruɓaɓɓar ayaba..!

"Ƙarya kike wallahi kin sani sarai ni namiji ne. " Ya faɗa a harzuƙe.

Ta kalle shi sheƙeƙe tana faɗin" Sai fa namiji, minti ɗaya an buga ya fita fiiii kamar riƙaƙƙen fitsari, ita kuma ta koma ta langwaɓe kamar ƙwaɗaɗɗen latas, malan dallah ka dinga karanta littafan hausa anan zaka ga namiji ba tamiji, masu share dare rankatakam suna abun arziki da matayen su. "

Takaici ya hana sa ƙara ce mata komai, ya juya da niyyar bar mata daƙin sai tsinkayar muryar ta yayi tana faɗin" Idan ka fita ka taho mani da tsire, dan Allah mai kitse kitse nake so. "

"Ba za'a siyo ba, ki je mazan littafan su siya maki." Ya faɗa kai tsaye.

"Uban kuturu  kuma yayi kaɗan wallahi, kai nake aure ba su ba, don haka kai zaka siyo shi, kuma ka ƙwana da sanin yau na fara wankin mahaifa, duk masifar ka sai ka kusance ni, ni haihuwa na ke so." Ta ƙarashe maganar ta ƙanƙance ido saboda azabar fitinar dake cin ta.

Haka ya juya ya bar mata gidan, yayin da ya nufi gidan mahaifiyarshi dake nesa kaɗan da su, a can ya samu ta zubo mashi ɗan wake da mai da yaji, ya ci sosai ya bi da ruwan randa, sannan ya shigingiɗa tana tambayar sa ya su Habibu.?

Ya lumshe idon sa "Lafiya yake Inna."

"Ɗan albarka, Allah ya ƙara tabbatar mashi da ita." Ta faɗa tana faɗaɗa fara'ar ta.

Bata da wata fira da ta wuce ta Habibu, tare da yabon shi, sannan ta sake jaddada ma Jafar ɗin ya riƙe amana, ya ƙyautata mashi kamar yadda suma yake ƙyautata masu. Sannan ta dawo ga Fadila, tana tsegumin har yau shiru abu shekara biyar amma ko ɓari bata taɓa ba, ita ta rasa wake da matsala cikin su? Anya ba zai ƙara aure ba? Ita fa bata so ta mutu ba taga jikan ta ba.

Wayar shi ta ɗauki kuwwa don haka ta dakata da zancen ta, ya kara a kunne da sauri ganin sunan Yaya Habib dake yawo a screen ɗin.

Habib ɗin yace dashi, ya zo office ya same shi zai bashi saƙo ya kai gida.

Jiɓi ya share yana faɗin "To ganinan zuwa."

Yayi mata sallama ya tafi tana faɗin "A gaida Habibun, ka ce Allah ya mashi rahama ya ji ƙan iyayen shi."

Shi dai amin ya ke faɗa wacce iyakar ta laɓɓan sa.

Ba dan ran shi ya so ba, haka ya amshi saƙon ya nufi gidan da shi, yayin da gaban sa ke dukan uku uku, da bismillahi ya tura ƙofar falon sannan ya kutsa kai ciki, cikin sa'a babu kowa, don haka ya sauke ajiyar zuciya tare da aje ledar bisa carpet ya juya da azama da nufin ficewa..

Yana gab da fita daga falon ya tsinkayi muryar ta ina tambayar "Waye anan.?

Gaban sa yayi mummunar faɗuwa" Ya salam," Ya furta a zuciya, sam ba haka ya so ba, so yayi ya fice ba tare da na fito ba.

"Who's there..? Na kuma faɗa a tsawance.

Ya lumshe ido, ba tare da ya jiyo ba ya ce "Ya Habib ya ce a kawo maki wancan saƙon.

  Duk da na fahimci ko waye amma hakan bai hana ni faɗin "I didn't ask you me ka aje, I just ask wane sakarai ne anan wuri? I mean wane dabbun arab ne ya shigo mani falo kamar tsohon ƙwarton."

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now