015

85 4 0
                                    

  💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*015*

      Jafar kam tunda ya zauna yake zabga tsaki, ya yi tsaki ya fi sau hamsin, har Faisal ya gama sallamar mutanen dake gurin sa ya juyo yana faɗin "What ups.?

Ya ƙara kan dogon tsaki tare da kawar da kai gefe yana faɗi "Mts, ni da wancan tabaɓɓen mutumin mana.!

"Wa ke nan.?

"Wancan bagidajen malamin zaure mana, shi yasa fa ni duk ban yadda da waɗannan surkullan ba, amma ka matsa mani na je, yanzu dan Allah ina amfani? Nayi wasting 5k ɗina for nothing.!

" Me ya maka.?

"Makaryaci, he told me idan nayi applying wannan ƙwallin muka haɗa ido da ita, duk abunda na tambaye ta, ba ta isa ta ce mani a'a ba! Sai da na yi sati ina rangaɗa shi kamar baƙauyen ƙwarto, without asking her anything, amma yau na tambaye ta ta mani tunkiya.!

Faisal ta ƙwalalo ido waje ya ce "Me kake nufi.?

"Na faɗa maka ta mani tunkiya, ta ɓata mani rai har na kasa controlling kai na, nayi revealing komai da komai gashi yanzu komai ya watse."

"Kar dai ka ce an yi baran baran.? Ya ƙarashe maganar tare da ware hannayen sa.

Cike da takaici Jafar ya ce "Sosai ma kuwa.!

"Ba zata gyaru ba.?

"Ta ina? Ina gaya maka na fayyace mata komai."

Faisal ya ke ce da dariya yana faɗin "Har ka ci sadakin ka kenan? Sau ɗaya fa kawai? Gaskiya na tausaya maka, amma mutumina wannan yarinyar ta ci banza, idan da a ce waje ka je, da waɗannan 24k zaka ci lafiyayyun ƴan mata har biyar."

Jafar ya ƙara harzuƙa ya ce "Uban wa ya ce ta ci banza? Wallahi ba ta ci banza ba, sai na karɓo kuɗina."

Faisal ya kece da dariya yana faɗin "How? Ka ga ba fa zata yiyu ba! Kawai ka zama abun tausayi, ni dai ka yi ƙoƙarin biyana kafin ka tafi, don ban ci nanin ba kuma nanin ba zata ci ni ba."

"To an ce ba za a biya ka ba.?

"Ni dai ina faɗa maka ne, don na san babu ta inda kuɗin zasu fito, tunda ba zaka yi ma ƴar mutane ciki ba sannan ka je ka ce su baka kuɗin ka.!

"Zaka gani, ina ce ba'a aure sai an yi test.?

"Hakane, to menene.?

"Good, I will use that opportunity, a mai do mani kuɗina, she's pregnant, gobe early morning zan tafi asibiti, sannan in kira tsohon ta ya zo da ita asibiti a gwada mu, da an ga cikin zan miƙa hannu a maido mani da kuɗi na, shi kenan.!

"Kai ka tabbatar ma da tana da cikin ne.?

Jafar ya dalla mashi harara yana fadin "5 weeks ma kuwa, ko an faɗa maka ban iya jefa ƙwallo da ƙyau bane.?

"Idan ta ce cikin naka ne fa.?

Ya taɓe baki "Zan tambayi agidan uwar wa na mata? Waye shaidan ta? Ni fa ko? Dama a ce ko sau biyu zuwa uku na latsa da zan iya hakura, amma sau ɗaya kawai fa? Kuma shima sai da ta bini da tsinuwa da la'ana.!

***

Yaya kam kiran Umma tayi da daddare sanar da ita ina gidan ta, kuma anan zan ƙwana, duk da Umma tayi faɗan me yasa na tafi ban faɗi mata ba, daga ƙarshen dai ta ce in ƙwanan, don Yaya ce mata tayi aiki zan mata. Ita kuma yaya ta yi hakan ne da zumar zuwa dare mu yanke shawarar hanyar da zamu ɓullowa lamarin, kuma a cikin daren yaya ta ce zuwa safe zata sayar da zoben ta na zinari sai mu je wani private hospital a zubar da cikin ba tare da su Baffan sun san me ke faruwa ba, idan abun ya lafa sai ta sanar da su.

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now