013

65 2 0
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*013*

  
    ***Tunda na gama kalaci wajen goman safe na ɓingire a gurin na ko kofin da na sha kunu ban ɗauke ba, na cigaba da sababben baccin da na ɗaura ma kaina a wannan ɗan datsin, babu cas bare as, ban kuma farka ba sai da azahar, shima Umma ce ta tayar da ni in yi sallah, Allah ya sani da ƙyar na kammala addu'ar yadda na ji wani sabon bacci na fizgata, na shigingiɗa bisa abun sallah da niyyar in ɗaura daga inda na tsaya, sai dai ƙamshin miyar alayyahun da Umma ta aje tsakar ɗakin ya dakar mani hanci, yayin da wani amai ya taho mani, na yunƙura da sauri na fita daga ɗakin da gudu na, na tsugunna bakin magudada na cigaba da sheƙa shi yadda kasan zan amayar da ƴan ciki na, shi kan shi aman nawa wani irin ƙarni yake fita daga cikin sa, don haka na matsa daga inda na sheƙa shi na ɗauraye bakina tare da komawa ɗaki na bi lafiyar katifa ina faman toshe hanci.

"Amina.! Naji Umma ta faɗa daga inda na barta tsaye riƙe da ƙwanon tuwo, ashe ko motsawa ba tayi ba daga gurin.

Na ce "Na'am Umma..!

"Me ke damun ki.?

A hankali na ce "Babu, dan Allah ki fita da miyar nan, wallahi ƙamshin ta babu daɗi Umma, sai tayar mani da zuciya ya ke."

Ta ƙura mani ido tana kallona yayin da na gyara ƙwanciya ta ina turo baki, ni kaina mamakin sauyin nawa nake, abubuwa da yawa sun sauya mani, a da ban da abunda nake so irin miyar alayyahun, amma yanzu ko ƙamshin ta bana buƙata, ga kifi ma da na tsana babu gaira ba dalili, da kuma uwa uba tuwon da na sahale ma kaina cin sa baki ɗaya, ga ƙosai ma yanzu ko kallon sa bana buƙata, sai dai in sha tsuran kunu ko koko.

"Ta shi zaune." Na tsinkayi murya ta tana faɗa babu alamun wasa a cikin ta.

Na turo baki haɗe da kau da kai gefe guda ina faɗin "Umma dan Allah bacci nake ji, kuma wallahi miyar ki ta takura mani."

Ta daka mani tsawa "Za ki tashi ko sai na ci maki mutunci.?

"Naa tashi..! Na faɗa ina zumɓurar baki.

"Ki faɗa mani me ke damun ki a ƴan ƙwanakin nan ki ke faman zaryar amai.?

"Babu komai fa Umma."

"Wallahi ƙarya kike.!

"To shi amai dole sai da dalili zan yi shi Umma? Kawai ni dai idan ƙamshin abu bai yi mani ba sai in ji ya taho, koko zan danne sa in hana sa fitowa.! Na faɗa a hasale ina kallon ta, domin a ƴan ƙwanaki nan ina da saurin hasala, abu kaɗan sai in ji raina ya ɓaci.

"Wannan watan kin yi al'adar ki.? Ta jefo mani tambayar da banga amfanin ta ba wannan maganar.

Na girgiza kai ina zumburar baki, a hankali na sadda kai na ƙasa ina faɗin "Tayi wasa har yau bata zo ba.!

"Ƙwana nawa ta ƙara.?

Raina ya soma ɓaci, har ga Allah na gaji da waɗannan tambayoyin, a hankali na ce "Dan Allah ki bari idan na tashi daga baccin sai ki tambayi komai kike buƙata.!

Saukar marin da na ji a fuska ta ya sanya ni faɗin "Sati biyu fa kawai ne, kuma ai na ji wasu na faɗin sai su yi sama da wata uku basu gan ta ba, kuma meye haɗin amai na da al'ada? Bare har mari ya ratso Umma.?

Wani sakaran mari ta ƙara tsinke ni dashi, ta fizgoni tsaye, tare da ɗage rigata sama tana kallon ƙirjina, ni kaina tunda suka gama yi mani ciwo naga sun ciko sosai, ta mayar da kallon ta ga fatar jikina da ta ƙara haske haɗe da sheƙi, na kau da kai gefe guda, na zubar da yawun da ya taru a bakina cikin ɗakin, don bata bani damar fita waje ba bare har in zubar.

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now