012

76 4 0
                                    

  💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*012*

      ***Lokaci guda na rufe babin soyayyar Jafar, ba goge lambobin sa daga wayar Umma tare da danna shi cikin blacklist ta yadda kiran sa na shigowa ya ke yanke kan sa, don kuwa wata irin tsana nake masa mara misaltuwa, tsanar da ban taɓa yi ma wani mutun ko dabba irin ta ba, wacce har ta tilas ta ni zuwa ɗaki Baffa da kaina ina kuka haɗe da roƙan shi, akan ya janye maganar aurena da Jafar, na fasa, ba zan aure sa ba.

Ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin "Kina buƙatar a ƙara lokacin auren ne koko ya kike nufi.?

" Ƙwata ƙwata auren ne bana yi Baffa.!

"A kan wane dalili ne zamu ce masu mun fasa Aminatu.? Baffa ya tambaye ni tare da kafa mani manyan idanun sa masu matuƙar daraja a fuska ta.

Cikin kuka na ce "Ni dai bana son sa Baffa, ka yi ma girman Allah ka fasa auran mani shi, ni ba zan yi aure ba.!

Ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin" Shin kina da dalilin fasa auren sa Aminatu koko ƙaramin mutun kika mai da ni.?

Ba wai ba zan iya buɗe baki in faɗa ma Baffana fyaɗe ya mani ba ne, matsalar shin zai ɗauki hakan a matsayin fyaɗe koko zai aje shi a matsayin da Yaya Salima ta aje shi? Muddun ya ɗaura laifin a kaina Wallahil Azim na shiga uku na lalace, domin babu wata yadda ko amana da zai ƙara shiga tsakanin mu, wasu hawaye masu ɗan karan zafi suka sauko saman kumci na lokacin da ya ke faɗin "Idan ba ki da dalili, ƙya iya tashi ki tafi ki bani wuri, amma ki sani ba ki isa ki zubda mani mutunci ba, ba kuma zan sauya magana ta ba, da ma ace na ji dalilin na ki da sai na ɗaura shi a mizani, amma na fahimci shaiɗan ne ke son ribatar ki.!

Shin zubewar mutunci har na nawa? Na miƙe jiri na ɗibata, na koma ɗaki na zube ƙasan leda na shiga rusa kuka babu ko ƙaƙƙautawa.

Umma na zaune bisa abin sallah ta kalle ni cike da damuwa ta ce "Ba zan tursasa ki ba ki faɗa mani abunda ke ranki ba, amma ina baki shawara da ki roƙi Allah ya zaɓa maki mafi alkhairi Aminatu, wani sa'in mukan ƙi mutun ya zamto shine alkhairin mu, wani sa'in kam mukan so abunda ba alkhairin mu ba..!

" Jafar ba alkhairi ba ne Umma, wallahi ba alkhairi bane shi, mugu ne, ma ci amana, kuma mayaudari, bana son sa Umma, bana ƙaunar sa har cikin raina, ki taimaka ki fahimtar da Baffa.! Na ƙarashe maganar cikin wani irin gujin kuka.

"Da kin faɗi dalilin rashin son sa, da wallahil azim babu mai maki auren dole Aminatu, amma ke kika kawo wannan mutumin, an kuma amsa masu da an basu har an sanya rana, sai yanzu zaki tsiro da wani abun? Ki ji tsoron Allah kar ki zubar da ƙima da mutuncin mahaifin ki wajen son zuciya..! Ta miƙe tsam ta bar mani ɗakin.

Shin wai so kike in kurma ihu in faɗa masu ɗan iska ne? Ja na yayi gidan su ya lalata mani rayuwa ta ƙarfin tsiya! Zuciya ta ta buga da ƙarfi lokacin da kalaman yaya Salima suka bijiro mani _Wannan ba fyaɗe bane Amina, Son zuciya ne irin naki, domin ke kika kai kanki gidan su Jafar, ba ta ƙarfin tsiya ba ya ɗauke ki._

Na fashe da kuka amma ai ce mani yayi Mahaifiyar shi bata lafiya, ya tursasa mani zuwa dubata! Sai dai da ƙafa ta na je, ba ɗauka ta yayi ba, amma duk da haka wallahi bana ganin laifi na, ƙaddara ta ce kuma ban isa in wuce ta ba..

***

Sati biyu gam nayi ban kula shi ba, ko ya canza number ya kira waya bana ɗauka, haka kullun zai zo ƙofar gidan mu ya ƙaraci tsayuwar sa ya tafi ko fita bana yi, ban san ya aka yi ba, ranar lahadi da marece sai ga Baffana ya shigo ɗakin ran sa a ɓace, ina zaune ina tilawar ƙur'ani, cikin fushi ya ce "Idan kin gama ki tashi ki fita waje Jafar na neman ki, kuma muddun na zagayo na iske ba ki je ba, wallahi ran ki sai yayi mummunan ɓaci, kar ki maida ni mutumin banza mana, yaro sai zarya yake kina wulaƙanta shi, shekaran jiya ya turo iyayen shi a baki hakuri amma a banza, to ki sani ko Allah dai muna mashi laifi ya yafe mana bare ke gayyar wofi, kuma kin san ba son gaske kike mashi ba, wa ya ce ki turo shi gare mu.? Ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba, ya ƙarashi faɗan ya fita.

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now