05

58 6 0
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM.💞*
Wattpad@Feedohm

05

    ****Tunda na fara sanar dashi an ce yazo ya nemi iznin gani na a gidan mu, ya kafe ni da ƙyawawan idanun sa, har na dasa aya, tare da sunne ƙaina ƙasa ina murmushin jin kunya, wai ni ce ke bayani haka dalla dalla, ko da yake masifar ƙaunar sa ce ta janyo hakan, ban san yadda aka yi ya dawo kusa dani ba, sai jin hannun shi nayi cikin nawa yana murza wa a hankali, na ɗago a firgice na kalle shi, don kuwa ban taɓa tunanin hakan zai kasance ba, yayin da na janye hannuna ina turo baki, a hankali na ce "Meye haka.?

Ya shafa sajen sa, har lokacin fuskar sa ɗauke take da tattausan murmushi, a tausashe ya ce" Sorry, farin ciki ne ya sanya haka Pretty, ranar da na ɗaɗe ina jira kenan."

"Shine kuma sai ka riƙe mani hannu? Bayan kasan haramun ne? Kuma ai neman iznin tsayawa fa dani kaɗai aka ce, ba nemanaure ba..! Na faɗa ina hararar sa ƙasa ƙasa.

Ya saki murmushi mai sauti yana faɗin" To yi hakuri, ba zan sake ba, kuma ai kin san ba hali bane.!

Ɗan siririn murmushi na saki ina faɗin "Na yi."

"Da gaske.?

Na gyaɗa mashi kai ina rufe fuska ta da tafin hannuna, ganin yadda yake aiko mani da wani kalar saƙo na musamman daga ƙwayar idanun sa, kallon da na fassara da _Ke ce cikar burina Meenari._ Kallon da ke ƙara narkar da zuciya ta, Allah ya sani ina ƙaunar sa da zuciya ɗaya tal, kuma babu algulus a cikin son da nake masa.

Mu ɗan taɓa fira, sannan muka yi sallama, ya aje man ƙwalin chocolates ya fita, na raka shi har bakin hanya yana jajjada mani, insha Allahu gobe da safe zai turo, shi sam bama iznin ganina zai turo ba a nema mashi ba, a'a aure zai nema, kuma ƙanin dad ɗin shine zai zo, tunda dad ɗin yana Sweden, daɗi ya kashe ni, na miƙa mashi soyayya ta gaba ɗaya, domin na tabbata ba zai taɓa yaudara ta ba, ji fa? Yadda yake farin ciki daga cewa ya aiko..

Bayan mun rabu, na haɗu da kamal, wani ɗan matashi dake Layin gidan su Yaya Salima, ka kalle ni da fara'a shinfiɗe a fuskar sa yana faɗin "A'a Meenari unguwar ta mu aka shigo.?

Na ce" Eh wallahi. "

"Dama ina son ganin ki."

"Allah ya sa lafiya.? Na tambaya ina kallon hanya.

Ya sosa kan shi, cike da jin nauyi ya ce" Maganar da muka yi dake ce ƙwanaki, har yanzu ban haƙura ba Amina, dan Allah ki bani dama. "

  Na murmusa ina faɗin "Ina da wanda nake so Kamal, dan Allah kayi hakuri, soyayya da mutun biyu kamar yaudara ce, ni kuma bazan iya ba, ina fatan zaka cire ni a ranka."

  Na juya na cigaba da tafiya ta, sam bana jin zan iya haɗa wani da Jafar ɗina, zuciya ta kacokam tasa ce, shiyasa ko kaɗan bana shayin faɗa ma kowa shi nake so.

  Na koma gidan Yaya Salima, na ɗibarwa su Ilhami chocolate ɗin, sannan na sunkuci sauran na nufi gida kamar zan tashi sama, tsabar farin cikin da nake ciki, don har ga Allah daga farko na ɗauka zai ce mani sai mahaifin shi ya dawo kamar ko yaushe, amma sai ya ce gobe zai turo ƙanin mahaifin nashi.

  A bakin sauro na ci karo da Baffa zai je masallaci, kallo ɗaya yayi mani ya gane ina cikin farin ciki, ya faɗaɗa fara'ar sa yana faɗin "Autar Ummi daga ina kike sai washe baki kike.?

Na ce "Gidan Yaya. "

Ya murmursa, yana kallon hannu na, a natse ya ce "Me ta baki.?

Na ware hannu na fito da chocolate ɗin dake hannuna ina dariya,

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now