03

85 6 0
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM.💞*
Wattpad@Feedohm.

*03*

    ***Yadda yayi tsaye yana kallona ya tabbatar mani da maganar ba ƙaramin kiɗima shi tayi ba, bai taɓa tunanin zan liƙa mashi wannan mummunan sharri ba, idan ya fahimta dai dai ina nufin yana neman aikata luwaɗi da Amir! Ɗan shi na cikin sa, sannan yana neman keta mutuncin matar yayan shi, wanda ya zame masu katanga a rayuwa.

"Hasbinallahu wa ni'imar wakil, wallahi ƙarya take Yaya Habib sam ban aikata abunda ta faɗa ba..! Ya faɗa idanu sa jawur kamar garwashi.

Ya Habib ya daka mashi tsawa" Kar ka maida ni shashasha Jafar! ko an gaya maka banga lokacin da ta ture hannun ka daga jikin ta ba? Ko ni makaho ne banga lokacin da ka ɗaga hannu ka mare ta ba? Ka ci amanata Jafar, matata kake nema da lalata, ga ƙaramin yarona shima ka son ka lalata mani shi wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, ashe wannan ne dalilin da ya sanya Meenari ta tsane ka? Tun yaushe kake neman ka keta mata haddi Jafar.?

A ruɗe ya ce "Ka fahimce ni Yaya Habib..!

Wani lafiyayyen mari ya shiga kifa mashi haggu da dama, yayin da idanu shi suka ri ga suka kulle ta ko'ina yake kai mashi duka yana kuka, kalmar butulu, ma ci amana ita yake furta wa da ƙarfi.

Hawaye suka biyo saman kuncin Jafar, lokacin da Ya Habib ya ja shi zuwa ƙofar fita daga gidan, ya juyo yana kallona, cikin muryar kuka yake roƙana "Ki ji tsoron Allah Meenari, ki faɗa mashi gaskiya, ki sanar dashi sharri kika yi mani, ban aikata ko ɗaya daga cikin abunda kika faɗa ba, ki dubi girman Allah kar ki wargaza mani rayuwa Amina, na tuba ki yafe mani, ki rufa mani asiri, dan Allah Amina, ki faɗa mashi gaskiya, wallahi zan iya rasa mahaifiya ta muddun ta ji wannan mummunan labarin, dan girman Allah Amina...! Ya saki wani irin razannen kuka yana durkushewa bisa guiwowin sa, amma a haka Yaya Habib ya fitar dashi, don ba ƙaramin harzuƙa shi maganganun sa suke ba, wai ta yafe mashi? Ba zai yiyu ba komai zai faru sai dai ya faru amma sai mahaifyar shi ta san wannan mummunan aika aikar da ya aikata.

Duk da na san bala'i da masifar da na jefa Jafar amma ko a jikina, kuma na tabbatar silar haka na iya kawo gushewar mahaifyar tashi, saboda babban matsayin da ta bawa Yaya Habib a rayuwar su, saboda shine gatan su a rayuwa, asali da mahaifiyar Jafar da Mahaifin Yaya Habib uwa ɗaya uba ɗaya suke, kuma Yaya Habib shine ya ɗauke nauyin ɗawainiyar su baki ɗaya, tun daga cin su, shan su da kuma tufafi, sannan ya bawa mahaifiyar Jafar koda ɗaya lokacin da take cikin buƙatar ta, wacce da ita take rayuwa a yanzu, shi yasa ta ke ƙaunar Habib ɗin fiye da yadda take ƙaunar Jafar, domin ya mata komai na rayuwa, wanda ba zata taɓa mance hallacin sa ba, n goge hawayen da suka sauko saman kuncina sannan na juya zuciya ta tas kamar madara, ko kaɗan bana jin nadama a raina.

Shin nadamar ne zanyi? Mutumin da ya rusa mani rayuwa ta, don na rusa rasa har wani abu ne? Na ja gwaron numfashi na buɗe ƙofar a hankali na shige bedroom ɗina, inda na taras da Amir ya sha kukan sa har bacci yayi awon gaba dashi...

Na faɗa saman lallausan gadona, tare da rungume hannaye na a kirki, idona a kafe bisa silin, kusan awa biyu ina ƙwance sai ji nayi an banko ƙofar bedroom ɗin an shigo ciki, na juyo da kallona ga wanda ya faɗo mani ɗaki kai tsaye.

Fadila ce kamar an koro ta, na saki murmushin yaƙe, tare da miƙe wa zaune ina faɗin "Su Fadila ne yau a gidan? Shigo mana ciki mana, ya zaki tsaya daga bakin ƙofa."

Idon ta a makance ta faɗo gabana tana jefa mani wani mummunan kallon, na murmusa na tashi tsaye ina gyara zaman rigata, sannan na ce "Mu je falo in baki ruwa ko.?

Ta cakumi ƙwalar rigata, cikin gujin kuka tana faɗin "Me Mijina ya maki Meenari? Me ya aikata maki da ya cancanci wannan mummunan hukuncin.?

Na ce "Ruwan sanyi ya kamata ki fara sha, sannan sai ki tambaye ni duk abunda kike so, amma ki fara sake mani riga tukun, sannan mu fita anan kar ki tada mani yaro..!

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now