04

68 7 0
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM.💞*
Wattpad@Feedohm.

*04*

      ***Ina jin lokacin da ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya, ya buɗe baki a hankali ya ce da mutanen da yake tare dasu "Samuel ku jira ni a waje please, zan yi magana da madam ɗita.!

Na lumshe idanu a hankali, domin na gamsu, ina da matsayi na musamman a zuciyar sa, ta yadda ba zai iya ɓoye matsayi na ba ga duk wanda suke a tare.

Zazzaƙar muryar sa mai kama da busar sarewa ta daki kunnuwa, na lokacin da ya kira sunana cikin wani irin sauti "Meenari..! Na ji tsikar jikina ta tashi yarr.. Yayin da na ji yo muryar sa na bin dukkanin ilahirin sassan jikina.

"Pretty kina jina kuwa.? Ya kuma tambaya jin ban amsa kiran sa na farko ba.

"Ina jin ka gudan jini.! Na faɗa kamar wacce aka zare wa lakka.

Ya ce "Shi ne kika mani shiru? Ko dai fushi kike dani.?

A hankali na ce "Na me.?

Ya tausasa murya" Na ce zan kira jiya ban kira ba, kiyi hakuri, wallahi ina ƙoƙarin dialing number ki sai ga baƙin Dad daga America, dole na katse kiran na sallame su."

Na murmusa cike da annashuwa, a shagwaɓe na ce "Ai ba ka laifi Yaya Jafar, ina fatan dai kana lafiya ko.?

"Kema kin sani! I'm incomplete without you Pretty.! Ya faɗa a raunane.

Tausayin sa ya kama ni, Jafar bawan Allah, baya taɓa samun natsuwa idan bai ji murya ta ba, ko ga ganni, gashi mahaifin shi yaƙi zama ƙasar bare ya turo ayi maganar auren mu kamar yadda ya faɗa mani.

"Yayana ko da waya ko babu waya kana nan a zuciya ta, kar ka damu, Meenari na matuƙar ƙaunar ka fiye da tunani.! Na faɗa a sanyaye.

" I know Pretty, Shi yasa nima nake son ki, fiye da rayuwa ta.!

Shiru ya ratsa gurin, yayin da mu ke sauraren bugun zuciyar juna, kafin ya numfasa ya ce "Me zaki tanadar mani yau Pretty nah.?

Cikin ɗoki na tambaya "Zuwa zaka yi.?

"Yes.!

Na turo baki kamar yana kallona, a shagwaɓe na ce" Ba wani nan, ai nasan ha zuwa zaka yi ba, don ko shekaran jiya haka ka ce mani zaka zo, ka sa na je gidan yaya nayi ta zaman jiran ka.!

"Amma ai na bayar da hakuri ko Pretty? Kuma na faɗa maki ina shirin zuwa sai ga private jet dad ya aiko a tafi dani Dubai, emergency meeting, ya na iya Pretty? Kinga dole na je, amma insha Allahu yau ba zanyi disappointing na ki ba kin ji ko? Kiyi haƙuri, na tuba..! Yadda ya ƙarashe maganar ya tabbatar mani da kunnen sa ya riƙe, don na lura duk lokacin da yake ban haƙuri hannun sa na bisa kunne, kuma hakan ba ƙaramin tafiya ya ke da imani ba.

Na yi shiru ina zabga murmushi, yayin da na sake curewa guri guda, don idan ba faɗa maka aka yi ba da mutun bisa katifar ba zaka taɓa yadda ba.

"Pretty na bata hakura bane.? Ya tambaya cikin wani salo mai ruɗar wa.

Na rufe fuska da tafin hannuna, a shagwaɓe na ce "Waye zai yi fushi da abun ƙaunar sa.?

Ya saki murmushi mai sauti yana faɗin "Babu kam Pretty..!

Mun jima muna fira mai ratsa zuciya sannan ya tambaye ni "Me zan taho maki dashi.?

Na ce "Babu komai..!

"Ban yadda ba, sai kin faɗa Allah, idan ba haka ba in fasa zuwa."

Ina masifar son chocolate, don haka cike da kunyar sa na ce" Chocolate.!

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now