016

218 10 2
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*016*

     **Cikin dakiya Baffa ya amsa sallamar, tare da basu umarnin shigowa ciki, kai tsaye suka kuwa kutso kai har cikin ɗakin sa, suka samu waje suka zazzauna, yayin da suka yi musabaha da juna.

Kallon ɗaya zaka ma ladan sani ka tabbatar da baya cikin hankalin sa, ya rusuna kusa da Baffa kan sa a ƙasa, tashin hankali soma faɗin "Sunana Malam Sani ni ne mahaifin Jafar.!

Baffa ya gyaɗa kai yana faɗin " Maraba, ya iyali.?

Wani takaici haɗe da bakin cikin furucin Baffa ya sanya hawaye masu zafi fitowa daga idon ta, ta juyar da kai haɗe da sakin wani ɗan siririn tsaki. Yayin da Abban Ilham ya miƙe tsam ya bar ɗakin, shi kan shi wani irin tuƙuƙi zuciyar sa ke masa, bare da ya fahimci gaskiyar abunda ke faruwa, da ya gane wancan la'anannen Jafar ɗin ba ɗan ladan bane ba, domin basu baro Unguwar ba sai da suka je gidan iyayen bogin da ya turo, yayi ƙwafa, Sam surukin sa bai cancanci wannan cin amanar ba, bai cancanci wannan rashin mutuncin ba, yayin da ya ɗauki alwashin hukunta Jafar dai dai da laifin da ya aikata, don haka direct daga nan gidan police station ya nufa, suka je aka ƙwashe iyayen bogin da ya turo, sannan aka tasa ƙeyar ɗaya har gidan su Faisal, da zumar duk gidan uwar da yake idan aka kama Faisal ɗin shi zai nemo shi, tunda babu wanda ya san asalin inda Jafar yake zama.

  A gida kam cikin matsanancin tashin hankali Ladan Sani ya ƙara rusunawa saboda darajar Baffa ya ke gani yana faɗin "Alhamdulillahi, Malam wani batu nake ji mai matuƙar mamaki da tashin hankali, wancan bawan Allah da ya fita yazo yana shaida mani, irin ɗibar albarkar da wani yaro ya maka, wanda wai ni na aiko da ƴan uwana nemawa yarona Jafar auren ƴar ka! Wallahil Azim ban san da zancen ba, ban kuma aiko da ƴan uwana ba, kuma sannan wancan saurayin ban san shi ba, ba yarona bane ya turo a neman aure, yanzu haka maganar da mu ke dirowar Jafar kenan daga gurin aikin sa garin zaria, bai san zance ba, kuma na kira sa yana hanyar zuwa nan gurin domin ku shaida da idanun ku, ban san komai ke faruwa ba, sai da wannan bawan Allah ya zo gurina yanzu, sannan na ja shi har gaban ƴan uwana, kuma a gaban sa suka faɗi kuɗi aka basu su zo su nemar wa wani jafar din auren ƴar ka, dan girman Allah ka yi hakuri, Malan ba kai suka wulakanta ba ni suka wulakanta, kuma insha Allah zan sanya a hukunta waccan yaron da ƴan uwana na abunda suka aikata.!

  Baffa ya girgiza kai cike da takaici ya ce "Shi wancan ba ɗan ka bane.?

" Wallahil azim ba ɗana bane, amma zan sanya a kamo shi gaban ka, ka ji da bakin sa, sannan a hukunta shi dai dai da abunda ya aikata.!

Ya gyaɗa kai tare da dakatar da Umma dake shirin magan ya faɗin "Ba buƙatar haka, babu wanda za a hukunta a cikin su, ni na yafe masu duk abunda suka mani, don haka ka je babu komai, aikin gama ya gama.!

Ladan ya ƙara rusuna cike da takaici ya ce "Ka gafarce mu Malam.!

"Allah ya gafarta mana baki ɗaya.! Baffan ya faɗa yana murmushin yaƙe.

Ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da faɗin "Mungode, Mungode Malan.!

"Ba komai.! Baffa ya faɗa cikin ƙosawa da zancen sa, domin har ga Allah duk juriyar sa, ransa yayi masifar ɓaci bare ma da ya ƙara sanin yaudarar da Jafar ya mashi.

  "Dan girman Allah Malan, tunda har abun ya zamana haka, ni ina roƙan ka da darajar fiyayyen halitta, da ka taimaka ka bawa yarona Jafar auren wannan ƴar taka, saboda duk abunda ya faru, ta dalili na ya faru, dan Allah kar ka ce mani a'a, ka dubi girman Allah malan, ni ina nemawa ɗana auren ƴar ka, domin babu wanda bai zai yi ƙwaɗayin haɗa zuri'a da kai ba, ina roƙan da ayi komai yadda aka tsara, na sani ɗana ba zai taɓa ƙin aminta ba, domin abun alfahari ne a ce ya auri ƴar ka.! "

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 11, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now