010

62 6 0
                                    

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*010*

     ***A bakin gate ɗin sardauna estate na same shi tsaye yana jiran ƙarasowa ta, na ɗauke kai daga kallon shi, ganin daga shi sai boxer da vex fara a jikin sa, zai sallami mai napep ɗin na ce ya bar shi kawai aƙwai kuɗi a hannu na, na miƙawa mai mashin ɗin 500, ba tare da ya bani canji ba ya nemi tayar da napep ɗin shi, na juyo ina faɗin "Baka bani canji ba malam.!

Ɗan matashin ya washe mani baki yana faɗin "Na ɗauka an bar mani." Ya fiddo ɗari ɗaya ya miƙo mani.

Na zabga mashi harara ba tare da na karɓa ba ina faɗin "Nawa ne kuɗin naka.?

"Dari huɗu ne Hajiya.!

"Daga ƙwaɗo zuwa nan ne 400, dallah malam bani canjina tunda ba nomar kuɗin nake ba.!

"Amma ai neman su kika zo.! Ya faɗa yana kallon Jafar dake tsaye.

Jafar ya ce "Sweetie dan Allah ki bar masa ki zo mu wuce.!

"Wallahi bazan bar masa ba, naira 150 zai ɗauka a mutunce.! A yadda na fahimta wani kallon banza yake mani, sai dai ban iya fassara ko kallon na menene ba.

Ya ciro 350 ya miƙo mani, na karɓe ina watsa mashi harara lokacin da yake faɗin "An dai cuci hijabi, kuma an ci amanar dattijai.!

Sai a lokacin na samu na fassara kallon da yake mani, ashe kallon ƴar iska yake mani mai yawon ta zubar, idanuna ya ciko da ƙwallah, cikin rauni na ce "Allah ya tayar damu ranar gobe ƙiyama, wallahi bazan taɓa yafe maka wannan ƙazafin fa.!

Na matsa gefe ɗaya ya tayar da napep ɗin shi ya bar gurin. Na sanya gefen hijab na goge hawaye na ina faɗin "Wallahi duk wadda za'a ga ta zo gidan su saurayi, ɗaukar ƴar iska ake mata, abunda na guda kenan Jafar, kuma ka ji da kunnen ka, mai napep ma haka ya ɗauke ni.!

A hankali ya ce "Ba kin ce Allah ya isa ba? Zai isar maki Meenari ta, tunda ai ke ba yawon Iskancin kika zo ba ko? Gurin mijin ki kika zo."

"Ni ba gurin ka nazo ba..!

Ya riƙe kunnuwan sa yana murmushi ƙasa ƙasa "Haka ne! Afuwan ganin Momma ki ka zo."

Na kawar da kai na gefe ina goge sauran ƙwallan da suka maƙale, ya sassauta ta murya ya ce "Babu gaisuwa.?

A daƙile na ce dashi  "Ina wuni.?

Ya leƙo fuska ta yana murmushi, ganin na ƙi yadda mu haɗa ido dashi, a hankali ya ce "Lafiya lau Aminatah.!

"Ya mai jiki.?

"Da sauƙi Alhamdulillahi."

Nayi tsaye ina kallon ƙasa, ya saki murmushi mai sauti tare da shafa ƙirjin sa ya nuna hanya yana faɗin "Mu je ko."

Yayi gaba na bi bayan shi, har bakin wani ɗan madaidaicin gida, ya sanya key ya buɗe ƙofar, na lumshe idona cike da takaicin kuskuren da na aikata.

"Bismillah madam.! Na tsinkaye shi yana faɗa lokacin da ya ƙarasa wangame ƙofar baki ɗaya.

Sai da na gyara zaman niƙabina, sannan na zare takalmi na bakin ƙofar, na shiga bakina ɗauke da sallama, sai dai abin mamaki babu wanda ya amsa, a take na ƙare wa falon kallo yadda kasan ba'a taɓa shiga cikin sa, ko'ina yayi ƙura, gashi babu ko furniture a ciki, sai dai ƙatuwar katifa dake yashe gefe guda, gabana ya faɗi ras! Na juyo na dube shi, ya sakar mani ja'irin murmushin mai kashe mani zuciya, sai dai wannan karan bai yi amfani ba, ya nuna katifar "Zauna mana Sweetie.!

RAMUWAR GAYYA Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα