RAMUWAR GAYYA

By Feedohm

1.5K 91 3

Revenge More

02
03
04
05
06
07
08
09
010
01
11
012
013
014
016

015

85 4 0
By Feedohm

  💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*015*

      Jafar kam tunda ya zauna yake zabga tsaki, ya yi tsaki ya fi sau hamsin, har Faisal ya gama sallamar mutanen dake gurin sa ya juyo yana faɗin "What ups.?

Ya ƙara kan dogon tsaki tare da kawar da kai gefe yana faɗi "Mts, ni da wancan tabaɓɓen mutumin mana.!

"Wa ke nan.?

"Wancan bagidajen malamin zaure mana, shi yasa fa ni duk ban yadda da waɗannan surkullan ba, amma ka matsa mani na je, yanzu dan Allah ina amfani? Nayi wasting 5k ɗina for nothing.!

" Me ya maka.?

"Makaryaci, he told me idan nayi applying wannan ƙwallin muka haɗa ido da ita, duk abunda na tambaye ta, ba ta isa ta ce mani a'a ba! Sai da na yi sati ina rangaɗa shi kamar baƙauyen ƙwarto, without asking her anything, amma yau na tambaye ta ta mani tunkiya.!

Faisal ta ƙwalalo ido waje ya ce "Me kake nufi.?

"Na faɗa maka ta mani tunkiya, ta ɓata mani rai har na kasa controlling kai na, nayi revealing komai da komai gashi yanzu komai ya watse."

"Kar dai ka ce an yi baran baran.? Ya ƙarashe maganar tare da ware hannayen sa.

Cike da takaici Jafar ya ce "Sosai ma kuwa.!

"Ba zata gyaru ba.?

"Ta ina? Ina gaya maka na fayyace mata komai."

Faisal ya ke ce da dariya yana faɗin "Har ka ci sadakin ka kenan? Sau ɗaya fa kawai? Gaskiya na tausaya maka, amma mutumina wannan yarinyar ta ci banza, idan da a ce waje ka je, da waɗannan 24k zaka ci lafiyayyun ƴan mata har biyar."

Jafar ya ƙara harzuƙa ya ce "Uban wa ya ce ta ci banza? Wallahi ba ta ci banza ba, sai na karɓo kuɗina."

Faisal ya kece da dariya yana faɗin "How? Ka ga ba fa zata yiyu ba! Kawai ka zama abun tausayi, ni dai ka yi ƙoƙarin biyana kafin ka tafi, don ban ci nanin ba kuma nanin ba zata ci ni ba."

"To an ce ba za a biya ka ba.?

"Ni dai ina faɗa maka ne, don na san babu ta inda kuɗin zasu fito, tunda ba zaka yi ma ƴar mutane ciki ba sannan ka je ka ce su baka kuɗin ka.!

"Zaka gani, ina ce ba'a aure sai an yi test.?

"Hakane, to menene.?

"Good, I will use that opportunity, a mai do mani kuɗina, she's pregnant, gobe early morning zan tafi asibiti, sannan in kira tsohon ta ya zo da ita asibiti a gwada mu, da an ga cikin zan miƙa hannu a maido mani da kuɗi na, shi kenan.!

"Kai ka tabbatar ma da tana da cikin ne.?

Jafar ya dalla mashi harara yana fadin "5 weeks ma kuwa, ko an faɗa maka ban iya jefa ƙwallo da ƙyau bane.?

"Idan ta ce cikin naka ne fa.?

Ya taɓe baki "Zan tambayi agidan uwar wa na mata? Waye shaidan ta? Ni fa ko? Dama a ce ko sau biyu zuwa uku na latsa da zan iya hakura, amma sau ɗaya kawai fa? Kuma shima sai da ta bini da tsinuwa da la'ana.!

***

Yaya kam kiran Umma tayi da daddare sanar da ita ina gidan ta, kuma anan zan ƙwana, duk da Umma tayi faɗan me yasa na tafi ban faɗi mata ba, daga ƙarshen dai ta ce in ƙwanan, don Yaya ce mata tayi aiki zan mata. Ita kuma yaya ta yi hakan ne da zumar zuwa dare mu yanke shawarar hanyar da zamu ɓullowa lamarin, kuma a cikin daren yaya ta ce zuwa safe zata sayar da zoben ta na zinari sai mu je wani private hospital a zubar da cikin ba tare da su Baffan sun san me ke faruwa ba, idan abun ya lafa sai ta sanar da su.

Sai dai wajen ƙarfe 8am na safe, tana haɗa masu abun karin kumallo aka yi sallama da Abban Ilham, inda ya tarad da saƙon Baffa wai ya tafi da ni yanzu general hospital Jafar da shi kan shi Baffan na jira za'a yi mana gwaje gwajen da ake yi kafin aure.

Cikin matuƙar kaɗuwa Yaya ta kalle sa lokacin da ya kai aya tana faɗin "Babu inda zata je wallahi, babu wani ɗan iskan awo da za'a mata, auren ma gaba ɗaya an fasa.!

"Me yasa Maman Ilham, kin san fa test ɗin dole ne yanzu, kuma ba rashin yadda ke sanya wa ayi shi ba, sai don tabbatar da ingancin lafiyar ma'uratan, Kinga bai kamata akan haka ki faɗi wannan maganar ba, dan Allah ki shiga ki ce tayi sauri ta zo mu je,kar su yi ta jiran mu, Baffa ne da kan sa fa ya turo, wai ya kira wayan mu a kashe.!

"To wai ma uban wa ya ce a yi awo.? A ƙara faɗa a hasale.

Cike da mamakin botsarewar ta ya ce "Shi Jafar ɗin ne ya buƙaci a yi shi yau.!

Ta share gumin da ya keto mata, yayin da ta miƙe ta shigo ɗaki ta iske ni riƙe da Kur'ani ta ce "Ba kin ce ya fasa auren ba.?

Na gyaɗa mats kai alamun eh.

"To kuma don menene zai ce a tashi asibiti a yi maku test a tare Aminatu? Anya gaskiya kika faɗa mani? Ko dai ke ce kika fasa auren sa ba shi ya ce ba..?

Da mamaki na ke kallon ta, Sam ban san ma me zance mata ba, domin na kasa hango abunda ya sanya Jafar ya buƙaci a yi mana test.

Cikin tsawa ta ce "Ki faɗa mana gaskiya, shi ne ya ce ya fasa ko ke ce.?

"Ni fa bangane ba Yaya, wallahi duk abunda na faɗa maki shi ne ya ce da kan sa, ban maki ƙarya ba ko ta kalma ɗaya, sai dai abunda ban gane ba, menene dalilin sa na cewa a yi mana gwajin kafin aure? Bayan duk kalaman da yayi amfani dasu a kai na.?

Idona ya ciko da ƙwallah, na lashe busassun laɓɓana, kalaman sa suka dawo mani inda ya ce " _Sai na wulaƙanta ki Aminatu, sai na tabbatar da ban bar ko ɗigon farin ciki ba a zuciyar ki_ "  A take zuciyata ta bani amsa kai tsaye, saboda ya san ina da ciki! Kuma tabbas na je gwajin za a tabbatar da haka gaban mutane, lallai Jafar shaiɗani ne, wato ba zai bar ni haka ba.!

Na ɗago na kalli Yaya, cikin kuka na ce "Ba zan je ba yaya, ya yi hakan don ya tozarta ni, yayi hakanan don ya shaida ma duniya ina ɗauke da cikin shege.!

Ta zaune gefen gadon haɗe da dafe kanta da hannu yayin da hawaye suka cigaba da kwaranya daga idon ta, kamar wacce aka tsikara ta miƙe ta dauki hijabin ta tana faɗin "Bara in je asibitin da kai na, ki zauna ina dawowa.!"

Na sadda kai ƙasa ina cigaba da rusa kukana, bana jin aƙwai mayaudari munafuki a duniya kamar Jafar.

Ta fita ta samu Abban Ilham suka tafi asibitin tare, inda suka iske Baffan da Jafar zaune bisa ɗan tebur suna jiran ƙarasowar mu, da mamaki Baffan ya ke tambayar ta "Ina Aminatu.?

Ta kalli Jafar da ke danne danne wayar sa hankali ƙwance, sannan ta ce ma Baffa "Tana gida.!

"To me ye amfanin zuwan ki babu ita Salima.?

"Wata ƙyil tana tsoron tonuwar abun kunya.! Jafar ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba.

Ta kasa hakura ta watsa mashi harara tana faɗin "Babu abun kunyar da ya fi wanda ka aikata Jafar, banza la'annanne, kuma wallahil Azim ba za mu taɓa tozarta ba kamar yadda ka so, kuma kai ba? Allah ya fi mu sanin yadda zai yi da mara imani irin ka."

Cike da mamaki Baffa ya ce "Me ya faru Salima.?

Jafar ya soke wayar sa aljihu yana faɗin "Alaramma dakata in faɗa maka da kaina, Ƴar ka dai ciki gare ta, ta daɗe da zama karuwar gida, shi yasa wannan ta gagara taho wa da ita a auna, don haka malam fiddo mani kuɗi na fasa aure, Allah ya toni asirin ku.!

Baffa ya ɗago ya kalle sa da idanun sa da suka sauya zuwa ja, kalmar karuwar gida ta masifar dakar mashi zuciya, ya daure ya saki murmushin takaici ya ce "Idan ba zaka aure ta ba Jafar, mai zai hana ka zo gida ka same ni ka karɓi kuɗin ka? Ai ni mai iya nemo maka aure ne da kai na, amma wannan sharrin na menene.?

  Ya kalle sa sheƙeƙe ya ce "Au kana zaton sharri na mata? To a kawo ta a auna mana sai mu tabbatar."

"Zan je na ɗauko ta, ka kira mahaifin ka a auna ta a gaban sa amma ka sani idan har ƙazafi ka mata bazan taɓa yafe maka ba.

"Ka aika mana tunda kai mahaukaci ne da baka san ƴar ka ta sauya ba? Ko ko ai ba gani zaka yi ba, don da alama duk kanwar ja ce, an fake da gidan malunta ana tafka karuwanci, kai ma wa ya san iya adadin yaran da ka latse a wannan zauren naku.!

Wani wawan mari Abban Ilham ya kifa mashi, ya ɗaga hannu da niyar rama wa amma mutanen suka rirriƙe shi, ya ci ga ba hargowa da zage zage yana faɗin "Mutanen banza marasa daraja, haka kawai za a liƙa mani auren karuwar gida, gashi tsofai tsidau amma wai shi na Allah, ƴar sa kullun cikin zumbulelan hijabi take, ashe lalatattar ce, wallahi sai kun maido mani sadaki na, kawali Allah kaɗai ya san shima ƴaƴan da ya lalata, ni fa Allah ne ya taimake mani, sai da aka wanke Allo aka bani da niyar a shanye ni, to ba'a sani ba uwata ba hakanan ta aje ni ba.!

Mutanen da ke gurin suna ta bashi hakuri, a tunani su shi aka cuta, yayin da suke ma Baffa wani irin kallo na kaskanci, ita kam Yaya banda kuka babu abunda ta ke, mijin ta ya fiddo naira dubu talatin da zai kai banki ya watsa ma Jafar din, sannan ya kama Baffa dake ta kallon Yaya ya gagara ce wa komai suka fito asibitin, ya tsayar da abun hawa ya ɗaura su suka tafi su kaɗai, domin ya tabbata suna da abun tattauna wa a gidan da suke buƙatar sirri, sai dai daga nan gidan su iyayen Jafar ɗin ya nufa don ya sanar masu da halin da ake ciki, ba tare da ya san cewa iyayen bogi bane yayi amfani da su.

Su kam sai da suka shiga ɗaki Umma ta shigo ta zauna tana tambayar lafiya ganin yanayin dukkanin su biyu.

Baffa ya kalli yaya da idanun ta suka kaɗa saboda azabar ɓacin rai ya ce "Faɗa mani me ke faruwa.?

Cikin kuka ta soma faɗa nashi duk abunda da suka faru, tun daga zuwana na farko gidan su Jafar da zumar dubo mahaifiyar su, da kuma fyaden da ya mani, da wannan zuwan da nayi bayan mun gama magana da Umma.

Cikin kuka Umma ta miƙe ta yayi bi hijabi zata fita, Baffa ya katse ta "Ina zaki.?

"Gidan wannan munafukar zan je, sai na kashe ta wallahi, domin babu amfanin zama da ita.!

"Koma ki zauna.!

Tayi tsaye tana kuka, ya daka mata tsawa "Ki koma ki zauna na ce ko.?

Bata da yadda zata yi da ya wuce ta koma ta zauna, don haka ta faɗi tuɓus taba hararar yaya.

Kur'ani ya dauko, ya buɗe ya soma karantawa cikin wata irin siga, So yake ya samu sassaucin da har zai iya yanke hukunci ba tare da yayi nadama ba, da ya ke da ƙarfi yake karatun su kan su abun ya natsar masu da zuciya, kowanne yayi kasaƙe yana sauraran karatu, yayin da suka tallabe kumatu suna hawaye.

Kusan rabin awa ya shafe yana karatu ya samu natsuwa haɗe da rangwamen tukukin da zuciyar sa ke masa dai dai gwargwado.

A hankali ya aje ƙur'anin da ke hannun sa, ya ɗago da idanun sa da suka rine, ya ɗaura bisa fuskar Yaya da ke tsugunne tana kuka ya ce "Da ta sanar maki ke me yasa ba ki zo gida kika sanar mana ba.?

"Na ɗauka abun zai tsaya anan Baffa, ban ɗauka zai ci amanar mu har ta haka ba, a tunani zan iya samo ma ƴar uwata mafita ba tare da mun sanar maku ba."

"Yanzu kun samo mafitar.?

Ta girgiza kai tana kuka.

Ya mayar da kallon sa ga Umma dake zaune gefe guda ta tallabe kumatu da hannu yayin da idanun ta ke tsiyayar hawaye ya ce "Ke kuma da kika ɗauki hijabi me zaki je kiyi mata? Har kike kiran ƴar ki munafuka akan abunda baki da tabbas."

Ta fashe da kuka ba tare da ta ce komai ba.

  Ya rumtse idon sa gam yana faɗin "Ya yaudare ni, na yafe mashi, ya zalunce ni, shi ma ya je na yafe mashi, ya zubar da  ƙimata da mutunci gidan nan a idon mutane, shima na yafe mashi, amma bazan taɓa yafe mashi ƙazafin da yayi ma Aminatu ba, wallahi zan tashi tsaye na roƙi Allah ya wulaƙanta rayuwar sa, ya bi mata haƙƙin ta, zan tabbatar masa da mun iya wanke allo mu shanye, na san wacece Aminatu, na san abunda zata aikata, na kuma son irin tarbiyyar da na bata, ba wai ina nufin bata yi laifi ba, ta yi laifin yadda da kuma zuwa da tayi gidan su, kamar yadda nima nayi laifin aminta dashi...!

Sallamar Abban Ilham ne da ladan Sani ta katse mashi sauran zancen sa.

*RAMUWAR GAYYA Feedohm.*
*RAMIN MUGUNTA Slimzy.*

Mai buƙatar tagwayen littafai biyu. 300 ne kacal gaba ɗaya, mai son guda ɗaya zai biya 200.
Payment.
👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank.
Amina Jibril.
Shaidar biya.
07042277401.

Or

Katin Mtn
08036953516.
Shaidar biya ga ɗaya daga cikin waɗannan lambobin.
08036953516 ko 07042277401

*FEEDOHM.💞*

Continue Reading

You'll Also Like

927K 55.3K 49
๐ˆ๐ง ๐ญ๐ก๐ž ๐“๐š๐ง๐ ๐ฅ๐ž๐ ๐ฐ๐ž๐›๐ฌ ๐จ๐Ÿ ๐‡๐ž๐š๐ซ๐ญ๐ฌ, ๐š๐ง๐ ๐ฉ๐ฎ๐ซ๐ฌ๐ฎ๐ข๐ญ ๐จ๐Ÿ ๐“๐ซ๐ฎ๐ญ๐ก๐ฌ, ๐‹๐จ๐ฏ๐ž ๐ฐ๐ž๐š๐ฏ๐ž๐ฌ ๐ข๐ญ๐ฌ ๐ฆ๐ž๐ฌ๐ฆ๐ž๐ซ๐ข๐ณ๐ข๐ง๐  ๏ฟฝ...
295K 17.2K 18
"แ€˜แ€ฑแ€ธแ€แ€ผแ€ถแ€€แ€œแ€ฌแ€•แ€ผแ€ฑแ€ฌแ€แ€šแ€บ แ€„แ€œแ€ปแ€พแ€„แ€บแ€œแ€พแ€ฏแ€•แ€บแ€žแ€ฝแ€ฌแ€ธแ€œแ€ญแ€ฏแ€ทแ€แ€ฒแ€ท.... แ€™แ€Ÿแ€ฏแ€แ€บแ€›แ€•แ€ซแ€˜แ€ฐแ€ธแ€—แ€ปแ€ฌ...... แ€€แ€ปแ€ฝแ€”แ€บแ€แ€ฑแ€ฌแ€บ แ€”แ€พแ€œแ€ฏแ€ถแ€ธแ€žแ€ฌแ€ธแ€€ แ€žแ€ฐแ€ทแ€”แ€ฌแ€™แ€Šแ€บแ€œแ€ฑแ€ธแ€€แ€ผแ€ฝแ€ฑแ€€แ€ปแ€แ€ฌแ€•แ€ซ.... แ€€แ€ปแ€ฝแ€”แ€บแ€แ€ฑแ€ฌแ€บแ€›แ€„แ€บแ€แ€ฏแ€”แ€บแ€žแ€ถแ€แ€ฝแ€ฑแ€€...
427K 12.8K 37
The Sokolov brothers are everything most girls want. Intimidating, tall, broody, they are everything to lust after. Not that they... particularly car...