RAMUWAR GAYYA

By Feedohm

1.7K 106 3

Revenge More

02
03
04
05
06
07
08
09
01
11
012
013
014
015
016

010

69 7 0
By Feedohm

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*010*

     ***A bakin gate ɗin sardauna estate na same shi tsaye yana jiran ƙarasowa ta, na ɗauke kai daga kallon shi, ganin daga shi sai boxer da vex fara a jikin sa, zai sallami mai napep ɗin na ce ya bar shi kawai aƙwai kuɗi a hannu na, na miƙawa mai mashin ɗin 500, ba tare da ya bani canji ba ya nemi tayar da napep ɗin shi, na juyo ina faɗin "Baka bani canji ba malam.!

Ɗan matashin ya washe mani baki yana faɗin "Na ɗauka an bar mani." Ya fiddo ɗari ɗaya ya miƙo mani.

Na zabga mashi harara ba tare da na karɓa ba ina faɗin "Nawa ne kuɗin naka.?

"Dari huɗu ne Hajiya.!

"Daga ƙwaɗo zuwa nan ne 400, dallah malam bani canjina tunda ba nomar kuɗin nake ba.!

"Amma ai neman su kika zo.! Ya faɗa yana kallon Jafar dake tsaye.

Jafar ya ce "Sweetie dan Allah ki bar masa ki zo mu wuce.!

"Wallahi bazan bar masa ba, naira 150 zai ɗauka a mutunce.! A yadda na fahimta wani kallon banza yake mani, sai dai ban iya fassara ko kallon na menene ba.

Ya ciro 350 ya miƙo mani, na karɓe ina watsa mashi harara lokacin da yake faɗin "An dai cuci hijabi, kuma an ci amanar dattijai.!

Sai a lokacin na samu na fassara kallon da yake mani, ashe kallon ƴar iska yake mani mai yawon ta zubar, idanuna ya ciko da ƙwallah, cikin rauni na ce "Allah ya tayar damu ranar gobe ƙiyama, wallahi bazan taɓa yafe maka wannan ƙazafin fa.!

Na matsa gefe ɗaya ya tayar da napep ɗin shi ya bar gurin. Na sanya gefen hijab na goge hawaye na ina faɗin "Wallahi duk wadda za'a ga ta zo gidan su saurayi, ɗaukar ƴar iska ake mata, abunda na guda kenan Jafar, kuma ka ji da kunnen ka, mai napep ma haka ya ɗauke ni.!

A hankali ya ce "Ba kin ce Allah ya isa ba? Zai isar maki Meenari ta, tunda ai ke ba yawon Iskancin kika zo ba ko? Gurin mijin ki kika zo."

"Ni ba gurin ka nazo ba..!

Ya riƙe kunnuwan sa yana murmushi ƙasa ƙasa "Haka ne! Afuwan ganin Momma ki ka zo."

Na kawar da kai na gefe ina goge sauran ƙwallan da suka maƙale, ya sassauta ta murya ya ce "Babu gaisuwa.?

A daƙile na ce dashi  "Ina wuni.?

Ya leƙo fuska ta yana murmushi, ganin na ƙi yadda mu haɗa ido dashi, a hankali ya ce "Lafiya lau Aminatah.!

"Ya mai jiki.?

"Da sauƙi Alhamdulillahi."

Nayi tsaye ina kallon ƙasa, ya saki murmushi mai sauti tare da shafa ƙirjin sa ya nuna hanya yana faɗin "Mu je ko."

Yayi gaba na bi bayan shi, har bakin wani ɗan madaidaicin gida, ya sanya key ya buɗe ƙofar, na lumshe idona cike da takaicin kuskuren da na aikata.

"Bismillah madam.! Na tsinkaye shi yana faɗa lokacin da ya ƙarasa wangame ƙofar baki ɗaya.

Sai da na gyara zaman niƙabina, sannan na zare takalmi na bakin ƙofar, na shiga bakina ɗauke da sallama, sai dai abin mamaki babu wanda ya amsa, a take na ƙare wa falon kallo yadda kasan ba'a taɓa shiga cikin sa, ko'ina yayi ƙura, gashi babu ko furniture a ciki, sai dai ƙatuwar katifa dake yashe gefe guda, gabana ya faɗi ras! Na juyo na dube shi, ya sakar mani ja'irin murmushin mai kashe mani zuciya, sai dai wannan karan bai yi amfani ba, ya nuna katifar "Zauna mana Sweetie.!

Na girgiza mashi kai, haɗe da lumshe idona, domin har ga Allah hankali na bai ƙwanta da gidan ba, bare ma yadda naji shiru babu ko alamun motsin mutun a cikin sa.

A sanyaye na tambaye shi "Ina maman take?

Ya lanƙwashe murya yana aika mani da wani fitinannen kallon soyayya "Sauri kike Sweetie nah.?

Kai tsaye na ce "Eh.!

"Kar na cinye ki.? Ya kuma faɗa yana kusanto ni.

Na ɗaure fuska haɗe da ƙara ja da baya ina faɗin "Kaga! dan Allah ka kaini inda nake na gaishe ta na wuce, tun kafin a neme ni gida.

Ta tausashe ya ce "Wa zai neme ki Sweetie? Ba kin faɗa ba kina gidan yayar mu? Bara na kawo maki ruwa ki sha tukun."

" Ba buƙata.! Na faɗa cikin ɗaga murya.

"Allah ya huci zuciyar Sweetie nah, wallahi yanzu driver ya tafi da ita asibiti ta ga doctor, ki zauna kafin su dawo, na san yanzu haka suna hanya.!

Na watsa mashi wata irin bahagguwar harara ina faɗin "Amma kasan bata nan me yasa ka takura sai nazo yanzu? To idan ta dawo ka gaishe ta.!

Na juya na kama handle ɗin kofar da niyyar buɗe wa, sai dai gam yake an rufe da makuli.

Ba tare da na juyo ba, na ce "Zan tafi." A daƙile.

Yayi shiru ya ƙi cewa komai, na fi minti uku ina jiran ya zo ya buɗe mani ƙofar, amma ban ji ko motsin sa ba, don haka na juyo a fusace ina faɗin "Malan dallah ka buɗe mani kofar zan fita b..

Sai dai turus nayi ganin shi tsaye a gabana, na zaro ido a firgice yayin da jikina ya ɗauki karkarwa, idan har ba gizo idona ke mani ba, to tabbas Jafar ne tsaye zindir haihuwar uwar shi yana murmushi, yayin da hannun sa ɗaya ke shafa mazantakar sa, jikina ya soma ɓari, na kulle idona gam, cikin karkarwa na soma faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, menene haka Jafar? Baka da hankali.?

"Ƙauna ce Meenari, ƙaunar ki ce ke neman hauka ta ni.! Ya faɗa yana jefa mani murmushi.

"Ƙaunar bura uba ka.? Na faɗa baki na na karkarwa, ni ban ma san na iya ashariya ba idan ba lokacin ba.

"Look in to my eyes, can't you see the love? Wallahi ina ƙaunar ki Amina, son..

Na katse shi a fusace ina faɗin "Babu uban da nake gani sai zallar yaudara da jahilci Jafar..!

Ya fara matso wa kusa dani yana faɗin "Haba Sweetie, taimaka  mani za kiyi ,wallahi likita ya ce idan ban kusanci wata ƴar mace ba zan iya rasa rayuwa ta."

  A tsawance na ce "Da kai da likitan kun ci kan abun uban ku, wallahi sai dai ka mutu Jafar, amma bazan taɓa baka mutunci na ba."

"Komai zaki ce ki ce Honey , ki zage ni son ranki amma wallahi son da nake maki ya sanya na kasa ɗauke idona a kanki, har ciwon sha'awar ki ya kama ni, ƙwana na uku asibiti, dan Allah ki taimaka mani, yau kaɗai, yau kaɗai na roƙa, na maki alƙawarin babu wanda zai ji har abada, dan Allah ki taimaka mani, wallahi na kamu da matsananciyar sha'awarki, ba zan ita hakura ba har a ɗaura mana aure, shi yasa na roƙi wata ɗaya, amma baffa ya ce dole sai wata uku, dan Allah Aminatu, nine zan aure ki, asirin ki ba zai taɓa tonuwa ba.!

Da ƙarfi na kama ƙofar ina bugawa haɗe da ihu, a tunanina ko zan samu wanda zai jini ya kamo mani ɗauki, ya sanya hannun sa ya finciko ni jikin sa, na kai mashi mari a fuska ina faɗin "Sake ni, banza ɗan akuya, dama wannan ne dalilin da ya sanya ka janyo ni gidan ku? Munafuki ashe ƙarya kake babh wata uwar ka da bata lafiya, to Allah ya ɗaura mata.! Na ƙarashe maganar ina kai mashi duka ta ko'ina tare da kiciniyar ƙwatar kaina, amma sam karfin mu ba ɗaya ba.

Idon sa a rufe yake faɗin "Karki manta nine zan aure ki, minti biyar nayi na gama, pls ki bani haɗin kai inyi yadda da ni da ke zamu ji daɗin abun."

Cikin kuka na ce "Auren uban ka! Ni ka sake ni, ka sake ni Jafar, ɗan iska asararre, wallahi na fasa auren naka."

Kokowa muka fara har yayi nasarar raba ni da hijabina, ya yage maki zip ɗin siket ɗina, ya jefa ni saman wannan katifar da ƙarfin tsiya, sannan ya bini ya danne..

Tsinuwa, yakushi, cizo, zagi, duka babu wanda bai sha ba, amma ko a jikin sa, bai kuma sarara mani ba har sai da ya cimma muradin sa, ya rabani da mutuncina, sannan ya gangare gefe guda, ya cigaba da aiko mani da kalaman yaudara, kalaman lallashi haɗe ba bani bakin, wai shine mijina don haka kar na ji komai, babu abunda zai taɓa soyayyar mu, in ma godewa Allah da ya ɗanɗani ya ji garɗin zuma ta, hakan daraja da ƙima ya ƙara mani, ta yadda ba zai iya rabuwa da ni ba.

Raɗaɗin da nake ji a ƙasa na, bai hanani miƙe wa tsaye ba, na ƙarasa cire pant ɗin jikina, na ɗauki siket na miyar, na kalle shi da busassun idanuna da babu ko ɗigon hawaye a cikin su, domin sun riga sun bushe, a dasashe na ce "Yadda ka rabani da mutuncina, ina rokan Allah ya raba ka da farin ciki a rayuwar ka, ya raba ka da ƙwanciyar hankali duniya da lahira, ya raba ka da Alkhairin dake cikin duniya da lahira, Allah ya watse maka albarka Jafar.!

Ya sakar mani murmushi yana kallon ƙirjina da na hana shi ko sau ɗaya ya taɓa, don da ya kai hannun shi dana danƙara mashi cizo, ya lumshe ido yana faɗin "Ni Sweetie? Zaki so ki auri watsatstse? Haba Aminatu, uban ƴaƴanki ne fa kike jefa ma wannan alkaba'in, please ki sassauta, son da nake maki ne ya janyo na aikata haka..!

Ban ƙara tanka shi ba, na matsa bakin ƙofa da ƙyar na tsaya ina dafe gabana da ke masifar raɗaɗi, yayin da zuciya ta ke soya haɗe da tafarfasa, duk wani so da ƙauna da nake masa lokaci guda na neme sa na rasa, yayin da ya maye gurbi da tsantsar tsana haɗe ƙiyayyar sa, ta yadda ko sautin muryar sa na tsana na kuma ji bare ganin sa.

"Please kiyi wanka tukun ki tafi, sai in taimaka maki ki gasa jikin ki mata ta, kinga first night ɗin mu kin huta ma." Na tsinkaye shi yana faɗa daga inda yake zaune.

Ban ko motsa daga inda nake ba, bare ya sa ran jin amsa ta.

Na fi minti talatin bakin ƙofar sannan ya taso ya buɗe mani yana faɗin "Dan Allah kiyi hakuri Aminatu, son da nake maki ne ya janyo haka..!

Jin kalmar son nake kamar yana narka mani guduma a zuciya ta, na fice ba tare da ya saurare shi ba, sai a lokacin na samu wasu hawaye masu ɗan karan zafi suka silalo saman kuncina, na fice daga estate ɗin yayin da ya biyo bayana yana bani hakuri, amma ko sau ɗaya ban kula shi ba, haka na tare machine na haye abuna..

Kai tsaye gidan Yaya na nufa, domin yadda nake tafiya da ƙyar ban isa in nufi gidan mu ba, ba tare da Ummi ta nemi sanin dalilin sauyawar tafiyar tawa ba, sai dai yadda Yaya ta kafe ni da ido bayan na shiga falon, ya sanya hankali ya ƙara tashi, yayin da nayi tsaye bakin ƙofar falon ta haɗe da sadda kai ƙasa.

Ta miƙe tsam ta finciki hannuna muka shige ɗaki tana ma su Ilhami kashedin duk uban da ya biyo ta sai ta yanka mashi wuya.

Tambayar farko da ta fara mani "Uban me ya kai ki gidan su Amina.?

Yaushe ne ta san na je gidan nasu? Waya faɗa mata? Kar dai ace bayana ta bi! A take hawaye suka soma gangarowa saman kunci na, na kafe ta da ido ba tare da ma amsa mata ba.

Wani sakaran mari ta kifa mani, ta kama kafaɗata ta daɓar dani bisa gado tare da yaye hijabin dake jikina, ta ware mani ƙafafuna da ƙarfin tsiya, ta haske al'aura ta da fitilar wayar ta....

*RAMUWAR GAYYA Feedohm.*
*RAMIN MUGUNTA Slimzy.*

Mai buƙatar tagwayen littafai biyu. 300 ne kacal gaba ɗaya, mai son guda ɗaya zai biya 200.
Payment.
👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank.
Amina Jibril.
Shaidar biya.
07042277401.

Or

Katin Mtn
08036953516.
Shaidar biya ga ɗaya daga cikin waɗannan lambobin.
08036953516 ko 07042277401

*FEEDOHM.💞*

Continue Reading

You'll Also Like

226K 17.2K 24
"ما هِي رَغباتُك المُظلمة ..دكتور جيُون؟" "لَدي غَرائز تايهيُونغ ..لا رَغبات، وَ هُناك فَرق" آدت أفكار تايهيُونغ وَ فضوله حَول رَغبات الأنسان المُظلم...
989K 30.6K 61
Dans un monde où le chaos et la violence étaient maitre, ne laissant place à ne serrait ce qu'un soupçon d'humanité. Plume était l'exception. Elle...
3.4M 37.9K 30
Diana is an 18 year old girl about to start her senior year until she bumps into a woman at the bookstore who has quite the personality. The woman ta...
224K 2.5K 20
I have found an ideal life. I have a loving husband, no work and no danger. This is exactly what I wanted when I ran away and changed my identity. Bu...