RAMUWAR GAYYA

By Feedohm

1.7K 106 3

Revenge More

02
03
04
05
06
07
09
010
01
11
012
013
014
015
016

08

54 5 0
By Feedohm

💧💧 *RAMUWAR GAYYA.!*

©️ *HASKE WRITER'S ASSO.*
Home of expert & perfect writers

*FEEDOHM. 💞*
Wattpad@Feedohm.

*08*

      ***Na sake gyara ƙwanciya tare da cusa kaina ƙasan pillow ina murmushi, yayin da ƙaunar sa ke ratsa kowanne lungu da saƙo na jikina, mun jima muna ɗumama juna da kalaman soyayya, masu rikitar da zuciyar masoya, sannan ya roƙe ni alfarma in kai ma Ummi wayar su gaisa, don basu taɓa magana ba, na miƙe tsam na fita tsakar gida, cikin sa'a na iske ta, ita kaɗai tana cin tuwo, na kanga mata wayar a kunne.

Ta ɗago ta kalle ni tana tambayar "Wanene.?

Shirun da nayi ina murmushi tare da wulla hannuwa na baya, ya bayyana mata kowanene, don haka ta sakar mani harara, lokacin da yake gaida ita, ta amsa kamar wanda ta riga ta saba da shi , har da su tambayar shi ya maman shi, duk da ba wani daɗewa suka yi suna magana ba, amma yadda kasan waɗanda suka shekara da sanin juna haka suke magana, ni kam ina gefe sai murmushi nake, sannan ta miƙo mani wayar bayan sun yi sallama, na koma ɗaki na shige cikin bargo.

Tun daga ranar muka koma fiye da baya, domin yanzu ya fi nuna mani kulawa da ƙauna, sannan ya ɗauke idon sa kacokam a kai na, ko yawan kallon surata ma ya daina, iyaka ta da shi muyi fira yana kallo fuska ta, ga wani wa'azin da ya koma yi mani duk lokacin da zai zo gurina, sannan ya mani alƙwarin da mu yi aure shine malamina, babu wata islamiyyar da zanje..

Baffa da kan shi ya taka har unguwar da aka ce suke, cikin dubara da hikima yayi bincike akan Jafar ɗan gidan ladan sani, kuma ya samu shaidar kirki daga mutanen unguwar, don wancan Jafar ɗin mutumin kirki ne, ya dawo gida sai yabon sa yake, kuma a ɗan datsin Jafar ya takura akan lallai sai ya aiko da sadakina a gidan mu, idan ya so sai a sanya rana bayan an kawo, Baffa ya aminta, tare da yanka masu naira dubu sha biyar a matsayin sadaki, sannan ya sanya wata huɗu ayi biki, shima dan ya cije ba zai rage ba, don kuwa a yadda Jafar ya buƙata wai a sanya wata ɗaya , zai mani komai da komai na hidima, kayan ɗaki , da kayan kitchen da duk ma wani abun amfani.
  Baffa ya sanar da shi, ai ba shine ke da alhakin wannan hidimar ba, zai yi komai a matsayin sa na mahaifina, idan lokacin ya masa tsawo sai dai ya haƙura ya nemi wata, don abun bana sauri bane, kuma ma yana buƙatar ƙara bincike sosai, sannan hatta lefe Baffa ya ce bama buƙata, ya bari duk abunda yayi niyyar bani idan an kaini gidan sa ya ɗauka ya ba ni. 

  Haka ya haƙura aka sanya wata huɗun, sai dai tun daga ranar ya fara janye jiki daga gare ni, ya dai na zuwa fira guri na, ya kuma dai na kirana a waya sosai..

  Idan na tambaye shi dalili sai ya ce "Idan ina tare dake Aminatu, na kan ji tamkar ina tare da matata, ina jin shauƙi mara iyaka, kuma ni bana so wani abu ya sake faruwa, shiyasa nake nesa nesa dake, amma babu abunda ya rage daga ƙaunar ki."

Har a raina nake karɓar uzurin sa, tare da ƙara ƙaunar sa har cikin zuciya ta.

Yau kam banyi zato ba, sai ga yaro an aiko wai ana kiran Amina.

Na kalli Ummi dake yanke farce tsakar gida lokacin da ta ke tambayar "Wa ke kiran ta.?

Yaron ya ce "Jafar aka ce."

Na zabura na miƙe zumbur na nufi ɗaki, na zuro hijab dogo har ƙasa na fito har ina tuntube.

Ummi ta dalla mani harara tana faɗin "Aji kam anan ya samu targaɗe.!

"Kai Ummi.!" Na faɗa ina ƙoƙarin zagaye tabarmar da ke zaune, in fice.

Ta dalla mani harara "A haka zaki fita?

  Na zunɓuri baki ina faɗin  "Me nayi.?

Ta zubawa kafafuna ido, na ƙara zumɓurar baki ganin kafafun nawa duk jirwayen omo, a cikin maƙoshi na ce "Ai ba jikina ya ke so ba, kuma ya ce baya so ina ƙwallah idan zan fita wurin sa, kuma ya ce a haka ma na fi ƙyau."

Ta kalle ni sheƙeƙe tana faɗin "Haba.?

Na gyaɗa mata kai.

Ta galla mani harara "Dallah koma ki cire hijabin ki dauraye ƙafar ki sannan ki fita.!

Kamar in yi kuka na ce" Jirana fa yake Ummi. "

" Idan ta gaji ya tafi." Ta faɗa kai tsaye.

Raina a ɓace na ɗauki buta na antaya ma ƙafafun, sannan na yi waje ba tare da na kuma kallon ta ba, sai dai ina ɗaura ido a kan ƙyaƙƙyawar fuskar sa, na ji ɓacin ran gaba ɗaya ya gushe, na sakar mashi tattausan murmushi ina faɗin "Ni ba ruwana da kai..!

Ya zaro ido "Me nayi Sweetheart.?

"Ka daina kirana mana..!

Ya tausasa murya yana faɗin "Haba Sweetie, phone call is nothing, our heart to heart connection is always intact."

Na lumshe idanu ina kallon sa.

Ya lanne mani ido "Ko ba haka bane.?

"Haka ne.! Na faɗa ina jefa mashi murmushi.

"Good Sweetie, yanzu dai zuwa nayi in faɗa maki, my momma is coming to see you tomorrow, yanzu haka jirgin su ya sauka Abuja har sun kamo hanyar kt, ta ce dole sai ta zo ta ga ƴar jinjirar da ta sace zuciyar her one and only child, gaskiya ko Amina? Wallahi kin yi sa'ar suruka, wallahi tana son ki tun kafin ta ganki, tana son ki fiye da ni."

Na rufe fuskata da tafin hannuna, a hankali na ce "Nagode.!

  "Yauwa, zo ki ga tsarin gidan ki, idan aƙwai abunda kike so a ƙara sai a ƙara, sai kuma ki faɗi wane irin paint kike so, idan sun zo zaria sai ta tsaya ta saya." Ya ƙarashe maganar tare da fiddo wayar shi daga aljihu, ya matso kusa da ni sosai, ya shiga nuna mani wani danƙareren gida da aka ɗauka part by part, har da su swimming pool da garden da aka ƙawata da furanni a ciki.

Ni dai ba wani gani nake sosai ba, saboda yadda nake jin saukar numfashi sa, a bisa wuyana, yayin da kafaɗar sa ke gogar tawa.

"Ya kika ga bedroom ɗina? Furniture ɗin sun maki ko a sauya wasu? Momma ta turo su daga Dubai shekaran jiya, irin su naso a sanya maki a na ki bedroom ɗin sai Baffa ya ce ba'a buƙata, wai shine ke da alhakin hakan.! Na tsinkaye shi yana faɗa cikin kunnena, cikin wata irin rikitattar murya.

A hankali na janye jikina daga nashi ina faɗin "Yayi ƙyau.!

"Paint fa? Wane color kike so.?

"Ko wanne..!

Ya buɗe baki da niyyar bani amsa wayar sa ta dauki ruri, yayin da sunan "Mom." Ya bayyana saman screen ɗin

Ya kanga a kunne yana faɗin "Mom kuna ina yanzu.?

Ban san me aka ce mashi ba, don ba'a speaker ya sanya ta ba, sai dai gani nayi yanayin sa ya canza, a hankali ya shiga maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, shikenan gani nan zuwa.!

Na ƙura mashi ido ina tambayar "Me ya faru.?

Ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido yana faɗin "Accident suka yi Amina.!

Idona ya kawo ruwa ƙwal ƙwal, na kalle shi murya ta na rawa na ce "Wani abu ya same ta.?

"Ta samu fracture ne a hannu da ƙafa, da babban rauni a kai."

Wata irin raunannar zuciya gare ni, sai ji nayi hawaye na gangarowa saman kuncina, sai nake jin kamar ni ke da alhakin accident ɗin nata, don saboda ni ta zo ƙasar.

Ya sauke ajiyar zuciya yana kallona, a sanyaye ya ce "Zan wuce..!

Na gyaɗa mashi kai "Ka faɗa mani ƙwatancen asibitin da za'a kaita, sai in gaya ma Ummi ta zo ta ganta.!

Ya juyo yana kallo na, a hankali ya ce "Ki gaya ma Ummi? For what? Hankalin ta ya tashi? Kar ki faɗa dan Allah, in dai ke zaki zo ki ganta wannan ba matsala, kuma bana tunanin ma zata zauna asibiti, a gida zata zauna.!

"To ai sai mu zo tare..!

"No, gaskiya kar ki fadawa kowa, Ke dai ya kamata ki zo ki ganta, don kar hankali su ya tashi."

"Ba za'a bar ni ba, sai dai ko da yaya..!

Ban san meye na fusata ba, amma sai gani nayi ya fusata yana faɗin "Dole sai kin zo da wani? Na ce bana so ko? Mom dai mahaifiya ta ce, idan har ke, ba zaki zo ke ɗaya ba ki ganta, to ki bar shi bana so, dole sai kin mani gayya? For God sake ke wace iri ce Amina? Me yasa baki da sirri a rayuwar ki? A haka zamuyi auren a tanbaɗe.?

Hawaye suka gangaro saman kuncina, a raunane na ce "Ina dashi mana Jafar? Na bar gaya ma Ummi komai wallahi, na bar gaya mata tsakanin mu, wannan rashin lafiya ce, ba sirri ba, me yasa baka so mu zo tare.?

"Bana so! Idan kuma har kin ɗauke ta uwa, ki zo ke kaɗai Aminatu, bana son gayya...!

" Ba za'a bar ni ba J...

Fuuu.. Ya fice daga zauren.

Kuyi hakuri da wannan.

*RAMUWAR GAYYA Feedohm.*
*RAMIN MUGUNTA Slimzy.*

Mai buƙatar tagwayen littafai biyu. 300 ne kacal gaba ɗaya, mai son guda ɗaya zai biya 200.
Payment.
👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank.
Amina Jibril.
Shaidar biya.
07042277401.

Or

Katin Mtn
08036953516.
Shaidar biya ga ɗaya daga cikin waɗannan lambobin.
08036953516 ko 07042277401

*FEEDOHM.💞*

Continue Reading

You'll Also Like

272K 18.7K 56
ABHIMANYU RATHORE :- Rude , workaholic CEO of Rathore Empire .Devilesing hot , every girls drools over him .But loves his family to dearest . . SAKS...
556K 18.9K 144
Read and find out...
732K 105K 39
Yaduvanshi Series #3 it is a book under yaduvanshi series. But it could be read as standalone too. Nitya Raghavendra is a telugu businesswoman earnin...
226K 10.3K 40
#yuyachi ဖန်းတီးမှုတစ်ခုသာဖြစ်၍အပြင်လောကနှင့်သက်ဆိုင်မှုမရှိကြောင်း...❗ start:July 9,2024(Tue) End:september 21,2024(sat) 7:22PM Total- 75 Days #warn...