ZYNAH

بواسطة Ishamoha

77.7K 4.7K 61

Here is a story of a teenage hausa girl Zynah who happens to come from a wealthy nd peaceful family but was h... المزيد

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63

Chapter 20

1.1K 65 0
بواسطة Ishamoha

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITERS ASSOCIATION*

QUOTE:-" Are you bored with life? Then throw yourself into some work you believe in with all your heart, live for it, die for it, and   you will find  happiness that you had thought could  never be yours".

     _I dedicate dis page to *My luvly Momma* luv u so very much sweet mom.❤😍_

               2⃣0⃣

     Yau ya kama Saturday, ranan da *ZYNAH* take jira ta samu ta tafi inda zatayi chasing dream dinta na zama professional medical doctor. Tunda ta tashi bata koma barci ba seda ta kara kimtsa kayanta ta tabbatar bata bar komai ba sannan tashiga wanka, tana fitowa ta tsane jikinta ta shafa mai tasa kaya, jallabiya tasa peach colour da white veil sannan ta fito lokacin karfe tara tayi, tashiga dakin Momsie da sallamanta, Momsie ta amsa suka gaisa, Momsie tace" Yau an tashi da wuri" ,"banson na makara ne shiyasa" ,"ok,Kingama hada kayanki, bakiyi mantuwa ba" ,"banyi ba" ,"toh shikenan, kira Daddynku da Islam breakfast is ready tun dazo" ok tace ta fita, dakin Daddy tafara shiga ta ganshi zaune kan resting chair yana karanta news paper ta gaishe shi tareda gayamai sakon Momsie yace gashinan fitowa sannan ta tashi ta fita ta shiga dakin Islam amma bata ciki ta duddubata amma bata ganta ba, ta fito ta tarar da Momsie wurin dinning tana shirya wurin tace mata bataga Islam ba, Momsie tace "bangane bakiga Islam ba ina zata da sassafen nan" Jummalo dake tsaye wurin tace "ai ta wuce Islamiyya". Tare suka hada baki wurin fadin Islamiyya? Momsie tace "lalle yarinyar nan zan koya mata hankali, wato yanda zata tsaya suyi sallama da er uwar ta take ganin asaranshi amma ba damuwa, zata dawo ta sameni" ita kuwa *ZYNAH* shiru tayi tarasa tacewa haka kwana biyu nan bata gane kan Islam kome matsalanta oho. Da wannan Tunanin ta zaune Daddy ya fito ba dadewa sega Uncle shima ya fito duk sukayi breakfast Daddy yace "ya banga Islam ba,ko bata tashi bane?" Momsie tace "ta tashi,taje Islamiyya ne wai ance suzo yau da wuri saboda wani gasan makarantu na musabaka da zasuyi" *ZYNAH* kallon Momsie tayi yanda ta shirga lbr ta gayawa Daddy.

     Suna gama breakfast suka koma parlour suka zauna Daddy yafara da "Bismillahi Rahmanir Rahim, yau Allah ya kawo mu ranar da mudukanmu nan muke jira, ranan da zamu turaki makaranta badan komai ba sedan kije ki karanto abunda ze amfane ki ya amfani Al'umma gabadaya, Mamana" ya kirata ta juyo ta kalle tareda cewa "na'am Daddy" yace "ni na haifeki, nine mahaifinki, saboda haka nasanki sosai, nasan abunda zaki iya yi da wanda bazaki iya ba, amma wannan baze hanani yimiki guntun nasiha ba, inason kisani duniyar nan ba matabbata bace, mu dukanmu nan bakine acikinta saboda haka watara duk zamu koma inda muka fito, dan haka nakeso komai zekiyi ki dinga sa Allah a lamarin ki In Sha Allahu zakiga daidai a rayuwarki, duk wanda ya rike Allah ya rike Annabi baze taba tabewa ba, ni banda abunda zan baki a duniyar nan illa ingaya miki Allah Annabi suna kadai kike dasu, kinga yanzu zaki inda ba uwa ba uba, se ke kadai se kuma Allahn ki da manzonki, da fantan bazaki bada min kura a ido ki bani kunya ba" yanzu kam ta fara kuka dan ko ba komai zatayi miss din iyayenta tace "Daddy In Sha Allahu bazan bada maka kura a ido ba koma abunda ya kaini shi zanje nayi" yayi murmushi yace "Dats my gurl, nw stop crying, come sit beside me" ta share hawayenta ta tashi ta koma kusa dashi ta zauna ya lallashe ta yace "ki daina kuka, nasan abunda kikema kuka, na miki alkawarin zamu dinga zuwa lokaci lokaci muna dubaki kinji" ta kada kai sannan Daddy ya kalli Momsie yace "da magana" ta girgiza kai tace "ai ka fada komai, koma ko ba komai na yarda da tarbiyan da naba ýata" yace "hakane, Yusuf fa" yace "ni banda abunda zance ka fada duka koma ita *ZYNAH* she's determined so nasan zatayi abunda ya kaita" da haka suka ta mata nasiha basu suka tashi wurinba se to twelve, duk suka shiga su shirya, Momsie taja hannun *ZYNAH* ta kaita daki ta zaunar da ita gefen gado itama ta zauna tana kallon ta tasa hannunta ta goge mata dan guntun hawayen dake idonta tace " *ZYNAH*" ,"na'am Momsie" Momsie ta kalle tace " *ZYNAH* kinga ke macece kuskure daya mace zatayi kiga tana regretting har karshen rayuwanta ba kaman namiji ba da kome yayi ado ne awurin shi saboda haka nakeson ki kare mutuncin kanki, komai yanada lokacin shi kinji, banda biyewa kawaye kinji" ta kada kai saboda ba zata iya bude baki tayi magana ba dan kukan da yaci karfinta. Itama Momsie karfin hali kawai takeyi tace "ki daina kukan, ya isa haka, ko kinaso nima kisani kukan ne" tayi sauri ta girgiza kai , Momsie tace "toh yi shiru" ta janyo ta jikinta ta rungumeta, sun dade a haka harseda Momsie ta tabbatar kukan ta ya saya sannan ta dagota taga har ta fara gyangyadi(jikin uwa dadine dashi😍) murmushi Momsie ta mata sannan ta bude side drawer ta dauko littatafai guda biyu _ASMA'UL LAHIL USNAH DA HUSNUL MUSLIM_ ta bata tace "ki rikesu sosai kinji" tace "nagode Momsie, in Islam ta dawo kice mata nace in laifi na mata ta yafe min amma zan kirata inna kai" ,"zan fada mata, tashi kije ki fito da kayanki lokaci na wucewa" tace toh tareda tashi tayi waje.

     Karfe 12:30 ta musu a airport, koda sukaje Humaira na wurin *ZYNAH* tayi sauri ta karasa wurinta tace "bestee kin cika  alkawari" tafada tana rungumeta, Humaira kuwa shiru tayi tana kallon idon *ZYNAH*  sannan tace "swthrt kuka kikayi?" ,"bestee dole ne nayi kuka rabuwa da family ba dadi, bazaki gane yanda nake feeling ba sabo ke kina kusa da naki familyn" ,"hakane amma kukan yayi yawa kinga idonki kuwa" ,"bestee me idon yayi" ,"tsaya kiga ta dauko purse dinta akwai mirror a jiki tace mata "look" ,"ita da kanta tasan idonta yayi ja" tace "don't worry i will put on a specs so pple won't notice" ,"dats a gud idea". Haka suka ta hira har aka fara kiransu *ZYNAH* da en uwanta kaman bazasu rabu ba amma dole ta hakura ta wuce suna dagawa juna hannu har ta bace musu. Ba'a dadeba jirginsu ya tashi su Momsie suka koma gida, Humaira ma tawuce gidansu, basu dade da komawaba Islam ta dawo Momsie tace "in kin cire uniform kizo ki sameni a daki" ita da kanta tasan tayi laifi saboda haka da tazo dakin kaman zata shiga kaman bazata shigaba daga baya ta sadaukar tayi sallama tashiga, Momsie ta amsa tareda cewa "meyasa baki tsaya kunyi sallama da er uwar ki ba" ,"Momsie ance muzo Islamiyya da wurine shiyasa" ,"Islam wlh ki kiyaye ni a gidan  nan kwana biyun nan duk ina lura dake, wannan dabi'un bazan da kika dorawa kanki ki saukishi tun wuri, tun muna mu biyu tam, fita ki bani wuri". Ta fita tana kumbure kumbure (hmm su Islam manya).

     Karfe biyu da en mintuna jirginsu ya sauka a Kaduna, wannan karon bata sha wahala ba saboda ta taba zuwa,taxi ta samu ya kaita tasha daga nan tashiga mota. Sun kai Zaria aka sauketa tasamu taxi ya kaita har cikin school din. Tana sauka ta kira Ashanty tafada mata tana cikin school din Ashanty tazo suka samo almajirai su kwashe musu kayanta suna shiga dakin taga Ashanty ta gyara mata gado dakinma an gyara, taji dadi, ganin da alamun Ashanty din nada tsafta. Ashanty tace "kingaji ko, bari na miki heating ruwan zafi kiyi wanka dashi" ,"a'a bar ruwan zafin tukun sallah zanyi" ,"ok, muje kiyi alwallah" ta tashi tabi bayanta sukaje tayi alwallah tazo tayi sallahn azahar da la'asar tayi addu'oin ta sannan ta tashi ta dau waya ta kira gida ta fada musu ta sauka sukayi waya da kowa sannan ta kashe wayan ta zauna kan gadonta tayi shiru tana tunani, shigowar Ashanty ce ta katse mata tunanin da takeyi, Ashanty ta ajiye mata abincin da tasiyo mata, jollof rice ne da chicken se drink da ruwa, tayi godiya dama yunwa takeji ta dauka taci tayi hamdala sannan tace zatayi wanka sukaje tayi wanka tasa wani simple gown me shara shara saboda zafi sannan ta kwanta ba dadewa barci ya dauke ta.
*WASHEGARI*
      Kiran sallahn asuba ne ya tasheta ta tashi taje tayi alwallah sannan ta tashi Ashanty itama taje tayi alwallah sukayi sallah tayi addu'ointa ta shafa sannan ta koma ta kwanta, ba ita ta tashi ba se to 11, koda ta tashi bataga Ashanty ba, ta tashi taje tayi wanka tasa kayanta top ne da arabian skirt ta dau cornflakes tasha sannan ta dau wayanta ta kira su Momsie suka gaisa, sun dade suna waya sannan daga bisani ta kashe wayan taci gaba da danne danne, tana cikin haka wasu suka shigo su biyu, daga ninsu kasan students ne suma, daya daga cikinsu tace "sannunki da hutawa" *ZYNAH* ta amsa da "yauwa sannunku da zuwa" dayan tace "kema student ne" ,"eh" ,"dakin nan kike" ,"eh nan nake" daya dogowan tace "dat sounds gud, by d way lets introduce ourselves, am Halima bt ppl call me leema nd she is my frnd nd course mate her name is Nafeesat, we ar both studying microbiology, muna 300level yanzu, kefa? "ni sunana Hasiya Muhammad Sani amma *ZYNAH*  ake kirana, am a new student who's going to study medicine" wacce akace Nafeesat sunanta tace "medicine, woow am impressed" Leema kuma tace "yeah, by d way wats d meaning of *ZYNAH*" ," it means sumtin *BEAUTIFUL* haka sukata janta da hira suna bata lbr tanata dariya har Ashanty ta shigo itama ta zauna anayi da ita.

**********
     Shirye shirye *ASHRAF* yakeyi saboda gobe ze koma school dama shi zaman gidan ya ishe shi kuma sannan yana jin wani spirit na jikin shi na Allah Allah yaje school saboda haka da confidence dinshi yakeson yashiga school gobe. Yagama abunda zeyi yayi dan guntun revision dinshi ya duba scheme dinsu na semester din, he is all set for school. Cike da murna yashiga parlourn mahaifiyar shi, ya ganta zaune da medicated glasses dinta tana karatu yace "Ummi inawuni" ,"lfy lau, ya naga kaman dadi yama waya, se blushing kakeyi lfy" ,"lfy lau Ummi, kawai dai dadi nakeji zamu koma school gobe"  ,"dadina da kai son karatu, bakaman er uwar ka Minal ba" ,"Ummi ai kowa da ambition dinshi" ,"hakane, toh da lbr ne" ,"a'a dama sonake zan dan fita shine nace bari nazo na miki sallama" ," ok ina zaka" ,"gidan gonan Abba" ,"toh se kadawo" ,"yauwa Ummi sena dawo" ,"a dawo lfy" ya fita ya shiga motanshi ya tafi gidan gona, bashi ya dawo ba se yamma lis, yana dawowa yayi alwallah ya tafi masallaci acan ya hadu da Sameer sukayi sallah, da suka fito *ASHRAF* yacewa Sameer "guy dan Allah ka shirya gobe muje school tare" ,"inaa nida zuwa school se wani Mondayn bade na gobe ba" *ASHRAF* ya girgiza kai yace "Allah ya shirye ka" ,"Ameen".

*WASHEGARI*
     Da sassafe *ASHRAF* ya tashi dayake lectures din 9:00am yake dashi,
saboda haka ya tashi yayi abunda zeyi ya shirya ya shiga motanshi yawuce.
Tashinta kenan daga barci ta duba lokaci taga 8:00am on dot ita dinda takeda lecture 8:30am, tana duba lokaci tace "Ya Allah ka yaye min wannan barcin" tana fada tana tashi daga gadonta se sauri takeyi, ko wanka bata tsaya tayi ba, tayi brush ta wanka fuskan ta tasa wani black jallabiya me white stones da white veil nd as always ba makeup se powder da lip gloss, sosai kayan suka mata kyau ta dau abunda zata dauka ta tashe Ashanty ta shaida mata ta wuce, sukayi sallama ta fita, koda ta duba lokaci 8:25 saboda haka ta kara daga kafa dan tayi sauri, tafiya takeyi ba tareda ta kalli gabanta ba, itadai fatanta ta kai hall kafin 8:30 saboda batason ace on her first day tayi latti, tana cikin tafiya taji taci karo da mutum ta dago da sauri tareda cewa am sor... sauran kalaman makalewa sukayi saboda ganin wanda ke gabanta, ganin beda niyyan yin magana yasa tace "wai meyasa kai bakason cewa sannu ne, dis is nt d first tym da naci karo da kai amma yanda zakace sannu shine matsalanka" shidai bece mata komai ba se binta da ido da yakeyi yana tunanin itace wacce ya gani kwanakin baya a airport ko ba ita bace, tsakin da tayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya shiga ya bude baki zeyi magana amma kafin yace wani abu har ta kara gaba.

   
_Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

واصل القراءة

ستعجبك أيضاً

Twenty Six Revenge بواسطة Grey

غموض / الإثارة

584K 38.4K 49
Khoon Thant Shein Wah+Sunshine SiThu
367K 6.7K 51
တစ်ယောက်ယောက်-------------ကျေးဇူးပြုပြီးးးးးးးးးး ကယ်ပါ------------------------------------------- ကိုယ့်ရဲ့ လှောင်အိမ်ထဲကနေ မင်းဘယ်တော့မှထွက်ပြေးလို...
150K 27.3K 102
English Name After the little crybaby enters the nightmare cycle Author(s) 菊长大人 Status in COO 127 chapters Associated Names Sau Khi Túi Khóc Nhỏ Tiế...
32.9K 6.6K 58
"Do you think betrayal never gonna pay back?" Come on let's go and seek it! One line ⬇️ It's a crime thriller love story. All based on 2 best frien...