ZYNAH

By Ishamoha

78.2K 4.7K 61

Here is a story of a teenage hausa girl Zynah who happens to come from a wealthy nd peaceful family but was h... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63

Chapter 9

1.4K 82 0
By Ishamoha

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

*ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

QUOTE:- "It's a very dangerous state. You are inclined to recklessness and kind of tune out the rest of your life and everything that's been important to you. It's actually not all that pleasurable. I don't know who the hell wants to get in a situation where you can't bear an hour without somebody's company."

_I dedicate dis page to *SAMRAH* I hrt u babe❤._

0⃣9⃣

*ASHRAF*
Tuki yake amma gaba daya hankalinshi na kan gurl dinda yagani a airport , tunda yake be taba ganin yarinyar da ta birgeshi wit lots of confidence ba sai wannan , wacce batada tsoro tunda ta iya daga kai ta kalli idon shi tafada abunda ke ranta ba tareda taji tsoro ko shaken wani abu ba. Da haka yaci gaba da tukinshi har suka kai gida cike ta tinanin ta , suna shiga gida tin daga compound Minal da Basma suka rugu a guje kaman ba en mata ba suka rungume Abbansu suna mishi sannu da zuwa, shima cikin murna ya amsa musu sannan suka shiga bangaren shi wanda yake ginin sama ne.

Suna shiga matanshi suka tarbeshi cike da fara'a, shima yayi farin cikin ganinsu. Nan Ummi tafara gaida shi "sanda zuwa Alhaji, ya hanya da gajiyan hanya" ya amsa da "Alhmdllh , amma gajiya na nan tukun har se na samu hutu" Ammi tace"sannu Alhaji, ai irin wannan tafiyan dole da gajiya" yace "gaskiya kam" Ummi tace "ba ka daiyi zaman jira a airport ba ko, dan beyi saurin tafiya ba","ko kadan shine ma ya jira ni" yana cikin magana sai ga *ASHRAF* ya shigo Ummi tace "kaci sa'a ka kai kan lokaci da nayi maganin ka yau" yana sosa keya yace " amin afuwa ranki ya dade ,tuba nake , next tym bazan makara ba" duk suka kwashe da dariya saboda yanda yayi maganan , shima dariyan yayi tareda zama kusa da Ammi, Abba yace "ina sauran yara na" Minal ta bashi amsa da cewar "Husna da Juwairiyya na makaranta , Hamma Fahad kuma wai golf stick dinshi ya karye, yaje shiyo sabo, Haydar kuma yaje bookshop ", "Allah ya dawo dasu duka lfy" duk suka amsa da Amin banda *ASHRAF* da bemasan me ake ciki ba. Basma ce tace " Abba my birthday is around d corner" yace " ok, any plans for d birthday" kafin tayi magana Ammi ta katse ta da cewar "yaran nan ku bari yayi wanka yaci abinci ya huta mana sai kuyi hira yanda kukeso inya tashi" Abba yace "a'a , bar min yarana sunyi miss din Abbansu ne kuma shima Abban yayi miss dinsu, saboda haka ku bari naji matsalan su" Ummi ta tace "inka biyewa yaran nan sai ku kai dare a nan wurin" yace yaji sannan ya juya wurin Basma yace "ina jinki wani plans kike dashi" tace "dama kawai ina so in hada small party ne, ni da frnds dina kawai","ok, bari zamuyi magana anjima, inna manta ki tuna min","toh Abba" kefa Minal "Abba zamuyi magana anjima, nt nw","toh shikenan".

Be gama rufe baki Hamma Fahad yayi sallama tareda Husna da Juwairiyya da yake ya biya islamiyyansu ya dauko su , suna ganinshi suka sake ihun murna tareda kaimai wani wawan hug amma banda Hamma Fahad ( as in babban yaya lol) shima rungume yaranshi yayi tareda da tambayansu ya makaranta, suka amsa da lfy, sai a lokacin yadago ya kalli Fahad yayinda su Husna ke zaune akan cinyarshi "Abba ka dawo lfy","Lfy lau Fahad","ya hanya da gajiyan hanya","Alhmdllh" sannan ya kalli *ASHRAF* yace "kai kuma lfy ka zauna kayi shiru kaman me daukan darasi" se a lokacin dukkan su suka ankara dashi dan harga Allah sun manta yana parlourn saboda yanda yayi shiru , kallon fuskan Hamma Fahad yayi, yayi murmushi sannan yace "lfy lau, me ka gani","naga kayi shiru ne , ko miskilancin ya motsa ne" yafada yana dariya, Ummi ta karba da cewar "ai kuwa, saidai miskilanci irin wannan shiru haka","ba wani miskilanci, kawai en maganan ne basa kusa,ko son?"cewar Ammi, shidai murmushi kawai yakeyi dan shi kadai yasan abunda yake ji tinda yabar airport ,ji yake inama ze kara ganin wannan *DAMSEL* din (sunan da zuciyarshi yasa mata) da yafi kowa farin ciki (ni kuwa nace sha kurumin ka indai *ZYNAH* ce zaku hadu) yana cikin tinani sukaji sallaman Haydar.

Yana gain Abbansu yafara rawa yana fadin "mai house ya dawo bara in mai oyoyo, mai house ya dawo bara in mai oyoyo" ai kuwa duk suka tuntsire da dariya saboda yanda yake maganan kaman waka da kuma rawan da yakeyi , inda sabo sun riga sun saba da shakiyancin shi ,dan shi kowa be bari ba harda iyayen shi. Nan duk suka ta hiran yaushe gamo sannan suka je dinning sukaci abinci, Abba ya musu sallama yace zashi ya hutu, Ummi tabi bayanshi da yake ita zata karbi kwanan.

*ZYNAH*
Suna kaiwa Zaria suka sauka sannan suka samu mai a daidaita yakaisu shagalinku hotel suka kama daki biyu ita tana room 55 shi kuma yana 56, tana shiga Uncle Yusuf ya biyo ta da kayanta yace " ga kayanki nan ki kintsa ki zo muci abinci" tace " toh Uncle inna gama zanzo" sannan ya fita ita kuma ta cire kayan jikinta tashiga tayi wanka tareda alwallah tafito tasa wando three quarter da top na _Jack nd Jones brand_ sannan tasa hijab har kasa tayi sallah, da ta idar tayi adduo'inta sannan ta mike ta cire hijab din ta dau wani karamin veil ta yafa a kanta sannan ta fito zuwa dakin Uncle Yusuf.

Knocking tayi ya bata izinin shigowa, ko da tashiga yana waya da daya daga cikin en matan shi, zama tayi taka kallon shi yadaga mata gira alaman lfy irin wannan kallo, dauke idonta tayi daga kallon shi tana mamakin yanda akayi yake playing gurls son ranshi yagama kuma yayi dumping dinsu a refuse bin, suna zaune akayi knocking ya mata alama da ta duba, ta tashi taje ta bude waitress ce ta kawo musu abinci ta bata hanya ta shiga ta ajiye musu abincin a kan center table ta fita se a lokacin ya ajiye waya sannan yataso daga inda yake yazo ya zauna kusa da ita yace "beauty ya akayi kin gaji ko" ta daga kai alaman eh, yace " bari muci abinci sai kije ki huta ko " tace "toh" sannan suka fara cin abinci, chips ne da ketchup sai fried chicken sai drinks, nan sukaci sukayi nak sannan ya kira aka zo aka kwashe plates din.

Kallon Uncle Yusuf tayi yace "da magana ne","eh Uncle" ,"toh inajinki , ya akayi" ," Uncle dama inaso inyi waya da Momsie ne kuma banda enough call card" ya dauki wayanshi tareda cewa " bari na kira su" nan yayi dailing numbern Momsie ta dauka tareda cewa " kaga dan hallak yanzu nake maganan ku nace har yanzu shiru ko baku sauka bane" yace "ai mun sauka tun dazu, da yake jirgin a Kaduna ya sauka seda muka shiga mota ya kawo mu Zaria muka kuma samu masauki sannan" ,"toh kun sauka lfy","lfy lau","Allah ya taimaka , ina Maman babanta","Amin , gatanan ta kosa in bata waya","bata mu gaisa" nan ya mika mata wayan ta karba " hello Momsie","na'am Maman babanta ya kike","lfy lau, Momsie wlh i am missing u already har na kosa na dawo","kinji ki, keda zakiyi karatu a nan din gabadaya a gwara ki saba tun yanzu","hum it will b hard for me to get used to it, yanzu ma inajin dama dama ne saboda Uncle Yusuf na nan","don't worry swthrt u will get used to it","ok Momsie,ina Daddy?" "yaje meeting","Islam fa","tunda muka dawo daga airport ya shige daki so daya ta fito,shima ruwa tazo tasha,duk tayi laushi","zan kirata ,i will talk to her bye","ok bye " suka yi hang din call din sannan ta mika mai wayanshi har ma ya fara bacci tace "Uncle ga wayanka","ajiye min, inkin fita ki ja min kofa","toh" sannan ta ajiye ta fita ta ja mishi kofa ta tafi dakinta.

Tana zuwa ta dau wayanta, dama can tana da call card saboda tana so tayi video call ne yasa tace ma Uncle Yusuf bata da call card. Tana daukan wayan ta kira Islam ta video call,tana zaune tana kallon _Barbie nd d three musketeers_ taji wayanta na ringing tana dubawa taga sunnan dake yawo kan screen din *BLOODY SIS* tsaki tayi ta yamutse fuska (nida kaina seda nace toh fa, me wannan ke nufi) kaman ba zata dauka ba har ya kusa tsinkewa sai kuma ta dauka ta saki ranta kaman ba abunda ya faru , a shagwabe tace "Sista sai yanzu kika san zaki kirani , ni nayi fushi" tana kallon kanwanta tace "ehhya yi hakuri, wlh tunda muka zo sai yanzu na samu tym din kaina","shikenan ya kike , kun sauka lfy" , "lfy lau" ," nayi missing dinki sosai sis d house is bored witout u"," nima haka u just have to endure for nw","ok Allah ya mudace " ,"Ameen, i hav to go nw i will call u later","ok bye","bye"suka kashe waya sannan ta kira Humaira , ringing daya biyu ta dauka "hello swthrt,idonki kenan naga kaman kin fada kodai idonane" ,"maybe idonki ne dan nidai lau nake","toh ykk ya lbr","ina nan lfy lau, lbr kuwa shine yau na hadu da wani arrogant jerk","tooohhh lfy dai ko meya miki for u to call him arrogant jerk","wai fa bige ni yayi a airport har kayan hannuna suka zuba, but dat guy couldn't even say sorry, in fact he just walk out on me","nd y ar u so angry just because of dat or are u affected","affected by who? him geez dats disgusting i can't even think abt dat"," c'mon say d truth" ,"hey wait, y should i b affected by him"," who knws maybe his handsome" tafada tana kanne mata ido daya "well u ar right he's handsome but dat is nt enough reason for me to get affected by him ok","ok as u say but tym will tell "tafada tana mata dariya, sosai ta kular da ita kawai sai ta kashe wayan, da Humaira ta sake kira sai ta kashe wayan gaba daya ta kwanta da niyyar bacci. Bacci zo yace ba zan zo ba sai tinanin maganan Humaira takeyi.

_Toh fa! ga Islam ta bullo da wani sabon salo ko me ta ke nufi........ sannan ka *ASHRAF* ya shiga tunanin yarinyar da yagani a airport har yana so ta sake ganinta a yayinda ita kuma *ZYNAH* tana mishi kallon mai girman kai har bata so ana mata maganan shi. Ku biyo ni dan jin yanda za'a warware wannan kullalen lbrn._

_Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

Continue Reading

You'll Also Like

151K 3.9K 24
ကိုကိုလို့ခေါ်သံချိုချိုလေးသည်မြတ်အတွက်နားထဲသံရည်ပူလောင်းချလိုက်သလိုပူလောင်လှသည်။ ဟိုကောင့်ကိုကျကိုကိုတဲ့လား ကလေးလေးရယ်။ ဒီကောင်ကဘယ်လိုခံစားရမလဲ။ ကို...
557K 15.1K 20
"ဘယ်သူကမှ သူရဲကောင်းအဖြစ်မွေးဖွားလာတာမဟုတ်ဘူး သူရဲကောင်းတစ်ယောက်၊ ခေါင်းဆောင်ကောင်းတစ်ယောက်ဖြစ်ဖို့ဆိုတာ ပင်ကိုယ်အရည်အသွေးနဲ့ ကိုယ်တိုင်လုပ်ယူထားတဲ...
368K 34.9K 101
ဇာတ်လိုက်က အရင်ဘဝတုန်းက အပယ်ခံလေးဖြစ်ပြီးတော့ ရုပ်သေးဘုရင် အဖြစ် ဖိအားပေးခံခဲ့ရတယ်။ ပြီးတော့ တော်ဝင်နန်းတော်ကနေ ဝိုင်းပြီးတော့ အနိုင်ကျင့်ခဲ့တဲ့ စစ်သ...