A fusace na ce "Allah ya tsinewa irin wannan albarkar! Kuma wallahi idan har sai ka ƙara zina dani tukun zaka sanya a cire sa, to na fasa Jafar, ka barshi ya kashe ni, domin ba zan taɓa yadda na aikata kuskure karo na biyu ba! Kuskure sau ɗaya kawai ake yin sa, muddun aka maimaita ya zama son zuciya.!

Ya maƙe kafaɗa cike da rashin damuwa ya ce "Is okay tunda baƙya so, dama taimakon ki zan yi ba wani abu ba, wata ƙyil ma bani bane asalin uban sa.!

Da sauri na ɗago ina tambayar "Me kake nufi.?

Kai tsaye ya ce "Ina nufin ko hanya na buɗe ma wasu, bayan na ɓula suka cigaba da zura guga.!

Na ɗago na kalle shi a razane yayin da zafafan hawaye suka cigaba da bin kumci na, cikin karkarwa na ce"Wallahi karya kake, ni ba mazinaciya ba ce Jafar! Ban taɓa zina ba, kai ne ka mani fyaɗe.?

" Haba.? Ya faɗa cikin rainin wayau.

Na kafe shi da ido cike da mamakin sa, ya taɓe baki  haɗe da maƙe kafaɗa ɗaya yana kallon cikin idanu na, ya ce "Ya kika ce.?

Ban ce masa komai ba na juya da niyyar bar masa gidan tun da dama bai rufe ba, amma sai tsinkayar muryar sa nayi yana faɗin "Wallahi ko ki tsaya in biya buƙata ta, ko kuma in fasa auren ki.!

Na juyo na zuba mashi ido, yayin da na saki murmushin da ya fi kuka ciwo ina faɗin "Ko na yi zina da kai ko kar na yi, a yanzu na gama fahimtar ba zaka aure ni ba Jafar! Tunda har zargi ya shigo cikin lamarin."

A tunanin sa hakan da ya faɗa zai juya mani tunani, sai ya yi saurin faɗin "Idan kika biya mani buƙata me zai hana na aure ki Meenari, na maki alƙawarin za'a fitar da cikin sannan muyi auren mu babu fashi, dama ke ce kika tunzura ni har na faɗi haka."

Na ce "Muddun sai kayi zina da ni sannan zaka aure ni, to wallahi Jafar sai dai idan kar ka aure ni, kuma ciki da kake magana ka fi kowa sanin na ka ne, zan je na samu Baffa na sanar dashi duk abunda ya faru, zan kuma haife maka abun ka, in kai ma mahaifin ka shi ya riƙe."

Da dai ya fahimci ba zan taɓa aminta da buƙatar sa ba,  sai ya ƙyalƙyale da dariya yana faɗin " Stop this nonsense gidan alaramma! Ladan Sani kike magana ko? Mtsee idiot, wannan ba ubana ba ne, uban wani Jafar ne daban! Ko ba mai gemu haka kamar dai na tsohon ki ba? Kar ki damu, ki haife ki kai mashi kin ji ko, ƙarin zuri'a ne, amma ki sani from now ba zaki ƙara ganin Jafar ba har abada, ya ci bulus, ya ci banza..!

Wani irin ƙululu ciki na ya yi, na kafe shi da ido, ya kuma ƙwashewa da dariya yana faɗin "Yeh! Jafar ba? You're kidding, ke yarinya ce, baban ki kuma shashasha, shi yasa ya kasa gane iyayen bogin da na tura mashi, but tunda ke yanzu kin sani, ƙya iya sanar dashi kin ji ko.?

"Allah ya tsine maka Jafar.!

Ya juyo ɗuwawu baya yana karkaɗawa, cike da shaƙiyanci ya ce " Kai haba? Sannu uwatata, ai ke baki ma san wani abu ba, wallahi tun farko ni bazan iya auren yarinya irin ki ba, wacce bata san komai ba sai ta wanke allo ta ɗauraye, daga secondary ta dasa aya, banda figure of speech bata san komai ba a boko, au na manta, ashe kin san yes da no, dama sha'awa ta kawo ni gurin ki, kuma na biya ma kaina buƙata sau ɗaya, dan kin ƙi aminta yanzu ba zan ji haushi ba sosai, ni da na ɓule leda mai zai dame ni don an hanani kingi.?

Ji nayi hawayen sun daskare, na tsaya kamar gunki har ya dasa aya, na lumshe idona, yayin da na lashe busassun laɓɓana na girgiza kai a hankali na ce "Nagode! Amma ka sani wallahil azim bashi ka ɗauka, muddun ina lumfashi sai na tarwatsa duk wani farin cikin ka, sai na ɗaura maka aure da baƙin ciki.!

" Ke Meye na waɗannan addu'o'in? Ba fa ƙyauta ki ka bani ba, ki na ji ko? Ki je gun tsoho ki karɓi ku ɗin neman auren da na kawo da kuma sadakin duk ki haɗa na sallame ki..!

  Ban ƙara ce masa komai ba, na juya na fice daga gidan, yayin da jiri ki ɗibata, na samu da ƙyar na fita wajen gate, na tsayar da mai adaidaita sahu ya kai ni gidan yaya, na amshi kuɗin sa na aiko Ilhami.

Suna zaune falo suna fira, na gifta su ba shige dakin ta, ba tare da ja gaida Abban su Ilhami ba, ya kalle ta cike da damuwa ya ce "KI je ki ji matsalar auta, bara in fita masallaci.!

Ya miƙe ya fice daga gidan, ita kam da gaba ɗaya hankalin ta na gare ni, ta taso a sanyaye ta shigo dakin, yayin da ta zauna gefen gadon haɗe da kiran sunana" Aminatu.!

Sai a lokacin wani sabon kuka ya kubce mani, na juyo na faɗa jikin ta ina faɗi "Jafar ya cuce ni yaya, ya xulumce ni, ya ci amana ta, ya ci amanar iyaye na..!

Jikin ta ya ɗauki ɓari, cikin ƙyarma ta ke tambayar" me ya faru? Me ya maki.?

"Ya ce ba zai aure ni ba Yaya..!

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un! Me ya faru kuma, me kika masa Amina tu.?

" Yaya ba da burin aure na ya zo ba, yaudara ta yayi, shi da kan sa yake faɗa, na shiga uku yaya, wallahi ya cuce ni.!

"Ba ki shiga uku ba Amunatu.!

" Wallahi na shiga uku, ciki gare ni, cikin shege fa yaya? Shine ya ce in ƙara ƙwanciya da shi sannan ya sa a fidda mani, da na ƙi aminta ya gaggaya mani maganganu sannan ya fiddo asalin kudurin sa, dan Allah ki taimaka mani a fitar dashi, kar su Baffa ya..

Ban kai ƙarshen zancen ba, ta miƙe ta shiga ban ɗaki da gudu, daga inda nake ina jin ƙarar fitar gudawar ta, ta sharari kusan awa ɗaya sannan ta fito idon ta jawur, ta zauna ƙasa Leda hade da dage kai tana fadin "Dama na san zaa Rina Amina, na tabbata duk namijin da ke da burin auren ja ba zai taɓa kusantar zina da kai ba, amma ban yi tunanin cin amana da rashin imani irin na Jafar har ya kai ga haka ba.!

Shiru ya ratsa gurin in banda sautin kukana babu abunda ke tashi, wallahi na yi nadamar zuwa na duniya, nayi nadamar sanin Jafar, da kuma yadda dashi, kamar an zabure ta ta miƙe ta finciki hijabin ta, ta ce "Faɗa mani ina ne gidan nasa.!

Na ce" Kar ki je Yaya, babi abunda zaki taras da ya wuce cin mutunci daga gare sa, ya ci mani mutunci sannan ya ci mutuncin Baffa na, amma na yi rantsuwa da mahaliccina bashi ya ɗauka..!

*RAMUWAR GAYYA Feedohm.*
*RAMIN MUGUNTA Slimzy.*

Mai buƙatar tagwayen littafai biyu. 300 ne kacal gaba ɗaya, mai son guda ɗaya zai biya 200.
Payment.
👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank.
Amina Jibril.
Shaidar biya.
07042277401.

Or

Katin Mtn
08036953516.
Shaidar biya ga ɗaya daga cikin waɗannan lambobin.
08036953516 ko 07042277401

*FEEDOHM.💞*

RAMUWAR GAYYA Kde žijí příběhy. Začni objevovat