A fusace ta ɗaga hannu da niyyar kifa mani mari amma na riƙe hannun har lokacin fuskata ɗauke take da murmushi, a tausashe na ce "Kar ma ki soma Matar Jafar, domin zaki aikata kuskuren da bazan taɓa yafe maki ba..!

Na fizgi hannun ta muka bar bedroom ɗin, muka koma falo, sannan na sake ta da ƙarfi ina murmushi," Zaki sha ruwan ne ko zaki juya inda kika fito. "

" Bazan sha, ruwan banza da wofi, wallahi Allah ba zai barki ba Meenari, sai kin wulaƙanta fiye da Habib, kema sai kin tozarta, muguwa munafuka, nasan sharri kika ƙulla mashi, domin yadda ya ɗauki mijin ki ba zai taɓa aikata hakan a gare ki ba, da kuma tsinannan ɗanki.. "

Na kuma jefa mata murmushi, sannan na harɗe ƙafa ɗaya bisa ɗaya ina faɗin" Tsinannan ɗan mijin ki dai? Amir ko? Ai ɗan Jafar ne ba nawa ba Hajiya Fadila, shi yasa na ce ki sha ruwa ki samu relief, idan ma kina so har bacci kiyi sannan ki tashi ki bar mani gida tun kafin in ci bura uban ki..! Na faɗa ina kallon cikin idon ta.

Ta ja da baya tana dafe kujeran, yayin da jiri ya ɗebe ta, na miƙe tsammani na nufi fridge na ɗauko mata ruwan faro, na daura bisa plate haɗe da cup, sannan na ƙarasa kusa da ita, na ɓalle marfin ruwan da baki na tsiyaya mata a cup na miƙa mata ina faɗin "Amir ɗan Habib ne...!

" Ƙarya ne Meenari..! Ta faɗa tare da hankaɗa ruwan ya zube a ƙasa.

Ban ce komai ba na koma bedroom ɗina, na janyo drawer da nake aje aje, na fito da wata envelop, na dawo falon har lokacin tana nan inda na barta, na zazzage mata pictures ɗin dake ciki a jikin ta.

Da mamaki ta fara dubawa tana kallona, kafin ta zube bisa rug ta saki wani azabben kuka tana faɗin "Kin taɓa auren Jafar dama? Ina kika san shi? Ta ya kuka samu yaro.?

Na murmusa "Na san Jafar Fadila, sanin da shi kanshi sarakan baiwa kanshi ba, duka tambayoyin ki zan amsa maki amma ina maman sa yanzu? Shin ta san abunda ke faruwa ko har yanzu ba'a faɗa mata ba..?

Ta kuma fashewa ta kuka" Ta rasu Meenari, Habib kai tsaye gidanta ya kai Jafar, ya faɗa mata abunda ya aikata, hakan ya sa ta faɗi a take sai dai gawar ta aka fitar, ta mutu da baƙin cikin Jafar akan abunda bai aikata maki ba Meenari me yasa zaki mashi wannan mummunan sharrin? Me ya maki wanda yayi zafi har haka..?

Na ƙyalƙyale da dariya "Abunda nake buƙatar jin kenan! Nayi farin cikin uwar sa ta mutu ta baƙin cikin sa! Masha Allah, yau burina ya cika..!

" Allah ba zai bar ki ba..!

Na daka mata tsawa, yayin da idona suka kawo hawaye, "Dallah ki dakata mani Fadila, ƙarya nake, kuma sharri na masa, bai aikata ko ɗaya daga cikin abin da na lissafa ba, amma ya aikata fiye da abunda na ce a baya..!

****

  Sunana *AMINATU ASSADDIƘU* Ni ƴar jihar Katsina ce cikin birni, Babana babban malamin addini ne, masani ne sosai ta ɓangaran musulunci, babbar makaranta gare sa wacce yake koyar da mutane ilmin addini, mu biyu ne a wajen iyayen mu daga ni sai Yaya Salima, wacce ta riga tayi aure abun ta, kasancewar daga makaranta secondary bama wucewa ko'ina, Mahaifin mu ya gina mu bisa tarbiyyar islama, ya bamu tarbiyya dai dai gwargwado, da shi da mahaifiyar mu mai suna Hafsatu  wacce kullun cikin sanyawar albarka ta muke.

Ina SS2 na haɗu da Jafar, komai ya sauya ta sanadiyyar sa.

   Babu abunda ke tausasa zuciya ta ya sani nishaɗi irin kalmar nan ta I LOVE YOU kalmar da na ɗauke ta, jigo, muradi tare da abincin ko wacce zuciya, a hankali na lumshe fararen idanu na tare da jifa babban yatsana a baki, wanda ya riga ya ya zame mani dabi'a muddun ina cikin yanayin farin ciki, na girgiza kai na cike da nishaɗi ina faɗin "I love you too gudan jini."

Banyi aune ba, sai jin saukar ludayin miya nayi a baya na, na gantsare haɗe da sakin ƴar siririyar ƙara "Auchh..!

Na juyo na sauke fararan idanu na bisa fuskar Ummi, a take na turo ƙaramin bakina ina lullumshe idanu, a shagwaɓe na furta "Wuƙar ne ta dakushe..!

"Ita ne kuma gudan jini.? Ta jeho mani tambayar ba zata, don van ɗauka ta ji me nake faɗa ba.

Kunya ta kama ni, na sanya hannu na rufe fuska ta ina dariya ƙasa ƙasa, a hankali na ce " Kai Ummi, kin cika sa ido, to ai kin san Jafar nake kira haka, shine kuma sai kin tambaye ni..?

Ta watsa mani harara "Anya kina da kunya ma kuma Meenari? Ni kike faɗawa haka.?

Banda turo baki babu abunda nake, har ta juya ta koma kitchen ta cigaba da girkin ta, maimakon in yanka mata albasar sai na cigaba da tunani na, domin na riga na sani zuciya ta, ta gama tafiya ga muradi na, wanda nake tunanin har abada bazan taɓa bari ba, har abada fa nake nufi, masoyi na na haƙiƙa kuma uban yarana, mun makance da ƙaunar juna har bana jin zamu iya rayuwa ba tare da juna ba, *JAFAR ALIYU* Bawan Allah, mutumin da ke sona fiye da rayuwar sa, mutumin da bai da wani buri da ya wuce ya mallake ni, a kallo ɗaya kacal muka kamu da makauniyar soyayya, na lumshe idanuna, babu abunda ke ƙara burge ni dashi fa ce ta yadda bai ɗauki rayuwar duniya a bakin komai ba, duk da kuwa ya sha faɗa mani Mahaifin shi ke da makarantar ALƘALAM UNIVERSITY KATSINA, amma sai dai Ummi da sauran ƙawaye na sun ƙi aminta da hakan, a cewar su makaranta ba tashi bace, ƙarya yake mani.

Sai dai in masu murmushin yaƙe, a raina ina faɗin "Duk zaku ci uban ku, ai ya ce da munyi aure zai bani shugabar makarantar, wallahi daga ku har zuri'ar ku sai na haramta maku shigar ta, don bazan taɓa baku dama ba."

Sai in rabu dasu, don a nawa wautar gani nake kamar har da bakin ciki ke sanyawa su karya ta ni, menene don ya ce ta baban shi ce? Mutumin da ya mallaki sardauna estate meye kuma ALƘALAM Allah na tuba? Duka fa mallakin baban sa ne.

Babban abunda ya ke ƙara burgeni dashi, shine ya tsani ƙarya a rayuwar sa, kamar yadda yake faɗi mani, domin duk iyayen kuɗin da Mahaifin shi ya mallaka, bai taɓa zuwa gurina da mota ba sai sau ɗaya, shima kamawa tayi, asali a ƙafa yake zuwa ko a machine ɗin haya, don ya ɓoye identity nashi, gudun kar mutane su dauke shi wani na daban.

Na saki lallausan murmushi tare da jingine albasar gefe guda, na miƙe tsam na shige ɗaki abina, na bi lafiyar katifa, ina sakin murmushi ni kaɗai kamar zautacciya, har ga Allah na gama ƙosawa muyi aure, ko mun tafi England, Canada, Paris, Sweden, Australia, Germany, da kuma uwa uba India da yayi mani alƙawarin sauka a gidan su Salman khan, don ya ce mani idan aka ɗaura auren ko sati ba zamu cika ba zamu tafi honey moon.

A take na janyo ƙaramar wayar Ummi da na mallake ta ƙarfi da yaji na danna lambar sa, tana shiga ina datse wa, domin kuɗin ciki ko ƙwandala ɗaya bana tunanin sun kai, na bi na rungume wayar a ƙirji har zuwa lokacin da ta soma ringing.

Sanyayyar ajiyar zuciya ta suɓuce mani, na cure guri ɗaya tare da janyo pillow na ɗaura bisa kaina sannan na kanga wayar a kunne ina faɗin "GUDAN JINI..!

*RAMUWAR GAYYA Feedohm.*
*RAMIN MUGUNTA Slimzy.*

Mai buƙatar tagwayen littafai biyu. 300 ne kacal gaba ɗaya, mai son guda ɗaya zai biya 200.
Payment.
👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank.
Amina Jibril.
Shaidar biya.
07042277401.

Or

Katin Mtn
08036953516.
Shaidar biya ga ɗaya daga cikin waɗannan lambobin.
08036953516 ko 07042277401

*FEEDOHM.💞*

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now