Ya kulle idon shi gam na ƴan mintina, kafin ya buɗe baki a dasashe ya ce "Jafar ne..!

Na murmusa tare da aje plate ɗin dake hannuna bisa dining table, sannan na ƙarasa shigowa falon ina taunar cingum, na ɗosana ƙuguna bisa doguwar kujera tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya ina faɗin "Ayyoh! Ashe ma dai dai na canka, tsohon ƙwarton ne! Yauwa, dama ina jiran ka, ka je bakin tap na baya, aƙwai kaya a bucket, ka dauka ka ƙarasa wanke su tas, na fara kuma bazan iya ba, dole na aje maka..!

Ya ja gwaron numfashi sannan ya juya ba tare da ya ce komai ba, ya sani sarai kayan wankin Amir ne ta aje masa, duk da kuwa wanki ake masu a gidan amma bata taba haɗa wa da nashi ba, haka zata tara su, na fitsari da kashe har sai lokacin da ta ganshi sannan ta sanya shi ya wanke su.

Bai da yadda zai yi haka ya tsugunna ya cigaba da wanke kayan, wanda yawancin su duk kashi ne a jiki, sai da ya ɗauraye ya shanya, sannan ya zauna bakin tap ɗin ya dafe kan shi, lokacin guda wasu hawaye suka fara silalowa daga ƙwayar idon sa, ya fara gajiya da waɗannan abubuwan dake faruwa..

"Jafaru..! Na ƙwala mashi kira daga inda nake tsaye riƙe da ƙugu.

Ya ɗago idon shi tab da hawaye ya ɗaura kaina, wani ja'irin murmushi na sakar mashi ina faɗin "Ga wasu nan ka haɗa da su."

A raunane ya ce "Fadila na asibiti tana jirana zan maida ta gida, kiyi hakuri madam idan na dawo zan wanke." Yayi ƙarya a tunanin shi zata fidda shi, don ina matuƙar ragawa fadila, ko zuwa suka yi gaida mu indai tare suke ko ƙala bana cewa dashi.

"Wallahi baka isa, ko Inna ce asibitin sai kayi abunda na sanya ka muddun kana son zama lafiya."Na faɗa kai tsaye.

Idon shi ya tsayar kan Amir da ya fito da gudu daga falo, cikin rashin sa'a silɓil tiles ya ja shi ya faɗi ƙasa, kafin in yunƙura gareshi har ya ri ga ni, ya saɓe shi a kafaɗa yana lallashin sa, wani so yake ma yaron wanda ban san iyakar sa ba.

"Idan ba aka aje mani yaro ba, wallahi sai na kifa maka mari." Na faɗa a tsawance.

Jikin sa na ƙyarma ya miƙo mani shi, amma maimakon da na amshe shi in rarrashe sa, sai ma mari dana kifa mashi na ja kunnen shi ina faɗin "Ban hana ka gudu ba a cikin gida..!

Har cikin ran sa yaji saukar marin nawa, ya kulle idon shi gam yana furzar da iska, yayin da Amir ɗin ya kuma tsallara ƙara, na angaje shi ina faɗin" Maza ka koma falo tun kafin in daka ka anan.."

"Komai za kiyi ki mani Meenari, amma dan girman Allah ki sassauta wa Amir, bai san komai ba, yaro ne." Ya faɗa a raunane.

Na kalle shi kallon ƙasƙanci ina faɗin "Meye matsalar da abunda zan ma yarona Jafar.?

" Nima yaro na ne..! Ya faɗa har cikin ran sa.

Na ɗauki shewa ina dariya, sannan na gumtse ina hararansa sama da ƙasa, a daƙile na tambaye shi "Wace uwar ta baka shi.?

Yayi shiru..

"Yarona! Yanzu na gane wane jinsin bunsura ya kamata na aje ka..! Na faɗa ina ɗage gira ɗaya.

" Let's forget the past Meenari." Ya furta yana kallon ƙasa.

Wani sakaran mari na kifa mashi yayin da idanu na suka rine, in manta fa ya ke nufi? Na mance da abunda ya faru a baya, na furzar da zazzafar iska daga bakina "Na manta ko Jafar? Ban taɓa sanin daƙiƙancin ka ya kai har zaka ce in manta baya ba! Wallahil Azim ba zan taɓa sarara maka ba muddun ban ga hawaye na ƙwaranya a idon ka ba, sai na tabbatar maka da baƙin ciki mara yanke wa a rayuwar ka, sai na tabbatar da ka wulaƙanta tun anan duniya."

Manyan idanun sa ya ɗaura bisa fuskata, da suka ri ga suka rine zuwa kalar jini, a raunane ya ce " Shin har sau nawa kike buƙatar ganin hawayen na wa Meenari? Duk abunda kika aikata bai isa kin rama abunda na maki ba? Bai isa kin manta ba? Ki ji tsoron Allah Aminatu, kar ki zama silar zubewar ɗan mutuncin da na jima ina tattali.."

Na murmusa, murmushin takaici haɗe da kunar zuci, yayin da hawayen da nake danne wa suka gangaro saman kuncina, na cije laɓɓana "Yaushe ne kasan Allah? Ai ban ma dauka ka fara sallah ba ma tukun? Mutunci kake magana ko? Har ka manta kai ne ka dagargaza yarda da amincin haɗe da mutuncin gidan mu? Ko ka mance wanene babana? Shehun malami ne masani addinin, mutun mai daraja da mutunci a idon duniya, amma da kalmar *so tak* ka kawar da duk wani mutunci nasa, da ɗaiɗaita mani rayuwa, ita wannan Yaudararrar kalmar kayi amfani da ita ka saka cuta a zuciyar sa, ya amince maka, ya yadda da kai, ka zamto silar jinyar sa har gobe..!

Hawaye na hango ƙwance bisa fuskar sa, na zabga mashi harara sannan na sanya bayan hannuna na share nawa hawayen.

"Ki yafe mani Meenari, nasan na aikata babban kuskure...

Na daka mashi tsawa ina faɗin" Dallah rufe mani baki, wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, kuma har gobe duk lokacin da na kai goshina ƙasa shin ko kasan ne nake roƙo? Ina tawassali da sunayen ubangiji na roƙe shi ya wulakanta ka Jafar, ya watse maka albarka, ya hanaka rayuwa cikin salama, ya sanya wuta ta zamto matabbata a gare ka...

Ya tsawan ce ya kira Sunana "Amina...!

Nima a tsawance na ce "Ai ban ƙarasa ba Jafar, Ina roƙan Allah ya haɗaka da fitina ta duniya da lahira, ya hana maka zama lafiya, ya tozarta ka...!

Ban san yadda aka yi ba, sai ganin shi nayi a gaba na a kiɗime, ya sanya tafin hannun shi ya wanka mani lafiyayyen mari haɗe da riƙe kafaɗuna yana faɗin "Ki dawo hankalin ki Meenari...!

Na fincike kafaɗa ta ina kallon shi a tsanake, mari na fa yayi da hannayen sa, a tsawance na cigaba da faɗin "Ina roƙan Allah ya watse maka albarka..

"Subhanallah, kina cikin hankalin ki kuwa Aminatu? Kin san me kike faɗa.? Murya Habib ta doki kunnuwa mu.

Wani azabben kuka ya suɓuce mani, na ƙarasa da gudu gare shi, na sanya hannaye na na rungume shi, sannan na cigaba da rai rai kukana mai tsuma zuciya.

Nan da nan ya ruɗe, ya juya a zafafe yana tambayar Jafar, me ke faruwa.

Bai bashi amsa ba sai jikin sa ya dauko ɓari, ya kuma daka mashi tsawa yana faɗin "Ka faɗa man me ke faruwa Jafar? Me ka ma Meenari ta? Me ka yi ma mata ta.?

Samun kai nayi da faɗin "Kama shi nayi yana sanya wa Amir al'aurar sa a baki, shine ya dawo kaina da zummar yi mani fyaɗe, don naƙi aminta shine ya kifa mani mari..!

Yadda idanun Habib suka fito waje ya tabbatar da maganar ba ƙaramin dakar shi tayi ba, ya ture ni daga jikin sa ya nufe shi ya cakumi wuyan shi yana faɗin "Maciyi amana ɗan iska....

*RAMUWAR GAYYA Feedohm.*
*RAMIN MUGUNTA Slimzy.*

Mai buƙatar tagwayen littafai biyu. 300 ne kacal gaba ɗaya, mai son guda ɗaya zai biya 200.
Payment.
👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank.
Amina Jibril.
Shaidar biya.
07042277401.

Or

Katin Mtn
08036953516.
Shaidar biya ga ɗaya daga cikin waɗannan lambobin.
08036953516 ko 07042277401

*FEEDOHM.💞*

RAMUWAR GAYYA Where stories live. Discover now