45/46

221 14 0
                                    

PRINCE AIRAN AND MAIOON
🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
(Love,Betrayal,Sacrifice,and sorrow)

✍️45/56✍️
Story
    And
Written by
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү  α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

Vote me on wattpad
YoungNovelist4

From the experience writer of.
🌺IHSAN🌺
🌺UQUBAR UWAR MIJINA🌺
🌺WATARANA SAI LABARI🌺
🌺KANKI KIKA CUTA🌺
And now with the most intresting one.

*Prince Airan and Maimoon.*

Dedicated to...
Muhamamd Namari Jr.
Aminullah Fulani.
Doctor Mhmad.
Misbahu Yelleman.
Saifullah Babajo.
Tnx for u du'a.

            💫

A zazzaune suke a fada mai Martaba da ammie fuskarsu duk cikeda alhini,Alhamdulillah kadai suke maimaitawa Abba yace"...Allah mungodemaka daya tsiretar daku,Ammie tace"...kada ku sake fita harsai munga abinda Allah yayi this ia serious,Khaleed yace"...toh Abba Insha Allah zamu kiyaye".

Hasna,Sadiq da Captain Haneef dasu Airan a zaune,Hasna tace"..kufara shiri kunkusa komawa gida nan da sati ɗaya,cikeda murna Maimoon tace"...masha Allah,Alhamdulillah,nayi farinciki,Airan yace"...kunaganin ba matsala,Sadiq yace"...shekararku daya da watanni anan ai kun daɗe kuma har yanzu su Abba suna cikin damuwar rashinku tunda basusan ko kuna raye ko akasin hakanba,Haneef yace"...hakane insha Allah komai yazo karshe,kuma nan da sati za'a taro agidan Abba,zaku shiga gida aranar kuma kafin lokacin daza'ayi taron insha Allah komai yanakan shiri.

Usman ya ɓoye damuwarsa yace"...Allah yakaimu lokacin,Aysha kam matar Aslam ta tsorata ainun da al'amarin dayafaru dasu,Hasna tace"...karku damu akwai matakan tsaro kuma mungano hanya wacce zamubi batare da kowa yaganmuba,Allah yataimaka cewar Zara matar Aslam wanda cikinta haihuwa yau ko gobe".

A washegarin Zara ta tashi da naƙuda inda ta haifi ƴarta mace mai kama da Aslam Usman sak,da kwana biyar matar Aslam Aysha ta haihu itakuma ɗa namiji wanda ke kama da Aslam sak,tare akayi suna inda Aslam yasaka mai sunan Airan shikuma Usman yasa mai sunan Maimoon dukda su Aslam sunce yasa sunan Mummy amma sam yaƙi donshi yana da reason ɗinsa,sosai su Airan sukaji daɗin takwarar da'aka musu wanda hakan yanuna haɗin kansu me ɗaurewane.

Yau saura kwana huɗu ayi taro a fada inda komai ya jagulema su Mummy sunrasa mafita kwata-kwata saboda yanzu ansaka sojoji a gate babu mai fita  sai randa za'a taro wanda duka shirinsu Hasna ne,gashi sunata gwada layinta amma baya tafiya gashi basusamu sun haɗu ba,basirarsu duk ta ƙare tunaninsu ya ƙare Mummy ta zauce donji take ranar taro zata iya harbe kowa a fada,yanzuma layin Hasna take gwadawa amma a kashe jefar da wayar tayi tayi tagumi ,can kuma saita tashi taƙira Mummyn Kamal tace"...karde ankama yarinyarnanne don wlh tasan sirrinmu karta tonamu ni yanzuma tsoron danake kar ranar tazo gashi saura kwana huɗu batazoba mu rasa abinyi,Mummyn Kamal tace"...Allah yasama ta mutu kinga bamu da fargaba,dallah can mara tunani inta mutu wazai taimakemu kide bari agama aikin saikimata fatan mutuwar daga haka ta kashe wayarta tana huci".

Yau takama friday saura kwana biyu ayi taro angyara duka masarautan amma a fadar su Airan za'ayi taron ,ɓangaren su Airan ma duk an gyara  ,kawai ranar taro ake jira,taron da Ahlinsu ne kawai zasuzo donyin addu'a da wata manufa wacce Hasna ce ta karfafa yin taron.

Ihu take kamar zata mutu Captain Haneef yace"...ku ganamata azaba saita faɗi waya aikata ta zubawa Ammie magani a abincinta,daganinta kasan ta azabtu sosai don duk jikinta ya fashe,wani ƙarfe kurtun sojan ya bugamata akai nan tasa ihu tana cewa zanfaɗa wlh zanfaɗa,Haneef yace"...muna jinki,cikin kuka tace"..dan Allah kamin rai ranka ya daɗe GIMBIYA Habeeba ce tasani wai inban aikataba zata kasheni ,a ranar bayan kuyanginta sungama aiki shine naje nasamata asirin a abinci lokacin tana wanka,bayan na aikata hakanne takoreni tace karnasake zuwa masarautar Khudba shine nake zama a ƙauyen dakukaje kuka kamoni wanda baida nisa da masarautad".

Hasna tace"...ku kunceta kubata abinci ayimata magani nan da ƴan kwanaki zamu tafi da'ita don bada shaida,jiki na tsuma tace"...wlh Gimbiya zata kasheni inna koma kumin rai ko kulata basuyiba suka fice agun".

Yadda su Hasna suka kama wannan baiwar kuwa shine bayan sun ƙarbi hotonta gun jakadiya,nan sukafara bincike harsuka gano inda take zaune a wani ƙauye kusa da masarautar shiɓe suka kamata suka kait cell,tasha wahala sosai a hannunsu kafin ta amasa laifinta tare da faɗin waya aiketa.

Yau asabar tana zaune tana feeding ɗin Noor Airan ya shigo da jaka sabuwa a hannunsa,sannu da zuwa ta masa sannan ta ajiye Noor ta ƙarbi jakar hannunsa ta ajiye tayi hugging ɗinsa tana i missed you today,murmushi yayi yace"...me too my Noor kinga yau naje kasuwar ƙauye naje na ƙarɓo mana jakar dazamu haɗa kayanmu don insha Allah gobe sai gida dukda zuciyata na harbawa,murmushi tayi me sanyaya rai tace"....karka damu ai komai yazo ƙarshe tunda mukasa Allah a al'amuranmu komai me ƙarewane,hakane Noor sai isa nakesonki"..

Usman ne yakalli matarsa da Little Moon yace"...yarinyarnan sak Maimoon,Zara tace"...aikuwa kamar ita tahaifeta,dataga yanayinsa ya sauya saita kama hannunsa tace"...ka ari jarumta kamar yadda kake da karkabar komai ya shiga ranka insha Allah komai yazo ƙarshe nasan kana addu'a komai zaizo da sauƙi ,rungumeta yayi yanajin nutsuwar samun mace tagari".

Hasna ce taƙira lokacin rayuwa tamata zafi tarasa mafita kawai taga ƙiran Hasna,jiki na rawa ta ɗaga Hasn tace"...Habeeba kwana 2 shiru,Mummy tace"...wlh kintada mana hankali amma Allah ya amsa mana addu'a tunda kinzo kafin ayi taron,meyafaru najiki shiru ne?,Long story saina shigo gobe zaki san meke tafiya ,to bakomai ɓari naƙira Hasiya nafaɗamata kundawo komai zai tafi normaƙ daga haka suka ƙatse ƙiran".

Captain yace"...amma meyasa kika sanar da'ita kina zuwa,eh nasan insukaga jini shiru zuwa gobe zasu canza shirin da mukayi amma in sukasan zanzo zasubar komai a hannuna kamar yadda muka tsara ,Sadiq yace"...hakane kinyi tunani maganar baiwar nan fa,captain Haneef yace"...itama goben zamu tafi ɗa'ita ,Allah ykaimu cewar Hasna".

Jabeer kuwa komai na gidan ya kammala a ahannunsa jira kawai yake gobe tazo jiyake kamar ya jawo goben da kansa,Mummy kuwa hankalinsu yanzu ya kwanta tunda sukaji ai Hasna zatazo,Airan dasu Aslam kuwa duk sun haɗa kayansu suna jiran gobe tazo saboda babu kamat gida kuma agaban iyaye daɗi,THERE IS NO PLACE LIKE HOME".

Yadda kasan Maimmon tazuba ruwa tasha haƙa taƙeji don gaskiya tayi kewar gida,ga yaranta yanzu watansu biyar sunyi ɓul-ɓul dasu kamar ƴan wata bakwai suna samu kulawa gun iyayennasu da tsohuwa harma dasu Aslam musamman uban gayyar  wato AIRAN.

Su Auta kuwa angirma anfara zama ƴen mata sunkai 15 yrs yanzu,kagansu kamar ƴan biyu saboda suna kama sosai ga ilimi ga kyau kuma suna samun kulawa gun abokin abba wanda yake zama da matarsa da ƴarsa ɗaƴa wacce itama take sa'anni dasu Auta sunanta Ƙhausar Abdallah,sun shaƙu sosai da'ita komai tare sukeyi gashi larabci raɗau a bakinsu,don akwai saurin ɗauƙar abu.

Mummy fa tasaki fuska da kowa sai faman fara'a take komai na tafiyarmata dai-dai burinta yakusa cika zatazama mai faɗa aji a masarautar Khudba bayan ta halaka kowa ta saka wanda takeso a kujerar,hakama Mummyn Kamal duniya ta musu daɗi sosai.

Ammi da umminsu Maimoon kuwa kallonsu kitse akan ruwa suke musu wanda sarai sun lura da farincikin dasukeyi amma basusan namiye ba kowa de da plan ɗinsa aransa sai gobe zamuji ya zata kaya.

ME SU AMMI SUKA SANI GAME DASU MUMMY.

MEYASA USMAN YABAR GIDA.

Duka amsar tambayarku tana gun YOUNG NOVELIST,saiku biyoni don na kusa ƙare liytafinnan dafatan yana nishaɗantar,faɗakar da kuma wa'azantar daku.

YOUNG NOVELIST✍️

PRINCE AIRAN AND MAIMOONWhere stories live. Discover now