Part 32

273 17 0
                                    

PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
PRINCE AIRAN AND MAIMOON
🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
(Love Betrayal, Sacrifice and sorrow)

✍️32✍️

Story
       And
Written by

KHADEEJAHT HYDAR ✨YOUNG NOVELIST ✨

✍️From the experience writer of ✍️

🌺IHSAN🌺
🌺UQUBAR UWAR MIJINA🌺
🌺WATARANA SAI LABARI🌺

AND NOW
🌺Prince AIRAN and MAIMOON 🌺

DEDICATED TO
ANTI FAUZIYYA❤️
ANTI NABEELAT🤍
INA K'AUNARKU SOSAI.

    
Fita yayi tare da jakadiya zuwa ɓangaren bayi,ganin yanayinsane yasasu shiga hankuƙansu,cikin kaushin murya yacema jakadiya wacce ke gefensa Mama suwaye ke aiki a ɓangaren Ammi?.

Ƙuyangi bakwai ta nuna duka suka fito suka tsaya jikinsu na rawa don basusan laifin dasukayiba,tafiya yafara batare da yayi maganaba sai jakadiya ce ta sallami sauran ƙuyangin tace ku kuma ku biyoni.

Binta sukayi jiki a saɓule zuwa part ɗin Ammi sbd ba kowa daga Airan jakadiya sai bayin daya ƙira,fuska ba wasa yace"....wacece ke kaiwa  Ammi abinci?,Shafa'atu aka nuna cikin in ina tace"...Eh ranka ya daɗe nike kaimata abinci kullum"....

Good, kenan randa tafara rashin lafiya ma kinkaimata abinci ko?,eh nakaimata amma bata ɗaki,lokacin tashiga wanka to amma dana dawo na tadda tana bacci, bayan ta tashine aka samu wannan rashin lafiyar tasameta"...

Yace".....to kenan kekikasamata magani a abinci taci waya aikoki?,a razane tace"....wallahi ranka ya daɗe bansan wannan zancenba wlh bansamata komai ba"...

Tsawa ya daka mata yace"...to waye ya shigo bayanke tunda in kinkaimata abincin yamma bayi basa kuma shiga saida safe,tana hawaye tace"....wlh bansaniba amma munhaɗu da mai aikin Mum a bakin ƙofa  zata shiga  ciki,amma harga Allah bansan meyakaitaba taƙarasa zancen tana hawaye"...

Da sauri yace"....wacece ita aje aƙirata,da sauri shafa'atu tace"...ranka ya daɗe Bilƙisu ce kuma annemeta anrasa ba'asan inda tajeba,Jakadiyace taƙara dacewa ba inda ba'ajeba nemanta amma babu labarin"..

Jikiyoyin kansa suntashi ruɗu_ruɗu tsabar ɓacin rai yace"...tun yaushene ba'agantaba?tace"....tunda Ammi ta kwanta rashin lafiya,jinjina kai yayi yace".....zaku iya tafiya ke kuma shafa'atu kizama cikin shiri don akowane lokaci zaniya nemanki daga haka ya juya zuwa part ɗinsu"..

Ƙiransu Khaleed yayi akan suyi sauri suzo amma karsu bari Usman yasan yaƙirasu it is urgent, cikin minti biyar sukazo part ɗinnasu damuwa ƙarara a fuskarsu..

Abinda yafaru  ya zayyanemusu suma sunyi matuƙar ƙaduwa da zancen,sannan ya ɗora da cewa tabbas ansata tayi aikinne sannan akace tabar fada gudun rana irin wannan,to amma tabbas nasan tana kusa da wannan masarautar saboda bazatayi nisa ba don zata sake zuwa aiwatar da wani aikin,kuma ni narasa waye yake son kashemana Ammi,abinda yasa nace karkuzo da Usman da Hydar shine ,banson suji maganar musamman Usman zaifi kowa shiga damuwa "...

Jinjina kai sukayi Khaleed yace"....dole saimunzamo masu saka ido cikin gidannan tunda yanzu muna gida,Ishaq yace"....karku damu Insha Allah zamusamu mafita fatanmu de yanzu Allah yabawa Ammi lafiya yakareta daga dukkan maƙiya mutum ko aljan,amin suka amsa"..

Jabir yace"...Bro muje guɓ Ammi ka dubata ko za'a ƙarbo magani,Airan yace"....ashe Abba yasa anbuɗe asibitin har anfara aiki gaskiya naji daɗi,Ishaq yace"....kuma sunan yayi kyau nasan Abba bailuraba saboda sai jiya dazamuzo nacema Sadiq yasa,Airan yayi murmushi yace"....wato sunan dakace zakasa kenan that's why kace nabaka zaɓin sunan ko lallema yaronnan zankamaka,dariya suka kwashe Ishaq yace"...kace dai yarannan  don bani ƙadai bane mu dukane muka shirya"...

Murmushi yayi yace"...tnx i really appreciate i love you guys ,we love u too suka faɗa in chorus,fita sukayi sukaje ɓangaren Ammi inda suka samu Usman da Hydar zaune a gefen Ammi,Usman nabata abinci abaki shikuma Hydar namata fifita"...

Sannu da aiki cewar Airan,murmushi Usman yayi yace"....don ina baiwa Ammi abinci shine aiki?,maida wuƙar Usman ɗin Ammi,zama sukayi suna mata sannu, dukda tana kishingiɗe hakan baihanata miƙama Airan hannuba"...

Da sauri yariƙe hannunta yana kallonta kamar zaiyi kuka   yace"....sannu Ammi na ya jikin?, kallonsa take cikeda tausayinsa don duk cikin ƴaƴanta babu wanda take so sama dashi saboda yadda tun yana ƙarami yake fuskantar hassada daga mutane,balantana lokacin data kwanta jinya tana yawan mafarkai akansa mara daɗi,fatanta tasamu lafiya tasa ido  da addu'a akan ƴaƴanta.
      
               🌸
           🌸*🌸
Ƙimanin  wata ɗaya kenan da dawowarsu Airan kuma alhamdulillah Ammi tasamu lafiya inda har anyi meeting a fada na cewar kowa ya fidda mata acikinsu wanda yaune alƙawari zai cika kowa zaije bada amsa,kuna haka takasance a ɓangaren su Maimoon ma.

Masarautar Khudba

Fada yacika da iyalan sarki Muhammad Musa don sauraren samarin gidan,taro aka buɗe da addu'a sannan sarki ya fara jawabi kamar haka,to alhamdulillah mungode Allah dayabamu ikon sake haɗuwa anan kuma kowa yasan musabbabin taron namu don haka ku nake sauraro yakai dubansa gasu Airan.

Su Airan saraken kunya shiru yayi saida waziri ƴace"...Ƴarima ku muke sauraro tukun yafara magana yace"...insha Allah Abba duk muncika alƙawarin damuƙa ɗauka"..

Masha Allah cewar Abba to muna saurarenku kowa ƴafaɗamana inda yasamu matar don bansan komai ya ɗau lokaci,Jabir ne yafara da cewa Abba a kano take sunanta Hafiza Ahamd,Khaleed kuma yace"...Abba ƴar nigar ce sunanta Khadeeja Sulaiman daga masarautar Mirya,Usman yace"...Dad nima yar nijar ce sunanta Fatima Yusuf,yar sarkin Tanis,Ishaq kuma yace"...Abba sunanta Rabi'ah Sani itama ƴar kano ce,Airanne ƙarshe ya kasa magana sai Usman ne yace"...Dad matar Bro kuma Sunanta MAIMOON Alhassan Musa  anan jigawa take a masarautar  Khadoob,Hafsat kuma tace"....Abba ni gaskiya ban tsaida mijiba"..

Jinjina kai Abba yayi yace"....Masha Allah ,zan aika waziri yamana bincike akan kowa ina fatan nasara,za'a saka bikinku nan da wata uku insha Allah"..
Su Hydar da Farouqh kuma sainan gaba.

Mummy ce tace"....ranka ya daɗe inada magana Abba yace"...munajinki saida tayi jim ƙadan don tasan duk iskancinta bata isa takawoma sarki wasa ba don haka cikin ƙasa dakai tace"....nifa nayiwa Usman mata"....

Kallonta kowa yake sororo musamman ma Usman dayaji zancen banɓaraƙwai,murmushi mai martaba yayi yace"...amma alhamdulillah agabanki ya faɗi zaɓinsa kuma na amince don haka zancenki ki janye,badon tasoba ta haƙura don sarki baya magana biyu"...


A ɓangaren su Maimoon ma haka takasance Aslam ne yafaɗi wacce yakeso wato Salma ƙanwar abokinsa Shareef,Maimoon kuma tace"....Sunansa Musa Muhammad ɗan masarautar Khudba ne,Kamal kuma   yace"...Abba nikuma sunanta Aysha anan jgwa take,Safiyya kuma tace"...Abba gaskiya niban fidda mijiba sainagama karatu"..

Masha Allah zansa amin bincike adukanku Allah yabada nasara daga haka ya sallami kowa.

To Alhamdulillah angama bincike a kowane ɓangare inda sunsaka sati mai zuwa zasu fara zuwa neman Auren ƴaƴannasu.

To muje zuwa.

Yanzu akafara fans kude kucigaba da bibiyata.

Taku a kullum
✨✨✨✨✨✨✨✨
YOUNG NOVELIST
ROYALTY
AUTARSU.

PRINCE AIRAN AND MAIMOONWhere stories live. Discover now