Part 28

370 16 0
                                    

🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
PRINCE AIRAN AND MAIMOON
🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
(Love,Betrayal,Hypocrisy,Sacrifice,Sorrow)

✍️28✍️

WRITTEN BY
KHADEEJAHT HYDAR
YOUNG NOVELIST

✍️From the experience writer of ✍️

IHSAN
UQUBAR UWAR MIJINA
WATARANA SAI LABARI

AND NOW

PRINCR AIRAN AND MAIMOON

DEDICATED TO THE LOVE ONES THE ONES I LOVE WIT ALL MY HEART

ANTI FATIMA
UMMITY
ANTI FAUZIYYA ONE LOVE TO U ALL.

Fans nabud'e wattpadd jiya,,follow, vote, like,and read my novels.

Masuson yin mgna ta Email.👇👇👇
Nanakhadeejamusa@gmail.con

Facebook kuma
KHADEEJAHT Hydar Young Novelist

Instagram kuma
Khadeejerht Muserh

Gamasuson shiga group din whatsapp kuma sumin mgna ta facebook d'ina sainajiku.

Kuma Inason ganin comment d'inku I mean sharhi me kyau, a wattpad ko a facebook,sainajiku fans I love u All.

ADDU'AR KARIYA DAGA BARAYI

امن مجيب مضطرا اذا دعاه ويكشف سوء و يجعلكم خلفاءالارض اءلهم مع الله قليل ما تذكرون.... سورة نمل

Kuduba cikin suratul naml.

To yau yakama sallah garin yacika da jama'a inda bakajin komai sai kid'e -kid'e ke tashi,kowa nata harkar gabansa ana shirye-shiryen zuwa eid.

Masaratuar KHUDBA kuwa duk ahlin gidan sunfito compound sunhau motoci,,me Martaba ne agaba saisu Ammi na bayansa, saisu Airan sannan dogarai na take musu baya.

Fili ne babba Wanda yacika da mutane makil babu masak'ar tsinke,kowa ya nutsu anajiran liman yabada sallah..

Ana gama sallah akayi hud'uba kowa yafara tafiya muhallinsa, mai Martabane sukafara tafiya inda akabar su Airan suna gaisawa da abokansu Waenda andade ba'a hud'uba.

Suna cikin raha da barkwanci wata mota ta danno Kai, dukansu babu Wanda yakalli gun kawai sunyi busy suna 'daukan hotuna.

Hasna ce da aneesa sukazo gun itakuma ta k'arasa gunsu Airan tana murmushi,kallonta sauran friends d'in sukeyi da alamun tambaya banda su Airan dasuka k'ara kauda Kai.

A hankali tace"....sannunku dafatan anyi sallah lafiya ?amsa mata sukayi shikuma Airan ya sauk'a daga kan motarsu yana niyyar shiga"..

Da sauri tasha gabansa tanamasa kallo irinna y'an duniya, murtuk'e fuska yayi yace".....get out of my way,k'ara gyara tsayuwarta tayi tace"...bazan fitaba saika min magana inba hakaba Wlh Nidakai zamu dad'e anan "...

Kallonta yayi da takaici yace".....banson raini da rashin kunya ni sa'ankine dazakizo Kina min magana?, murmushi tayi Wanda ya k'ara mata kyau tace"....to Kayi hak'uri amma Inason muyi magana da Kai"...

Dakyar yace"....inajinki meyafaru, a hankali tagabatar masa da kanta,,sannan tace"....in bazaka damuba I want to be your friend and ask u for forgiveness akan abinda yafaru rannan"..

Sassauta d'aurin dayayiwa fuskarsa yayi sannan yace"....is okay but Kina bawa manya daraja koda baki sansuba,tace"....nagode kuma zankiyaye,amma in bazaka damuba let's share contact"..

Kamar baze kulataba sai kuma yabata sukayi Sallama kowa yakama gabansa, suna zuwa gida akaci gaba da hidimomin sallah.

Washegari Airan ya shirya domin zuwa gun gimbiyarsa, sanye yake cikin shadda blue, sumarsa tasha gyara a kwance lub,baisaka hulaba .

Fuskarsa cikeda murmushi dakagansa kasan yana cikin farinciki, gun amminsa yaje yana sosa Kai, murmushi tayi tace"...ya akayine Babana ko gun 'Yartawa zakaje"?.

Jabir ne yace"....ai Ammi kema Kinsan irin wannan kwalliyar sai gun anti Maimoon, hararar Wasa Airan yamasa yana cewa Ammina saina dawo"

Dogarawa hud'u ne sukayi masa rakiya ,tafiyar awa biyu takaisu masarautar,,inda akayi musu iso zuwa cikin fada.

Dogarawan aka Kai b'angaren bayi shikuma akamasa iso zuwa fada don gaida me Martaba, fad'uwar gaba ce taziyarceshi,atake wani sanyi me tsanani yafara shigarsa,k'ank'yame jikinsa yayi fad'uwar gabansa yana tsananta...

Me martaba Sarki Alhassan Musa yana zaune cikin shigar alfarma, babbar rigace fara ajikinsa yasha rawani, fuskarsa me cikeda kwarjini da haiba tafito ras da'ita.

Da Sallama Airan yashiga fad'ar dogarai namasa k'irari, Zama yayi a k'asa yafara kwasar gaisuwa kansa a k'asa,amsa masa dogarai sukadingayi tare da shaida masa sarki ya amsa.

Aslam Wanda shine ya tarbi Airan yamasa iso zuwa fada yana zaune kusa dashi ,Sarkine yazubawa Airan ido yana kallonsa ko kiftawa bayayi,wanda ko Islam ya Lura dashi.

Airan ne ya d'ago don zuciyarsa tana ingizasa daya kalli direction d'in Sarkin koda kuwa a sace ne, 'dagowar dazeyi kawai sai idonsa yasauk'a cikin idon me Martaba..

Atare zuciyoyinsu ya buga,Airan yayi saurin d'auke kansa, me martaba ya zare glass d'in fuskarsa yana kallon Airan, tabbas Airan yana masa Kama da d'anuwansa ga kuma kamar dayaga yanamasa da Airan.

Gaisawa suka sukeyi a mutunce don lokaci d'aya yaji Airan ya kwanta masa, Sallama sukayima me martaba suka nufi guest room, shikuma Aslam yatafi don 'kiran MAIMOON.

Zama yayi yana tunanin me martaba wata zuciyar tace masa kama ce kawai, a haka MAIMOON tasamesa.

Murmushi yayi yana amsa sallamarta ,Kallonta yayi tana sanye cikin doguwar rigar shadda blue tayafa babban mayafi pink, ba makeup a fuskarta Amma tayi kyau sosai.

Gabansane yafad'i ganin kamar datamasa da little Deejansa, wannan Kama dasukeyi da ahlin wannan gidan abun tambayane, wannan yawuce Kama kawai, dole akwai wani abun,.

Sunsha firarsu irinta masoya daga bisani kuma yamata Sallama, sunata d'agawa juna hannu kamar karsu rabu, Saboda bazasu sake ganin junaba se a makaranta.

Yau jumma'a kuma yaune su Airan zasu koma makaranta, sun shirya komai nasu saura jiran lokacin flight d'insu.

To kubiyoni domin Yanzu ne Abubuwa zasu kankama..

Taku a kullum

🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍ROYAL BLOOD TYPING ✍️
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

PRINCE AIRAN AND MAIMOONDove le storie prendono vita. Scoprilo ora