Part 1/5

1.9K 41 1
                                    

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION
~*
*~ We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

💖ZINARIYAR💖FORUM TA GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION

Da sunan Allah me Rahma me jinkai,Allah nagodemaka daka sake bani wanj chance Na rubuta wani littafin.
Hakika rubutun littafi koda ace kirkirane t o tabbas kanada abin da zaka amfana aciki,ni kullum fatana da burina be wuce Na fadakar Na nishad'antar kuma Na wa'azantar da jama'a ba,ia Rok'on Allah ya isarmin da sakon har inda bana tsammani,Alhamdulillah Ala kulli Hall.
Happy Sallah to u all,a yau ni Khadeejaht Musa wacce kukafi sani da Khadeejaht Hydar nasake dawowa da wani sabon novel Wanda yahsa banban da waenda suka gabata ta fannin komai,fatana kawai kuci gaba da bibiyata har kusan abinda nake shirin sanar daku.
Tunkafin ayi nisa inason sanar da fans cewa,wannna karon banson likes da comment kamar su tnx ko ngd,a'a inason likes da sharhi hakanne zesaka nasan anatare,ngd sosai.
The Book is all about two Kingdom which have many crisis

🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
PRINCE AIRAN AND MAIMOON
🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
(Love,Betrayal,hypocrisy,Sacrifice, and sorrow).

Written By
Khadeejaht Hydar
Younge Novelist.

💗ZINARIYAR💝GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💞

Bismillahir Rahmanir Raheem.
🦚1🦚
Tafiya nake cikin motata k'irar benz ina tafiya inajin wak'ar gwanina D One,a zuciyata ni jikar Hydar nace amma garinnan akwai nisa inbadon so nake nakaiwa masu karatu gulma ba da bazan jeba,ina cikin tunanin naganni gaban wani k'aton masarauta wanda yake can garin jigawa,nace wash wannna masararutar akwai girma wlh ga shegen nisa amma gurin da garin abin burgewane saboda birni ne sosai.
A gaban gidan naga an rubuta welcome to KHUDBA KINGDOM.
K'arasawa nayi dakyar akabarni na shiga,ina shiga saura k'iris Na fad'i,ganin mugun kyau irin na masarautar ga ankashe dukiya don komai yaji ba k'arya,a haka nakai har bakin k'ofar parlourn harna kama zan bude naji ana magana sama-sama.
Waike AIRAN wane irin mutum ne kai Sam bakada kirki yaza'ayi daga dawowarta zaka mareta meta maka nifa Sam banason halinnan naka na zafin rai,k'arasa don naga mai maganar.
Wata dattijuwa nagani fara sol ga tsayi ga gashin ta har gadon baya, gafenta na dama na kalla naga maza biyu a zaune,hannun damanta kuma mata biyune kyawawa ajin k'arshe suma gashinsu har waist d'insu,mazan ta kalla tace".....kai Usman tashi kaje ka k'itamin yayunku kaikuma Hydar tashi d'akkomin wayata akan bed tashi sukayi zuwa inda aka aka aikesu.
Jim kad'an saiga Usman yafito daga wata k'ofa yace".... Ummi gasunan zuwa,zamansa befi da minti biyu ba saiga wasu samari sunfito cikin kaya iri d'aya black shirt da blue jeans,kowannens
u kansa a d'uk'e,haka suka k'araso suka zauna a k'asa."
A raina nace to wane iyayinne na sadda kai k'asa,Ummi ce tacigaba da fad'a kamar ta ari baki tace"....wlh AIRAN ka shiga hankalinka banson zafin ran banza daga zuwanta zaka mareta akanme?, atare naga sun d'ago suna bata hak'uri,saurin ja da baya nayi na murza idona don gaskata me idanuna ke gani."
Ganin dagaskene yasa na matsa don sake kallonsu,Maza ne su Hud'u kamanninsu sak iri d'aya ba tainda suka banbanta bazaka tab'a ganesuba saboda kullum tare suke kuma shigarsu iri d'aya.
Azuciyata nace"....to waye AIRAN acikinsu?"
Asalin Labarin
Sarki Muhammad Musa II,d'ane ga Sarki Musa Kalla,Yana da mata d'aya mai suna Aisha,aurensu da shekara 3 Allah ya azurtasu da y'an biyu maza Wanda D'aya yaci Suna Muhammad d'ayan kuma Alhassan.
To haka suka taso cikin masarautar duk kowa na sonsu banda kawunsu d'an uwan mahaifinsu mai suna Malam Bala,to sanadiyyar k'iyayyar da Malam bala kemusune yasa aka sace Alhassan,jin wannnan labarin masarautar ta girgiza anyi nema anyi nema har angaji kuma a lokacin sunada shekaru biyu a duniya,har aka gaji da nema aka hakura,sakamakon hakanne Sarki ya kamu da ciwon zuciya har tayi ajalinsa,bayan rasuwarsa ne aka nad'a Sarki na yanzu wato mahaifin su AIRAN.
To alokacin da'aka nad'asa sarauta beyi aureba,to bayan hakanne yayi auri da matarsa ta farko wato Gimbiya Fatima wacce take y'a tilo ga wani Sarki a wani k'auye ,lokacin dasukaje wasa anan yaganta ya nuna Yana sonta daganan akayi magana akayi aure.
To bayan aurensu da shekara d'aya ne Allah yayima mahaifiyar sarki rasuwa,masarautar ta girgiza sosai da rasuwar mahaifiyar Sarki .
To bayan arba'in komai ya dawo normal dukda a cikin zuciyar Sarki abin da ciwo saboda ita k'adai ta rage masa ya rasa d'an uwansa tun suna yara ga mahaifinsa ya rasu.
To Gimbiya Fateema ganin bata haihuba har lokacin yasa ta shawirci Sarki akan yayi aure,dakyar ya yarda saboda tsananin son dayake mata,bayason ya had'ata da wata tazo ta haihu ta raina ta saboda sam baze d'auki hakanba.
To haka ya nemi auren wata Gimbiya mai suna Habiba,to bayan auren da wata uku Fateema ta tashi da laulayi inda ana bincika aka gane ciki ne da'ita.
Murna gun sarki da Fateema kamar me,harda hawayen su don murna wanda hakan sam beyima Habiba dad'i ba.t
To ahakan tafara neman hanyar zubar da cikin Wanda Allah be bata sa'a ba, saboda har Cuba tasamata a abinci amma cikin be zubeba,kuma sarki jin haka har sakinta yayi dakyar yanaidata hakanne yak'ara rura wutar k'iyayyar da takemata.
Bayan wata tara ta haifi y'a y'anta maza hud'u,kowa a fada yaji dad'i,sarki harda kukan murna,amma banda Habiba bak'inciki kamar ya kasheta.
Ran suna yara sukaci suna kamar haka Musa me sunan Mahaifin Babansa Wanda akecena AIRAN, se Jabir,Khaleed,se Ishak.
Anyi shagali kamar ba gobe,haka tayita renonsu cikin koshin lfya.
Bayan shekara d'aya aka haifi,usman,shima tsak'aninsa da Hydar shekara d'aya.
Said aka haifi Nafisa, daga ita se auta Khadeeja (Deeja).
Habiba ta haifi d'anta sulaiman wanda yake sa'ansu AIRAN, se k'anwarsa Hafsa sa'ar Khadeejah.
To dukansu sun taso cikin son juna Wanda hakan Sam bayayiwa Habeeba dad'i, saboda ita burinta Suleiman yayi sarauta Wanda tasan hakan bezeiyu ba,se ta k'awar da AIRAN tunda shine Babba.
Kullum suna mak'ale da juna dukda shi AIRAN akwai miskilanci amma akwai son y'an uwansa harma dasu Suleiman.
To tirkashi kubiyoni donjin yazata kaya,da jin labarin d'aya masarautar.

PRINCE AIRAN AND MAIMOONWhere stories live. Discover now