“Ranka ya dade ayi hakuri dan Allah ban san nan gidan ba ne, na dauka can makota ne Wallahi”

“Ba komai”

Sadan ya fada bayan ya fito daga motar fuskarsa ba yabo ba fallasa, ya nufi kofar falon, kamar yadda ya sani at early morning irin wannan lokacin ba a tararda kowa a falon by this tike yasan Siyama da Suraiya suna dakinsu, Siyama na shirin scul Suraiya kuma na shirin zuwa aiki idan aikin duty safe ne da ita. Kai tsaye kitchen ya nufa inda yake jin motsin Mommy tana magana da mai aikinta Rahama. A bakin kofar ya tsaya ko sallama ya kasa yi balle ina kwana. Kallo daya Mommy tai masa ta san danta be yi bachi ba, domin idonsa sun so su kumbura, and be saba zuwa gidan da wuri haka ba.

“Rahama je ki yi wani aikin bar ni da kitchen din”

Cewar Mommy dan ta samu damar magana da danta ita kadai.

“To Hajiya”

Sai da ta gaishe da Sadam sannan ta ratsa gefensa ta fice daga kitchen din. Mommy ta dauko wuka ta cigaba da firaye dankalin da Rahama ta aje tana fadin.

“Kaje jiya kun gaisa da Aleeya, sai ka kara tabbatar da ba ita zuciyarka take so ba ko? Wata kila ma ka ganta tana tadi da wani ko kuma tana cikin gida abunta, da ka kawo sai ka kasa zaune ka kasa tsaye, tunaninta ya addabeka kana ta neman yadda za kai ka cire son ta a ranka ya saka son Aleeya, wannan tunanin ya hana ka bachi har safe right?”

“Yes Mommy”

Ya fada yana zuba hannayensa aljihu tare da doso cikin kitchen din. Mommy ta juyo da kyau ta kalleshi.

“Kasan meye favorite? Karka fara abunda kasan ba zaka iya karasa shi ba, kawai kaje ka fadawa Daddy ka cewar Aleeya batai maka ba”

“No ba zan iya ba, Daddy zai jidadi idan na aureta kuma aurenta zai kara kusancina da Zinneera”

“You See Zinneera dai, ita ranka yake so ba Aleeya ba, zaka cutar da ita ne kawai idan kace ka aureta bayan kuma yayarta kake so, ka rayu da Aleeya da gangan jikinka, Zinneera kuma ta rayu da Sadiq da da zuciyarka da bata san tana tare da ita ba, daga sai ka fara cutar da kanka kuma ka cutar da Aleeya, sannan shaidan ya shiga Zuciyaka ya fara raya maka abubuwan da zaka dawo daga baya kana nadama, zuciyarka tai ta sosuwa da ganin Zinneera gidan wani, Aleeya kuma tai ta bakincikin mijinta yana son yayarta”

Mommy ta fada tana murmushi. Jingina yai da freezer yana sauke ajiyar zuciya.

“Mommy akwai rashin kyautawa idan na ce zan yi son kai dan na auri Zinneera da wane idon zan kalli Sadiq? Da wane idon zan kalli Daddy ya fada nasa ina son Zinneera?”

“Da idon da ka kalleshi kace mishi ka karbi zabinshi, akwai rashin kyautawa a auren Aleeya sannan na rayu da soyayyar Zinneera, daga Aleeya har Zinneera ba za su saurareka ba, mahaifinka kuma ba zai yafe maka ba, ni kadai ce zan maka uzuri a lokacin da bani da ikon yi komai akai, ba zaka taba iya cire son Zinneera aranka ba har abada ko da ko tana gidan wani ne  domin ita ka fara so, dan haka ka daina wahalar da kanka”

“Mommy ba zan miki karya ba, Wallahi ina son Zinneera sosai”

Ya fada cikin yanayin damuwa.

“Idai har kana son ta, kai abunda zaka iya ka mallaketa, domin auren Aleeya a yanzu zai iya haddasa kiyayya a tsakaninsu, daga ranar da Aleeya ta gano Zinneera kake so, zata fara tsanarta kai ba zata ga laifinka ba,sai tai tunanin Zinneera ce tai abunda ya dauki hankalinka har ka fara sonta haka mata suke so you should be very carefull”

Iskar bakinsa ya busar ya kunna tap din kitchen din ya wanke fuskarsa.

“What a surprise Mommy's Favorite tun da safe”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now