Biological Mother

1.9K 299 35
                                    

A yadda ta farka da nishadi ya kawar da duk wani tunani da take na halin da Sadiq zai shiga. Yau bata zuwa scul dan haka ita tai shara tana gintsa gidan. Umma kuma ta shirya abun karyawa, bayan sun karya Aleeya da kanenta suka wuce makaranta. Umma kuma tana daki tare da Abbah domin yau tafiyar rana zai yi saboda motarsa tana gurin gyara a can ta kwana sai shabiyu na rana zaije ya karba kamar yadda suka kai da mai gyaran, daman Nabeel kam tuni ya fita gurin aikinsa domin hana cikin malaman dake taron latti. Zinneera na tsakar gida tana wanke wanke Hajiya Karima tai sallama muryarta har wani gargada take.

“Wa'alaikissalam”

Zinneera ta amsa sannan ta gaisheta.

“Ina kwana?”

“Lafiya kalau”

Ta amsa tana fashewa da kuka. Hakan yasa jikin Zinneera ya dan yi sanyi, ganin babbar mace kamar ta tana kuka, sai ta soma kiran Umma.

“Umma ga bakuwa”

“Ba gurin Ummanki na zo ba, gurinki na zo”

“Ni kuma?”

Zinneera ta nuna kanta tana kokarin tashi tsaye tare da zare hannayenta daga wanke wanken da take. Sai Hajiya Karima ya gyada kai tana kuka marar sauti ta matso kusa da ita.

“Eh gurin na zo”

Fitowa Umma tai sai ta tsaya cak kamar an dasata a gurin ganin haka yasa Abbah ya taso ya fito.

“Me kika zo yi gidana Karima? Ashe rashin kunyarki ya kai har ki taka kafarki cikin gidana? Tirrr da ke Wallahi kuma fita ki bar min gida bana son ganinki”

Cikin tsananin bacin rai Abbah hake fadin haka.

“Abbah wacece wannan?”

“I am your biological mother”

Hajiya Karima ta fada a take ba tare data kula da maganar da Abbah yake mata ba. At first Zinneera bata dauka da ita Hajiya Karima take ba, musamman ta taji tayi kalamin da yaren nasara duk kuwa da kasancewar ta ji abunda ta fada, amman bata dauka kalmar tana da alaka da ita ba. Sai dai ganin hawaye a idon Umma ya katse mata duk wani hanzari tare ta raunana mata zuciya.

“Abbah wacece?”

Ta sake maimaita tambayar.

“Ni mahaifiyarki ce”

Cewar Hajiya Karima cikin kuka. Bata jin taji abunda ya fito daga bakin Hajiya daidai har sai da Abbah ya karaso kusa da ita ya dafa kafardarta ya nuna mata Hajiya Karima.

“Wannan matar da kike gani ita ta haife ki ke da Nabeel, ba Safiya ba Safiya Aleeya da Larai da Aliyu kawai ta haifa amman ke da Nabeel ba yayanta ba ne, Safiya ce ta shayar da ke har kika kawo yanzu, wannan matar da kike gani guduwa tai da bar ni ni da ke da Nabeel saboda talauci saboda bani da shi, ita ta dauki cikinki wata bakwai aka haifeki yar bakwaini, kin ga gurin da ta aje can ta tafiyarta ba tare da ta damu da ki rayu ko ki mutu ba”

Abbah ya karasa cikin kuka yana nunawa Zinneera bakin kofar dakinsu. Sannan ya kalli Hajiya Karima wacce ke ta aikin kuka ya ce

“Na fada mata shine burinki? Fitar min daga gida ko na wulakanta ki”

Kamar Umarni take jira sai ta juya da sauri ta fice tana kuka. Bakin kofar dakin da Abbah ya nunawa Zinneera take kallo hawaye na fitowa daga idonta da dai daya.

“A'a ni ban gane ba, Abbah ni ban gane ba”

Ta fada tana maida dubanta gurin Abbah, sai Abbah ya kasa ce mata komai ya nufi dakinsu yana kokarin tare hawayen da zasu sake zubo masa. Sai ta nufi gurin Umma ta kama hannayenta ta rike.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now