ZR-08

3.1K 455 75
                                    

Da sallama ta shiga gidansu Maman Ramatu. Sai da suka gaisa sannan ta fadawa mata abunda ya kawo ta.

"Wai Umma ta ce na zo na karba mata kudin adashe"

"Allah sarki, ai nasan ta yi hakuri kudin ne har yanzu ba a hada ba Wallahi, ki ce mata tai hakuri idan na hada kudin zan aiko mata"

"Tau"

Ta amsa tana juyawa da zimmar tafiya.

"Sai anjima"

"To a jima da yawa"

Tana fitowa kofar gidan sai ta ga Sadam tsaye yana kallonta fuskarsa da murmushi, ta yi mamakin ganinsa sosai bata dauka yana nan yana binta a baya ba.

"Biyoni kai?"

Ya gyada mata kai, sai ya mikamata sim dinta dake hannunsa.

"Na gode"

Ta fada bayan ta karba. A nan ma kan ya gyada, sai kawai ta kama hanya rike da sim din shi kuma yana tsaye a gurin yana kallonta. Har ta bar kwanar gidan bata waigo ba, ba macece mai tafiya tana yawan waige waige ba, tana maida hankalinta a gabanta idan tana tafiya, wannan yasa mutane suke mata kallon mai hankali da natsuwa.
Da sallama ta shigo gida murya can kasa kasa, Umma ta amsa mata ba tare da ta dago ta kalleta ba.

"Umma ta ce wai kudin ba su hadu ba, kiyi hakuri idan sun hadu zata aiko miki"

"Tau"

"Umma baki raba abinci da ni ba?"

Ta tambaya kalar tausayi.

"Na raba da ke amman nan gaba kadan zan daina dafa abincin da ke, dan ba zan cigaba da ciyar da mahaukaciya ba"

Wani irin kololon bakinciki taji ya taso mata akan wannan furucin da Umma tai, har ga Allah ita dai tana ganin kanta a mai hankali sam bata ganin abubuwan da take akwai rashin hankali ko natsuwa a cikinsu.
Hanyar kitchen ta nufa sai Umma ta kwala mata kira.

"Zinneera dazun kanen Sadiq sun zo nemanki basu same ki ba, kila su dawo yanzu dan haka karki yi wani wawanci kanen miji su tarar da ke ba a kintse ba"

"Ai sun je makaranta"

"Kin gansu?"

"Eh tare ya dauko mu ya sauke su a hanya saboda dayar tace min wai ban dace da shi ba"

Umma ta tsaya kallonta.

"Wani abun ki kai, da baki yi wani abun ba da babu yadda za ayi ta kalleki haka kawai ta ce baki dace da shi ba"

"Fada ta tarar muna yi da wani dan department dinmu, amman Wallahi Umma shi ya mareni kuma ban masa komai ba..."

Bata karasa ba Umma ta tari nunfashinta.

"Yauwa ai idan ba ki saida hali ba, ba ki amsa sunanki ba, idan baki ja mana zagi ba to hankalinki ba zai taba kwanciya ba, Allah ya wadaran halinki Zinneera Wallahi kin ji haushi kowa yana kokari yai taka tsantsan da kanen miji amman ke kin zubar da mutuncinki tun kamin ki shiga cikin gidan ma, bari Abbah kin ya zo karatun nan ma ba zaki cigaba ba, dan in akai sake sai ki kwaso mana abun kunya tunda ba hankaline da ke ba, kara a zo ayi ta tare ni dai na gaji da ke, na gaji da rayuwar nan taki, kara in aure zai miki yai miki idan kuma daukeki zai yi ya kai wani gurin na dauke ni dai na gaji da ke na gaji da halin nan na ki Zinneera..."

Umma ta fada idonta cike da kwalla. Fasa shiga kitchen din tai sai ta nufi dakinsu ita ma nata idon cike da kwalla, saman katifarsu ta kwanta a take hawayen idonta suka soma zuba.

"Ni dai Allah yasa na mutu na hutu, kowa cewa yake ba ni da hankali, Umma ta tsane Abbah ma yanzu ya fara tsanata kowa yana min kallon mahaukaciya, har Sadiq din ma"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now