Some Words

1.1K 126 25
                                    

SADIQ POV.

Wani bangere na asibitin ya nufa bayan ya fita daga emergency din. Bakinsa ya cika ma iska ya fitar ya shafa kansa, yana jin rashin dacewa a akan abunda yai ma Sadam a gaban iyayensa, amman Sadam din ne ya cika shigar masa hancin da yawa, and he can't controlling himself idan ransa ya bace. Ya dade a harabar tsaye sannan ya juya ya nufi gurin daya faka motarsa, yadda ya fisgi motar kai kace ba a asibiti yake ba. Kai tsaye gidan Hajiya Karima ya wuce a tunaninsa ita ma tana da hakkin sanin halin da Zinneera take ciki ganin itama yarta ce, hakan kuma ba karamin kusanci zai kawo tsakaninsu ba.

Horn daya yai aka bude masa gate din ya faka motarsa harabar gidan, sannan ya bude motar ya fito ya doshi kofar gidan. Door bell ya danna sau biyu sannan wata dattijiwar mata ta bude masa kofar bakinta cike da goro.

“Sannu da zuwa”

Be amsa ba ba, sai kawai ta dora da neman Hajiya.

“Hajiya Karima na ciki?”

“Eh tana nan ciki sai dai jikin nata ne bata jinsa da dadi”

“Ki ce da ita ta yi bako”

“To”

Dattijiwar ta juya ta koma ciki, bayan yan mintuna ta sake dawowa.

“Gata nan fitowa”

“Na gode”

Ya fada yana jinginawa da kofar, ita kuma ta koma ciki. Tunani biyu ne ya zo masa a rai, ya fada mata gaskiya ko karya fada? Idan be fada mata gaskiyar cewar Zinneera bata da lafiya ba, to me zai ce ya kawo shi? Idan kuma ya fada mata hankalinta zai iya tashi, wata kila ma dalilin abunda ya faru ne ya haddasa mata ciwon.

“Ahh Sadiq ne? Miyasa baka shigo ba”

Ta fada cikin muryarta ta rashin lafiya, fuskarta ya dan soma kumburi. Juyowa yai ya kalleta.

“Eh Hajiya, ance baki da lafiya”

“Eh fever ne kawai, ka shigo mana”

“Aa ba sai na shigo ba, Allah kara lafiya”

Be jira ta amsa da Amin ba, ya juya ya soma saukowa a stairs din dake gurin babbar kofar falon.

“Sadiq...”

Jin ta kira sunansa yasa shi ya juyo.

“Ba zaka zo haka kawai ka duba lafiya ko kuma ka duba ni ba, idan akwai wata matsalar ko wani abun daya kamata na sani ko na ji ka fada min kawai”

“Zinneera ce bata da lafiya har an kaita asibiti kuma an bata gado”

Ya fada mata kai tsaye yana saka hannunsa a aljihun shaddar dake jikinsa mai ruwan madara. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u shi tai ta maimaitawa har sau uku sannan ta tako kofar ta fito.

“Miya same ta?”

“Nima ban sani ba, kawai dai naga ya kamata ki sani ne shiyasa na fada miki”

“Wace asibitin aka kaita?”

“Gaskuwa Hospital, tana Icu unit 4”

“Okay gani nan zuwa”

Da sauri ta juya ta koma ciki, shi kuma ya karasa gurin motarsa ya bude ya shiga ya, yana fita daga gidan ya dauki hanyar asibitin.

ZINNEERA POV.

Ta dauki awa hudu tana bachi, har Abbah ya zo ya koma, sai su Razinatu da Gwaggo Nana suka zo a dakin suka tare sai da Sadiq da Hajiya Karima suka shigo sannan suka fita. Aka barta daga ita sai Nabeel da Sadiq, tashi Nabeel yai ya fita ya bar mata dakin, hakan kuma ba karamin sosa mata rai yai ba, sai dai babu wani abun da zata yi bayan binsa da kallo har ya fice.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now