ZR-10

2.8K 457 84
                                    

SADAM POV.

A hankali yake tawa kamar mai tausayin kasa, daidaikun mutane da baben hawa dake kai kawo a tsakanin unguwar zuwa babban titin daya hada manyan motoci. Abu daya ke masa yawo a kwakwalwa, zancen Sim din da Zinneera tace masa an bata waya taba? Tace shi bayan kuma be san ya bata layin ba, ba shaye shaye yake ba balle har yai tsammanin ko ya bata shi ba a hayyacinsa ba.

"Indai da gaske an bata sim din ai ba zan ganshi ba, bari na duba gurin da na aje shi"

Ya fada a fili yana fiddo wayarsa dake ringing yai picking call din ya kara a kunne.

"Sadiq"

"Kazaure kana ina?"

"Gani hanyar gida na fito daga islamiya"

Daga dayan bangaren Sadiq yasa dariya.

"Are you kidding me islamiya fa kace malam?"

"Yes, you know yadda nake son zama malamin islamiya ai, a can ma ina karantarwa, a wani masallaci na yan istabul"

"Oh men kayi abu mai kyau ban tsammaci zaka iya a haka anan ba, kawai dai ban jidadin sabon shafin rayuwar lalata wacce ka budewa kanka"

"Itama zan daina da na yi aure"

"Har sai ka yi aure Sadam?"

"To ya zan yi ai kasan ba zan zauna ima cutar da kaina ba, ba zan iya hade kwadayi a yanzu ba i can't"

"Amman kara ka daina tun wuri domin idan ya zame maka jiki ba zaka iya dainawa ba ko da kana da auren ne, kazo kana wasan boya da matarka"

Har Sadam ya bude baki zai yi magana sai yaji wata murya a bayansa tana masa sallama cikin tattausan lafazi.

"Assalamu Alaikum"

Waiyowa tai ya kalleta a lokacin da yake daf da kai hannu ya tura gate din gidansa. Kyakkyawar budurwa sanye da uniform din makarantar Babus Salam wato islamiyar da ya soma karantarwa. Littafin dake hannunta ta mika masa.

"Ga littafin ka daka baro"

Sai da ya kalli Littafin sannan ya kalleta ya ce

"Ba nawa ba ne"

"Amman inda ka zauna ka bar shi"

"Ba nawa ba ne, ban je da littafi ba a nan ma tarar da shi maybe na wani ne cikin malaman"

"Okay yi hakuri na tsayarda kai"

Dan murmushi yai mata kadan ya juya ya tura gate din ya shiga yana maida wayar akunnensa

"Da wa kake magana?"

"Ina ruwanka.. Kaji mutum da gulma"

"A'a wai naji idan ka samu sai mu fara shirin aurar da kai"

"Wannan Daliba ce but to be honest, akwai wata yarinya da nake so"

"Da gaske?a ina take?"

"A nan take, ban san miyasa nake son ta ba, kawai dai abunda na sani ina sonta sosai kuma ina jin nishadi da farinciki idan na ganta, kiriniyarta na burgeni..."

Ya fada yana murmushi idanuwansa na ayyana masa sifofin Zinneera.

"Mashallah haka na ke son ji, da alama kuma kana son ta sosai"

"Yes Sadiq ina sonta sosai, zan iya yin komai dan na mallaketa, amman abun ya zo gidan sauki domin yar'uwata ce"

"Wow hakan yai kyau, u can't wait to see her"

"Yes amman fa bata san ina sonta ba"

"Amman ai ya kamata ta sani na san ba zata yi rejecting naka ba"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now