50 End

2.5K 305 93
                                    

Iyakar abunda zai yi a yanzu shine rumgumar kaddarar zama da Ummi a matsayin matarsa duk kuwa da kasancewar idan ya kalleta sai ya ji babu dadi amman a hakan ya rike matarsa suka soma shimfida kyakkyawar rayuwar da be taba mafarkin zai iya yinta da Bazawara mai yaya biyu ba. Yau kimanin wata bakwai kenan da aurensu amman har gobe yana jin kishi da bakinciki idan tana waya da yayanta ko kuma suka kawo mata ziyara a gidan. Yana ta jin cewar da ma Zinneera ce ita din da bata ma taba haihuwa ba sai dai ace ba budurwa ba ce, yana jin kewar masoyiya Zinneera, irin rayuwar daya tsara zai yi da ita ta zama labari and the most painful part is tana auren Sadam tana zaune cikin farinciki kamar ba ita ba, duk lokacin daya tuna hana sai ya ji kamar ya hadiye zuciya ya mutu. Da taimakon Ummi da jajirwata ya soma azumin wata biyu a jare har ya gama, be zata zai iya rayuwa mai sauki da Ummi kamar haka ba, macecec mai addini sosai duk kuwa da irin gatan data tashi cikinsa be saka ta watsar da addininta da rumgumi rayuwar turawa ba.
Mahaifinta da kansa ya nemi canjawa Sadiq aiki daga state zuwa federal, kuma aka sama masa aiki babba, irin karancin da Ummi tai masa ita da mahaifinta sai suka daure shi daga yin duk wani unkuri daya shafi maganar karin aure. Suna da wata biyu da tarewa a sabon gidansa police suka kai masa samame wai suna zarginsa da aje makamai a gidansa, a can suka tafi da shi aka tsare shi ana ta bincike suka bincika iya bincikensu ba su samu komai a gidan ba, shi kuma be yarda da nuna komai ba, kowa fadin yake shairin makiya ne, babu wanda yasan gaskiya sai shi da Ummi da kuma Sadam daya samu labarin abunda ya faru.

ZINNEERA POV.

Tun da cikinta ya Shiga watan na takwas suka fara shirye-shiryen barin kasar duk da kasancewar ita din bata so hakan ba, amman Sadam ya dage kai da fata sai sunje gani yake kamar idan aka je can din wata kila zata iya haihuwa da kanta ba sai an mata theater ba. Har Kaduna ya kaita suka gaisa da Hajiya Karima kuma sukai bankwana sannan ya dawo da ita nan suka karasa wasu shirye shiyensu, tana ji tana gani suka bar kasar gashi anata shirye shiyen bikin Suraiya a watan. A jirki tai ta bachi har suka isa bata sani ba, sai da ya tasheta haka ta fito da tulelen cikinta da tana sanye da abaya.

"Wa zai zo daukar mu?"

"Ba wanda zai zo daukar mu texi za mu shiga"

"Har ina?"

Ta yi masa tsaye tana bata fuska.

"Da mun fita harabar Airport din za mu samu"

"Akwai nisa?"

"Ba ni sa"

Ta kara bata fuska kamar ta fasa kuka, haushinsa take ta ji yanzu daman tun da cikin ya tsura ta rika jin haushisa ba tare daya mata komai ba, balle yanzu kuma daya hanata zama a gida har a gama biki. Shi ke tura kayansu ita kuma tana lafiya akadan kadan har suka fito daga hall din. Shi ya tari texi din ya bude mata ta shiga sannan aka saka kayana na baya shima ya shiga mai texi din yaja mota. Yau a kirjinsa ta kwana kamar dai yadda suke a gida duk rashin jindadin zuwan da take garin sai ta wayance a lokacin da take duba yadda gidan da kuma unguwar da suka sauka take. Wannan karon shi yai bachin gajiya ita kuma ta hada musu breakfast domin ta samu komai a cikin kitchen din, daga abincin kasar har irin wanda zata iya sarrafawa ta ci na Nigeria. Tana ta zumudin sabon gida, gashi ko'ina glass door ne gwanin sha'awa. Tana tsaye a window falon tana kallon yadda wata baturiya ke wasa da kare taji an rumgume ta baya.

"Ya akai kikai saurin tashi?"

"To ban gaji kamar kai ba"

"Saboda dai jiya ban baki aiki kamar na kullum ba ko? Na tausaya miki ne naga mun yi tafiya shiyasa na daga miki kafa"

"Ai abun ne ma na daga kafa ne?"

"Yes kisan duty ne ai"

Ta yi dariya tana juyowa ta kalleshi sai ya dora hannayensa kan wuyanta.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now