MATAR SADIQ*
*Na fertymerh xarah*
*61 to 70*
Suna fita part din motarsa ya nufa da ita,ya sanyata gidan gaba kana ya xagaya hr lokacin dukan qofar take tana kuka
umma banso,ni banso baxanjeba,bai kulataba ya tayarda motar ya fita gidan ganin sun dauki hanya ya sanyata yin shiru ta sanya hannunta a baki hade da langabar da kai tana kallon hanya...
ya juyo yana kallonta kafin ya maida hankalinsa gun tuqin da yake,yarinyar tana matuqar kyau da shan hannu,baisan meyasa duk abinda tayiba yake mata kyau....yayi parking din motar ya fita, tana xaune hannunta a baki tana kallonsa ya fice bai jima ba yafito dauke da kaya ninke ya bude bayan motar ya sanya kana ya qara shiga ya dauko wasu kayan duk tana kallonsa sai da yagama jide kayan saanan ya shiga motar ya tayar
ta cire hannunta daga bakinta bayan ta juya tana kallon kayan daya xube bayan motar can ta tsinkayo sabuwar game new design ba irin wadda tasani bace ta dubeshi da murmushi karo na farko cikin jindadi
tace game ditace yaya? ya gyada kai yana kallonta, ta tashi ta haura baya tana dariya sai yaji dadi a ransa ganin tasaki ranta ta soma bude kayan tedys ne kala kala da kayan wasa ta tashi tsaye hade da sunkuyowa tana kallonsa
tace duka wancan kaya nawane?ya gyada kansa
tace tor waye ya baka kudi?
yace Allah
tayi shiru tana kallonsa kafin ta qara xauna tana kallon kayansanda suka iso gidan ya fito hade da daukarta da hannu yayi alamar su jido kayan xuwa cikin gida, tana ganin sojoji ta qanqameshi,baisan daliliba amma yayi mamakin boye fuskarta a qirjinsa a falo ya sauketa ta soma tsalle tana kiran mama da gudu ta haura sama tana kiranta
cikin lokaci qanqani ya hada mata komai kana ya fita.
*
washe gari ya kasance monday talatu ta shiryata saboda skul ta fito da ita tana goye da skulbag dinta yayin da talatu ke riqe da foodflask dinta suka nufi mota, tana ganin soja ya nufi motar ta cire hannunta daga bakinta ta qanqame talatu hadd da fashewa da kukamama bana son shi banaso yakaini pls kice ya tafiyarsa ke xaki kaini,
tace amma kinsan bn iya mota ba
tayi shiru idanunta hr sunyi jawur, talatu tace ikon Allah ta dago tana kallon sojan yace wai meyasa bata son nayi driving
tace tana tsoron soja tun fil'azal haka take.
ya bude baki da mamakiyace tor ya takeyi da yayanta oga
talatu ta tabe baki inaji bata taba ganinsa a cikin uniform dinsa bane shiyasa, taja hannunta xomuje mushiga taxi karkiyi late, suka fice yabi yarinyar da kallon mamaki wannan fa sangartacciyace wlhy ba wani yarinta mtsew.
Washe gari ma sunfito suna niyar fita saiga sadiq ya fito cikin shirinsa na uniform xuhura na bayansa, nan da nan duka sojojin gidan na taru gabansa
cikin muryarsa marar sauti ya kira talatu dake neman fita
yace ina zakuje haka?
sai alokacin ummy ta lura da yawan sojojin dake tsaye gurin, nan da nan ta rikice tayi hanyar part dinsu tana ihu abinda ya janyo hankali sadiq gareta da mamaki ya baiwa xuhura cap dinsa ya bi bayantatana shiga falo yana shigowa cikin tsoro ta juyo taga kowaye suka hada ido,cikin tsananin tsoro da firgice dan bata taba ganinsa in uniform ba ta soma ja da baya idanunta a rufe bata son ganinsa tana juya hannuwanta
_pls yaya..pls dont touch me plssss_
yanda take kuka abin yabashi tsoro da mamaki tor meke damuntane ko tanada matsalar aljannu ganin xata fadawa dianing table batare da tasaniba yasa yayi saurin tarota ta fada qirjinsa dai dai lokacin talatu ta shigo
kabarta sadiq kada ka tabata,bai kula talatu ba ya dago ummy yana kallonta tuni numfashinta ya dauke,a razane yake kallon talatu kafin ya maida kallonsa da ummy dake kwance ragwaf a jikinsa hankalinsa yayi matuqar tashi
yace bata numfashi talatu,meke faruwa?
da sauri ta cillar da kayan dake hannunta ta karbi ummy hannunsa tana jijjigata
[9:21AM, 7/11/2016] Pherty馃帳馃懐: Yace wai menene meke damuntane meya ruda ta haka,talatu tace ina zuwa kajirani anan ta haura da ummy sama, saman gado ta kwantar da ita kafin ta shiga toilet ta debo ruwa a cup tazo tana shafa mata a fuska
ta dauki kusan minti biyar kafin tasamu numfashinta ya dawo amma a firgice ta tashi tana ganin talatu ta qanqameta,tace kiyi shiru suna waje da sunji kukanki xasu shigo su tafi dake
nan da nan ta sanya hannunta a baki ta rumtse idanunta tana hawaye talatu na shafa mata baya hrta samu tayi barci ta ajiyeta
tana saukowa ta sameshi nan falon sai safa da marwa yake cike da tunani iri iri
tace baka tafiba sadiq? batare da ya amsa tmbyrtaba
yace kigayamin meke damun ummy talatu?tace meke damunta ko illah tsoro,kai bakasan tana tsoron soja bane,ganinkune ya firgitata musamman ma kaida takeda kusanci dakai bata taba ganinka a uniform ba inaji shine ya qara firgitata
da mamaki yake kallonta
yace tana tsoron soja meyasa?
tace Allah ne yasan gaibu,ya jinjina kansa kawai
yace toh fa matar soja na tsoron sojane ikon Allah
tace karka tsaya mamaki katafi office karkayi late,yayi murmushi ya fice hr yaje office abin na bashi mamaki da tunaninta ya yini yau hr ya dawo gida, inda zuhura ya shiga uniform kawai ya cire ya zura jallabiya ko wanka baiyiba yana son ganin ummy a ynxu ta zamemasa wani bangare na xuciyarsa bai iya zama batare da itaba yana son shagwabarta da yarintarta, xuhura tabishi da kallon mamaki tana harararsa itadai ta rasa gane masa tsakaninsa da yarinyarnan,ita ko amaryar hr yau bata saniba, gab da zai fita falon taja dogon tsaki bai juyoba ya fice yana murmushinsatun kafin ya shiga falonsu yake jiyo ihunta tana dariya sosai da sauri ya shiga ya sameta zaune qasan carpet tana buga game ta tseren motoci sai dariya take,tanajin sallamarsa ta tashi a firgice ta juyo tana kallonsa a tsorace
yace menene haka,shine yau baki ganniba kuma baki nemeni ba,
ta make kafadarta tana neman hanyar tserewa,ya gane nufinta yayi saurin riqo hannunta jikinta ya fara rawa ya zauna yana kallonta_have i done something wrong?_ ta gyada kai tana qoqarin kwace hannunta daga riqon da yayi mata
yace tor tsaya kigayamin menene,inba haka ba xamu fada kuma baxan sake fita dake ba sannan xan dauke game din danasiyo maki naje na kyautar...
ta soma share hawayen fuskarta
yace tor gayamin,ya zaunar da ita kan qafafunsa ke nake saurare
da kyar ta tsaida hawayenta tana kallonsa da manyan idanuwanta
tace _ar u a soldier_
yace _nooooo am not_waya gayamaki haka
tace _but i saw u in uniform today_
yace _not me ummy,its a dream_ kinyi mafarkine,
tayi shiru ta tsura masa ido alamar bata gamsu ba ya ajiyeta ya tashi yana fadin bara naje nayi wanka ummy
tace yaya xnje,
yace shikenan,
ta dauki pringles dinta tabi bayansa suka nufi part din xuhura tana zaune falo ranta a baceya dubeta shima fuskarsa a daure
yace madam xnyi wanka ko xaa taimakamin? batare da tayi mgn ba tashi fuuuu tayi cikin dakinta,yabita da kallo kafin ya juyo ga ummy
yace kizauna anan kijirani kada kije ko ina kinji, ta gyada kai tana kallon t.v ya ficeshiru bataga fitowarsuba sai tatashi tabi dakinda taga sun shiga ta zauna bakin gadon tana kallon yanayin dakin,cikin toilet taji motsinsu suna dariya suna wasa da ruwa ta tashi hrxataje sai kuma tadawo ta zauna tana cigaba da cin pringles dinta
tana nan xaune suka fito dukansu daure da towel ya rungumo xuhura a jikinsa bai taba tunanin xata shigo dakinba gabansa yayi mummunan faduwa lokacin da suka hada ido da ita
tsananin mamaki yasanya ummi bude bakinta hade da kai hannunta a bakinta tana fadin
lahhh ashema yan iskane.....!馃檴