81-90

7.1K 288 1
                                    

Sanda suka shigo da sauri wasu sukayi kanshi wasu sukayi cikin gidan binciken abinda k faruwa

xuhura na tsaye hannunta aka sai hawaye ke kwanrowa a idanunta fadi take nashiga uku

suka kamashi suka fito dashi hr lokacin ummy na qanqame dashi taqi sakinsa yanayinta ma xai nunama a rude take tunda yau gata acikin sojoji amma bata tsorataba

sanda aka sanyashi mota ummy ta zagaya xata shiga motar taji wani furucin xuhura datace yau na bani na illata mijina da kaina *subutar bakine*

ta shiga motar aka fita dashi da sauri anan sauran sojojin suka shiga cikin gidan suna bincike sosai wai ko wani ya shigo tawata hanya yayiwa yallabai wannan rauni

captain jabir yace madam wai ya haka ta faru ko barayi suka shigo gidanne?

tayi shiru hade da xamewa nan qasa ta xauna dirshan hannunta daya akan kanta tana kuka sosai dai dai lokacin sojojin na qaraso

sukace bamuga wata alamar an hauro bafa akwai dai dalili ajira yallabai Allah yasa ciwonsa bayada nasaba da aikinmu

suka amsa da amin lokaci daya duk jikinsu a sanyaye......

Sanda suka isa asibiti hr lokacin tana maqale a jikinsa aka nufi *trauma accident an emergency* dashi, shigarsu keda wuya Dr.Merah ya shigo duba wani friend dinsa danayi accident jiya hanyarsa ta kaduna, suna hada ido da sadiq suka nufi juna cikin tsananin mamaki da farinciki suka rungume juna batare da maina merah ya damu da jinin dake xuba goshin sadiq ba

cikin murmushi yace long time, ashe akwai rabon xamu hadu

sadiq ya dafe goshinsa cikin qarfin hali
yace ikon Allah kenan prince, ina sarautarmu

maina ya tintsire da dariya ya juya yana kallon fadawansa

yace _a friend indeed_
ku gaida best friend dina a skul sanda muna pheonix bayan bilal

lokaci daya duk suka zube qasa suna kwasar gaisuwa, sadiq ya jinjina hr ynxu mulki da qasaitar tana nan ashe....tunaninsa ya katse lokacin da yaji ummy na cewa abokin yaya ni baxasu gaidaniba nima *matar sadiq* ce

duk suka tuntsire da dariya hr fadawan kai tsaye merah ya tsura mata ido kafin ya maida kallonsa ga sadiq

yace qanwarka x beautiful,inason kalar fatarta chocolate

sadiq yayi jim kafin yace yau kaizaka dubani kenan wannan raunin xafi yakemin sosai

merah ya yatsina fuska yana kallonsa
yace _sorry as i can see_ yana damunka zomuje likita ya dubaka kasan _my own is based on *cardiothoraxic*_

suna tafe suna hirar yaushe gamo hr suka iso inda likitan, ganin dr.merah da kansa yasa likitan yayi gaggawar amsarsa kai tsaye suka fara yimasa dressing hrda dinki sai da suka masa likitan na mamakin ko miye ya shige masa a goshi tabbas mai tsinine ganin ynda wurin yayi xurfi

duk inda likitan yayi ummy na biye dashi
tace dr. shi wannan me akeyi dashi, waye ya koyama allura,amma baxakayiwa yaya alluraba ko?sai dai anti xuhura _she x a wicked woman i hate her_ lokaci daya duk suka juyo suna kallonta cike da mamaki

likitan yace wacece xuhura ummy? hr yasan sunanta lokaci daya

tace matar yayace, tana dukana kuma tajiwa yaya ciwo

cikin tsananin mamaki da faduwar gaba
yace waye ya gayamiki xamewa nayi na fadi

tace but yaya meyas..........ya katseta cikin hanzari

_shut up ummy_ banason wannan surutun

hr lokacin merah bai tankaba yadai xuba mata narkakkun idanuwansa yarinyar tayi matuqar birgeshi

yace sadiq kabani aron ummy injewa affiya da ita _i knw she will be happy with sultan_

kafin sadiq yayi mgn tayi saurin make kafadarta hade da fadawa jikin sadiq

ni bazanjeba yaya
yace tor shikenan....ta dago tana kallon merah
tace abokin yaya xaka koyamin likita in gyarawa momina qafafunta, ingyarawa talatu teeth dinta danayi baqi sannan in dinkewa umma bakinta ta daina fada

gabaki daya office din na dauki dariya, merah ji yake kamar ya saceta, ynda take mgnr cikin kalar tausayima abin dariyane _cos she mean it da gske takeyi_

sanda akagama dressing din likitan hr mota ya rakasu shida merah badan komai ba sai dan ummy hr fadawan sunji dadin xama da ita, suna shiga motar ta kwanto a jikinsa hade da sanya hannunta abakinta tana sha ya sunkuyo ta kunnanta yace menene merah ya gayamiki a kunne

tayi murmushi _wai yace he lyks my childish_ yaya meyake nufi?kuma shine yasanyamin wannan xoben馃拲

ya cire xoben a yatsanta fuskarsa ba walwala yace kibari xn ajiyemaki kada talatu ta karba

ta jinjina kanta tana kallonsa kafin ta sanya hannunta a baki ta kwanta a qirjinsa...

kusan awa biyu sukaji kukan jiniyar motarsu da sauri aka hangame gate din tun kafin isowarsu, tashin xuhura yayi dai dai da shigowarsu, anayin parking duk suka qaraso suka bude motar sunayimasa sannu

sanda suka riqosa xasu nufi part din xuhura da hannu ya nuna masa part dinsu ummy kai tsaye suka wuce dashi

talatu na zaune taga shigowarsu dashi ta miqe tana salallami sai fadi take subhannallah meya samesa
[5:21PM, 7/14/2016] Pherty馃帳馃懐: sojojin sukace muma haka muka sameshi

yallabai me ya faru ne? akwai matsala idan oga yaji xaiga kamar bamu aikinmune hr aka shigo akayima wannan illar

sadiq ya dafe kansa
yace karku damu xamewa nayi na fad....kafin ya qarasa ummy ta tashi taja baya tana fadin

lah馃檴 yaya yayi qarya, a islamiya malam yace qarya na daya daga cikin alamomin munafiki

duk suka zuba mata ido, gabansa na faduwa yake kallonta cikin mamaki

yace nine nayi qarya ummy? kenan ni munafikine?

tayi shiru ta dauki tedy dinta ta haura sama tana waiwayensa sai da tayi nisa
tace yayaaaa, ya juyo yana kallonta
yace karkice komai pls ummy jeki kawai, ya kalli sojojin yace idan ta qara mgn ku kamata ku daureta, duk suka amsa da yes sir cikin murmushi tanajin haka tasha jinin jikinta tsoronsu yadawo jikinta tayi shiru tana kallonsu

yace su fice yanaso ya huta,kai tsaye suka sara suka fice,talatu tace meke faruwa saddiku meya sameka haka

yace wlhy xuhura ce duk saboda ummy

tace amma ko anyi yar banxa,so tayi ta illatakane kome?amma batayi hankaliba anan,

ummy dake tsaye tanaji ta sauko hannunta aqugunta
tace yaya meta jima ciwo dashi
yace kije ki xauna,wai meyasa bakyajin mgn ne ina ruwanki,

ta zauna gefensa ta daga kai alamar tunani馃ya zuba mata idanu yana kallonta kartaje ta caba masa wata mgnr
yace karkiyi mgn pls ummy banaso
tunani take a duk sanda suke kallo da faruq india film tana ganin boss na kashe mutane shima ana kashe shi,kenan duk mutum yajima wani ciwo shima sai anjimasa tunda tana gani a film in hakane xata ramawa yayanta tunda anti xuhura taxama boss itama mai qarfice,ta dubi hannunta馃挭馃徑tanada qarfi xata ramawa yayanta

ikon Allah ya kamasu basusan metake tunaniba kuma basusan dalilin ta na tayarda hannuntaba gani kawai sukayi ta tashi ta fita hr lokacin xuhura bata shiga sashentaba abin duniya duk ya isheta

ummy tayi tsaye gabanta hade da dora duka hannayenta a qugunta ta daure fuska kamar yadda taga sunayi a film, ta kira sunanta anti xuhura

xuhura ta dubeta da mamaki,bata ankaraba sai jin dutse tayi a goshinta gap, aikuwa xuhura ta saki qara

ummy ta juya xata fice saiga sojoji da gudu dauke da bindigarsu,tuni hr sadiq yafito dafe da goshinsa.......

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now