Ina gamawa na kora da ruwa mara sanyi, sannan na goge jiki na, na nufo kitchen in da na tabbatar zan samu Ammi.

Kai tsaye dinning table na nufa ina murmushi na kai hannu zan yanki red velvet cake mai chocolate a sama, wanda ya kasance favourite ɗina sai naji an chapke min hannu ɗuk da ban ɗaga kai ba na san Ammi ce.

*Anam*!!!!!!!

Nayi mata murmushi ina daɗa kai ɗayan hannun na yanka nayi saurin lunkumawa a baki ina dariyar samun nasara, yayin da nake kokarin guduwa kenan, Ammi kuma na dariya tana biyoni sai muka ji karar buɗe kofa..mamaki ya sani sake baki ganin Abhi tsaye da kayan tsaraba anyi rapping ɗin su niki niki a hannu.

Na buɗe baki chike da murna na ce,"Ammi look Abhiiiiii!! na faɗi hakan amma ban san lokacin dana ruga na rungume sa ba kawai jina nayi kwance a jikin sa ina daɗa yi masa shagwaɓa tamkar dai yar goye, ɗabi,'a tace hakan.

Daga bisani muka ci abinci, we catch alot of fun that very day sannan muka fita cikin garin turkiyya domin shakatawa.....a wannan lokacin Abhi yayi mana good 2month kafin wata ranar asabar naji suna having misunderstanding tsakanin Ammi da Abhi, if i could remember i heard Ammi was saying that, She want's to go meet his parents and siblings in Nigeria, She want them to know that two of us exist in Abhi's life, Abhi says no, not now, that she should wait for the right time, but all of the sudden they quarrel both of them.....daga baya kuma sai naji shiru Ammi na kuka, Abhi kuma na bata hakuri...na koma ɗaki na ina ta tunanin meyasa Abhi baya son muje Nigeria?

"Let all get to the point readers by starting with introducing my self to you"

Suna na
*SA'ADATU SULAIMAN* Inkiya ta kuma *Anam*

Ni haifaffiyar ƙasar turkiyya ce, asalina kuma ƴar ƙasar najeriya ce cikin karamar hukumar Daura cikin jahar Katsina.

Shekaru na 18 cur da haihuwa *Yes am just 18* very young, Ni ɗin fara ce amma ba sol ba kasancewar na ɗauko hasken fatan Ammi dana Abhi, mai kyau baya yaba kyan sa, sai dai dayawa mutane suna yaba, baiwa, kyau da suran da Allah yayi min. Nayi makarantar islamiyyah na sauke alqur'ani da littatafai da dama sannan nayi makaratar boko in da na gama secondary school ɗina cikin kwanciyar hankali, karatun degree ɗina kuma Culinary Institution of America, in da nake karatun zama kwararriyar *CHEF* tsara girke girke wanda salo na ne hakan shiyasa na zama kwararriya a fannin *Culinary Art* inda nake final year ɗina, kar kuyi mamaki saboda an sani a school da wuri, duba da yanda nake mai da hankali a school promotion ɗina sau ukku gashi ya zame min alkhairi tun d zan gama school at my teenage year old.

Kar ku man ta kuma ina da karamin class wanda akwai page ɗina ma a instagram mai suna *Cook with Anam Academy* ina koyar da girki kala da iri fannin girkin Chinese,korean, American, Sudanese, Nijar, Mali, Kenya, Ghana,Uganda, India, da kuma ƙasar turkiyya da sauran kasashe daban daban, , ɓangaren Snacks, grilled chicken and grilled fish, haɗin coffee mai kyau da daɗin ɗanɗano, cake, birthday cake da sauran abubuwa babu abin da ban iya ba, Yayin da na zake dantse ina koyan girkin Nigeria wanda sai na yi research a ɓangaren tribe kafin na ke sanin yadda ko wani yare suke girka best food ɗin su...

Bana manta Abhi ya kan zo mana da KUKA da KUƁEWA har da wani black spices wai Daddawan kalwa...lol, all powdered , ya ce wai Kakan shi ce ta haɗa masa wai ya samu wacce ta iya girki ta rinka sarrafa mi shi, Da fari ni da Ammi duk bama so, amma daga bisani dana kware wajan girki da su har da spices na gargajiya sai ya zamana da duk zuwan Abhi nijeriya sai na sashi ya taho min da su.

Ɗabi'u na sun banbanta da halayyan ƴan ƙasar turkiyyah kasancewar ni mace ce wacce bata son hayaniya, mace mai natsuwa da kamala.....idan nace hallayyah ina nufin shigar su.

Wasu daga cikin ƴan matan kasar suna shigan banza kuma halayyan su kenan, wasu kuma ɗabi'ar su ce su sanya kananan kaya su fita amma basa harkar ban za.....likewise me ko wacce irin shiga ina yi kuma na fita amma bana halayyan ban za idan ban manta ba ko saurayi bani da shi kuma ban taɓa son wani ɗa namiji ba tun da Ammi ta haife ni na fara girma ni ban ga namijin da yake burge ni ba a duniyar nan, kawai ni rayuwa ta nake yi babu ne babu ne kawai.

To kunji na muku takaitaccen bayani a kai na.

______________________________________
NIGERIA
DAURA, KATSINA STATE
Gidan daurawa estate

Ɗaya daga cikin manya manyan gidajen dake cikin estate ɗin, gidan *Bishir* wanda ake ma lakabi da *Baban gida* baban kowa da kowa kenan... shine kuma wan Kakana.

Da alama kamar meeting suke kasancewar yadda gidan ya cika da ƴaƴa da jikoki kai har da tattaɓa kunne, kowa yana sha'anin sa, wani babban falon *Baban gida* wanda manya ne kaɗai a ciki.

Kaka na Mustapha wanda ake kira da *Baban Sulaiman* sai Baba Huraira, da Matayen su, sannan sai ƴaƴan su har da Mahaifi na (Sulaiman) da kanwar sa Salima wanda ita ma tayi aure tana da yara biyu...duk yaran ko ince jikokin suna waje kowa yana damuwan sa.

Baban gida yayi gyaran murya ya ce,"Mu buɗe taro da addu'a"

kowa ya ɗaga hannu alamar ana addu'a daga bisani suka shafa, Sai Baban gida ya kalli Kaka Mustapha ya ce,"Ɗan uwa bisimillah"

Kaka na wato Baban Sulaiman yayi gyaran murya ya ce,"Assalamu alaikum warahmatullah"

"Wa'alaikumus-salam warahmatullah" duk suka amsa masa sallamar sa.

Ya ce,"Alhamdulillah, muna godiya ga sarki Allah da kara bamu aran rai da aran lokaci har ya kai ga mun zagayo karshen wata muna wani meeting ɗin batare da mun rasa kowanne daga cikin agalin mu ba"....ya cigaba da cewa,"Nayi mamaki kwarai abin kuma yana cimin tuwo a kwarya wai ace har yanzu Sulaiman ka kasa fito mana da matar da zaka aura, duk cikin ƴan matan da muke dasu kace basu maka ba, sa'anninka duk sun yi aure gasu nan duk yaran su daga mai shekara ashirin da shida sai me shekaru kasa da haka, dayawa daga cikin yaran ma an aurar da su, amma ka gagara aure Sulaiman idan boko ne ka gama boko, ka gama duk tara kuɗin da kake so ka tara ka gina tsararran gida da babu irin sa a estate ɗinnan, har yau babu kowa a ciki, mun maka magana, mun koma mun zuba maka idanu, kullin sai kace mu baka lokaci" shi lokacin har yanzu bai yi ba, To ba ni kaɗai ba har ta sauran uyayen ka sun gaji da wannan ɗabi'ar taka.

Daga nan kuma Baban gida Ya ce,"Shawaran da zamu yanke Baban sulaiman, dama ga lubabatu kanwar Asma'u, ƴaƴan Baba huraira,....Lubabatu tun da Anas (Ɗan Baban gida) ya rasu bata sake aure ba tana zaune a gida....me zai hana a haɗa su aure da Sulaiman ɗin.

Charaf Lubabatu ta ce,"Kuyi hakuri Baba wallahi na tsaida mijin aure, Zakariyyah zan aura (Ɗa ga Baban gida)

Baban gida yayj caraf ya kalli Zakariyyah ya ce,"Wai haka?

Zakariyyah ya gyaɗa kai, yayin da matar sa *Salima* Kanwar Sulaiman idanuwan ta sukayi ja, za ai mata kishiya kishiyar ma kanwar kawar ta wato Asma'u ce kawar ta, lubabatu kuma kanwar Asma'u.

Baban gida ya cigaba da cewa ko ya kuka gani, kowa yayi na'am tun da Zakariyya da Luba sun aminta da juna, dama a tsarin al'adar nasu basa ma kowa auran dole, abin da yasa sukayi zaman nan saboda ƴaƴan su da suka rage basuyi aure ba, gashi jikoki suna ta aure, sai suke kokarin suka sun gyara abin tun daga kan manya kada yara yaran jikokin su fara kokarin rushe al'adar tasu.

Baban Sulaiman ya ce,"Sulaiman you are too old for that art, kabar yara yara suyi borin da kakeyi, idan zaka natsu ka je gidan Baban gida ku daidai ta sauran ƴan matan, kana jina, wallahi idan ka bijire min sai na saba maka, duk cikin ku nan na san kun san hukuncin da muka yanke ma Asma'u, yanzu ko da wasa bata isa ta taka kafar ta ta dawo cikin wannan zuri'ar ba.

Kai ma kuma ina mai tabbatar maka idan ka bijirewa al'adar mu to zan sallama ka Sulaiman, ka duba ka gani ka manyan ta shekara Arba'in da ɗori wasa ne?.....tashi ka bani waje.

Sulaiman ya tura baki, ya mike ya tashi yabar falon ranshi a bace, bai san tayaya zai fara sanar dasu cewa shi fa yana da zuri'a ƴar sa ma har ta isa aure...bai san ta yaya zai nuna musu cewa Ammi da Anam sun jima a cikin rayuwar sa ba, Ba zai yu ya cigaba da ɓoye truth ɗin sa ba is either ko ya faɗa wa ƴan uwan sa, ko kuma ya ɗauko su Ammi ya kawo su Nigeria duk abin da zai faru sai dai ya faru....don bai shirya zama da mata biyu ba, yana ganin idan yayi haka ya ci amanar Ammi tun da kullin tana rokon sa da ya kai ta Nigeria, kullin tana faɗa masa ya dena ɓoye ma iyayan sa cewa yayi aure saboda halin yau da kullin.

Alkalamin Diela📝
Wannan book ɗin free book ne bana kuɗi bane.

Comment please

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now