06

261 20 9
                                    

RAYUWAR JIDDAH
part 1/06
Mallakin DielaIbrahim

__________________

******Jiddah ta dubi Faisal tace Why Yaya Faisal?why did you let him go?
Am not happy with what you did right now, and don't talk to me anymore ta wuce da gudu....bin bayanta yayi cikin sauri yana kiransunanta amma taki tsayawa kuma taki amsawa har ta isa ward din.
Tana shiga ta haye gadon ta kwanta hade da kallon bango ta rufe idanunta momma nata magana amma shuru ba answer, cen sai ga Faisal ya shigo hankali atashe shima yana tayima Jiddah magana tayi masa banza, Momma tace Faisal meya faru ne?
Faisal ya zayyana wa Momma abinda ya faru yace Momma wlhy mutumin shine head na hospital dinnan tayaya zan iya kamashi, ki duba rigimar Jiddah fah,Momma please explain to her.
Ya samu chair ya zauna kusa da gadon ta yana facing dinta, hade da share zufan forehead dinsa ya cire hulan shi ya aje gefe guda yamaida kallon shi zuwa ga Jiddah, momma kuma ta fara kiran sunanta ahankali,tana yi mata kirarin da tasan Jiddah na so matuka tace Jiddah na, Autan Momma, Autan Ummi" Jiddah bata son momma na shiga damuwa saboda ita, hakan kuma duk yadda tai fushi idan taji wannan kirarin na momma to sai taji hankalinta ya kwanta juyowa tayi tace momma kada ki damu kinji ba laifinki bane,"momma tace noooooo Jiddah muna so mu fahimtar dake ne......Wace irin fahimta Momma? Ku saboda ba'a jikin ku ciwon yake ba shiyasa ta karashe tana hawaye Momma tai saurin rungumeta tana cewa nooo darling don't cry yi shuru kinji sai da Jiddah tayi mai isarta kafin tayi shuru tana kallon Faisal dayayi tagumi da hannu biyu ya tsura mata idanu, Veil dinta ta cire ta wurga masa tana hararanshi, tana cewa na rama abinda kamin.
Faisal da dariya ta kusan turnuke shi,amma yace Auchhhh my little girl da zafi fah yana sosa inda veil din ya taba afuskar shi.....Jiddah tace Allah ya kara kuma bazance maka sannu ba....."Faisal yace ayyahhhh ni Yayanki guda daya bazaki bani hakuri ba Jiddah.
Ta zumbure baki ta gyara kwanciyar datayi a jikin momma tana nuna kanta tana cewa ni Jiddah mai yayu dayawa kamanta inada "Yaya Muhammad" inada "Yaya saif" "Yaya Idris" "da kuma "Yaya Isma'il" ( Idris da Isma'il yaran Momma ne kuma sun girmi Faisal).....Jiddah ta kara sunne kanta a jikin momma tana masa gwalo,
Faisal da ya rikice a fuska yace nasan kina da yayu dayawa amma kin manta am your lovely Yaya Faisal....."Jiddah ta kalli sama hannun ta nakan cheeks dinta kaman mai tunani tace uhmmmmm hakane fah toh amna sai ka roki momma kafin nace na hakura sannan sai nabaka hakuri kaima......ai bata rufe baki ba ya kamacewa momma please  kishiga cikin maganar don Allah kice mata tayi hakuri ta yafe ma yayanta,.....Momma tace Autan momma, Autan Ummi ayi hakuri kinji.
Take wani murmushi ya subucewa fuskar Jiddah lokaci daya dimple guda daya dan karami ya lotsa, bakinta ya bude take kuma fararen hakwaranta suka bayyana to which kyawun fuskarta yadada fitowa dukda cewa bakar fata gareta amma maidan haske kadan kuma komai na fuskar mai kyaune batada muni ko kadan... Veil din ta amsa ta rufe kanta wanda ko kitso ma batayi ba tsabar tsayi da laushin suman ta.
Haka sukayita wasa da dariya tsakaninsu, tuni Jiddah ta manta da wani Hafiz, har Fatima tazo suka hadu suna ta hira abinsu.

*******

Tunda ya koma office kasa tabuka komai yayi, gabadaya yarinyar ta dagula masa lissafinsa, Shikam babu abinda yake mamaki game da ita sai da tace akamashi a kulle shi, and hardawani cewa uniform dinsa basa masa kyau,..Yayi deep breath sannan yace Allah yasani bana son tashin hankali ko kadan, wannan dalilin yasa bana shiga harkar mata, mazan ma da colleague dina kadai nake mu'amula, amma yarinyar nan tana son kure ni......uhmmmmm ya kuma jan dogon numfashi sannan ya daga wayarsa yayi dialing number Mom, firan da suka farayi shi ya cire mashi damuwar dayake ciki....hkanan lokaci daya shima yamanta da existence din Jiddah.
***************

*A week later*

Jiddah ta fara samun sauki hakannan aka ce ta ringa motsa hannunta kadan kadan.
"Sannan kuma su Abba da Ummi sunso zuwa dubata amma momma ta hana, tace kada su damu su bari idan ta samu sauki sai su zo su dubata.
a yau kuma Fatima tazo tana tuna mata cewa yau zasu ansa acceptance letter, don taje tun rannan akace ba'a gama ba shine suka basu 1week.
Fatima ta dubi Jiddah tace zaki iya kizo muje mu ansa.
Jiddah tace zan iya mana" ta dubi momma tace momma bari muje mu anso acceptance letter, momma ta gyada kai tace Allah ya bada sa'a
Ameen suka fita.
Ko da suka shiga bangaren lab din suka je office din Head of the lab anan ya sanar dasu cewa yakai letter din Admin Office and idan suka anso zasu kai office din commander yai masu signing, daganan sukayi godiya suka fita.
Admin suka je amma sai sojojin sukace musu su fita su shigo one after the other, hakan kuwa akayi inda Fatima ce ta fara shiga aka sallameta tayi signing a wani book sannan tafita Jiddah ta Shiga, tana Shiga ta gaidasu sannan ta fadi sunan ta aka fara duba mata, sai dai me bata san me suka gani ba taga kowa ya tashi tsaye ya kame kaman gunki, takai dubanta ga sauran ma wanda akalla sojojin office din zasu Kai goma amma gabadayansu saida suka tashi tsaye hade da kamewa waje guda ita ko mamaki yasa ta saurin kara waigawa sai taga ashe wani ne yashigo, sake kallon wanda yashigo tayi da mamaki ashe sojan nanne dai wanda ita fa har yau bata san sunanshi ba, ta tabe baki sannan ta kwashe da dariya wanda yasa hankalin kowa ya koma gareta, ta daura hannu daya mara ciwo a waist dinta tace wai dama saboda kai suka wani kame kaman wasu gunki haka, wayyoooo Allaha duniya akwai abubuwan ban mamaki, sannan kuma ta sake kwashewa dawani dariyan, wannan karan harda rike ciki, sai da tayi mai isarta sannan ta maida hankalinta ga matar dake dubamata nata Acceptance letter din tace don Allah jiba ki dawo normal ki bani acceptance letter na, nikam ina da abinyi....don ita Jiddah aganinta ba normal suke ba, taya daga ganin mutum zasu wani kame kaman sunga abin mutuwa........Ashe abinda bata sani ba shine Forces haka suke ma junansu akwai respect atsakanin su, dakuma nuna girmamawa ga wanda ya fisu rank.
Hafiz da ya tsura mata idanu shikam ayanzu gani yake kaman yarinyar tana da tabin hankali saboda abubuwan da takeyi kamar tabbaba haka yake gani. Amma bari yagwada wani abu yagani, hakan yasa ya dakatar da sojojin da suka fara yimata tsawa suna fadin ta fita waje kuma da frog jump zata fita, yace dasu cikin stop. Kallon ta yayi sosai wanda ita kanta Jiddah sai da ta tsorata da irin kallon dayayi mata, ganin ya fara takowa  izuwa inda take ahankali sai kuma ta fara ja da baya itama har takai bango shima dai bai tsaya ba harya zo inda take yana kallonta ido cikin ido, yadau akalla tsahon minti biyar baya ko kyaftawa haka zalika itama bata kyaftawa, sai asannan yadubi hannunta yace ahankali kamar mai rada yace ya hannun hope da sauki?
Jiddah ta kyafta idanunta mai dauke da natural eye lashes dinta dogaye kuma zara zara masuyi kaman tayi kuka,"don a school ma yawanci cewa akeyi ta Sanya lashes wanda itakuma bata biyewa masu fadan hakan"
Ta kyafta ahankali ta kuma bude sannan ta tsura masa ido itama ayayinda ta kasa furta komai Jin soft voice din da bata taba jin irin shi ba aduniya,amma tsabar tsoro da fargaban da suka shige ta awannan lokacin shi ya dameta. sauri tayi ta matsa awajan ta nufi table din matar tace please ki bani mana ta fada zuciyar ta na dukan uku uku jikinta kuwa sai bari yakeyi kodaga yanayin maganarta ma zaka gane hankalinta atashe yake Allah Allah take tabar office din, kuma tarasa dalili, tadai san ita ba tsoronshi takeyi ba, matar ta kalli Hafiz ta ido yayi mata alamar ta bata, sai ta mika mata Jiddah tayi signing sannan ta fice cikin sauri ko kallon Hafiz batayi ba.
Shikam dariya yai cikin ranshi yace so I got you, I got your weakness, sai dai sauran staffs din sukaga yana ta murmushi shikadai har suka gama abinda ya kawo su, ya fita....kai tsaye office dinshi ya nufi ayayinda yace ma sauran escort din su jirashi yayi mantuwa,yace bari ya dauko yazo hakan yasa ya tafi shi kadai yana Shiga corridor din office din anan ya iske su tsaye Fatima nata faman tambayan Jiddah me ya sameta ne jikinta yayi sanyi haka, wanda ita kuma jiddah ta kasa Fadi mata komai.
Ganin shi data sakeyi ne yasa ta kara zare idanu lokaci daya ta juya baya zuciyarta na dukan uku uku tarasa dalili, take ta soma tambayar zuciyarta ko miyasa take jin haka, Amma ta kasa samun answer runtse idanuwanta tayi tana addu'a Allah yasa yabar wajan, Allah yasa bazata Kara hada idanu dashi ba sai awanan lokacin ta fara addu'a Allah yasa ma bazata kara sashi a idanuwanta ba ahankali ta soma budewa at thesame time tana cewa ahankali Allah yasa bayanan.....saidai tana budewa ta daurasu akan fuskar Hafiz wanda yake dauke da killing smile ya tsura mata kyawawan idanunsa,
Lord! ta furta da karfi cikin siririyar muryar ta, kara matsowa yayi kusa da ita
sosai ita kuma ta daburce ta rasa abinyi,
Gira ya daga mata hade da cewa "Allah yasa bayanan kuma," waye ake Addu'a Allah yasa bayanan?

RAYUWAR JIDDAH ✔Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon