19

201 18 10
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/19
Mallakin DielaIbrahim

____________________________________
Mumbai
12:00pm

Dr.Rahul ya gama cirewa ya shafa mata wani abu kaman ruwa da wiper sannan yace pray before you open your eyes"
Jiddah ta hade hannayenta waje biyu ta fara addu'a adai dai lokacin aka turo kofar cikin sauri , to which duk suka waiga don ganin wanda ya shigo Amma Banda Jiddah"
Hafiz Abubakar ne ajiyar zuciya ya sauke mai karfi sannan ya taka zuwa inda sauran suke, batareda bata lokaci ba su Momma suka bashi waje ya zauna saman gadon da take yana facing dinta, Bayan ta gama addu'a ne, Dr. yace to bude ahankali I repeat very slowly please"
Ahankali ta soma bude idanun wanda ta soma ganin blurred, sannan ta fara gani daga bisani ta sauke su akan Hafiz Abubakar, sai ga vision dinta ya dawo tangaran take ganin Hafiz, Wanda ta tsura masa idanu kaman bata gani har saida Dr. yace Jiddah how far? Can you see?
Tana kallon Hafiz still sannan ta fara murmushi to which kana nan dimples dinta suka fito daga bisani fararan hakwaranta suka baiyyana, ahankali tace Alhamdulillah Momma, granny, Yayanah, ya muhammad and "Mi Alma" I can see again, Alhamdulillah!!!!!
"Who is "Mi Alma"?
"Or What is "Mi Alma"?🙄🤔who knows 🤷"

Momma ta rungume Jiddah saboda farin ciki, Jiddah tana ta kallon Yayanta da ida nuwansa sukai jajir to which guntun hawayen dayake boyewa ne suka diga a kuma tunsa, ahankali ta sauko ta dibi tissue paper ta share masa hawayen sannan tace Aa yayana farinciki zakayi Banda kuka bagashi Ina ganinka yanzu ba,
Faisal yayi murmushi yace Alhamdulillah Jiddah farin cikin ne yasani zubar da hawaye, am so happy da vision dinki ya dawo, Muhammad yace congrats lil sis, am also the most happiest person in whole world,
Granny tace MashaAllah Ina tayaki murna takwara Allah ya Kara maki lafiyar idanu.
Kowa ya amsa da amin, sai alokacin ta koma wajan Hafiz ta zauna tana kallon sa kaman wacce zata fadi abin kirki amma sai ta daure fuska tace Yaya Faisal fired him, tell him am angry with him"meyasa ya tafi ya barni bayan he is the cause of everything,and na fada mishi shi nake son na fara gani,shine ya tafi" ( niko nace Jiddah iyayen korafi da shagwaba an samu lafiyar ido dole shagwabar ta dawo, shi kuma Hafiz yaga ta kanshi komai yasamu Jiddah shine sila" shi kuma Faisal kullin sai ace shi zaiyi punishing Hafiz😂)
"Faisal yace ayyahhh Jiddah waya fada maki baya nan, tun dazu fah yake nan, mun boye maki ne saboda muna son muyi surprising dinki"
Jiddah ta kalli Momma alamar bata yadda ba tana son ta fada mata gaskiya, kamar kuwa "Momma ta gano ta tace Jiddah bana son rigima kinaji na oya kuzo mu fita mubar Dr.Rahul yayi aikinsa.
Duk suka fita, Dr. yayi murmushi ya fara aikin duba lafiyar idanun nata.

*****
Da yamma akayi discharging dinsu Momma tace ma Hafiz yaushe zasu koma Nigeria!
Hafiz yace gobe inshallah Momma!
"Momma tace okay toh zaku tafi dasu Muhammad sai muma amana booking flights.
Hafiz yace okay Allah ya kaimu Momma yai masu sai da safe sannan suka tafi da granny.
Ranar Jiddah kwana tayi tana jin shaukin soyayyah tana tunanin Hafiz aranta ta aiyyana bazata amsa masa cewa tana sonshi ba sai ta wana shi.
******
Hafiz kwance saman gadonsa shima yana tunanin Hauwa'u, Allah Allah yake ita ma ta furta masa tana sonsa, yace ko da bata sona nasan yadda zanyi na cusa mata soyayyah ta, Allah yakaimu Nigeria lafiya
Ni ko nace Ameeeeeeen ya rabbal alamin"
Ya tashi yana hada kayanshi waje guda ya daukk Sari da Pakistan din daya siya wa Leemarh don bai manta akawarinsu ba, yace in ban siya ba, bansan awani matsayi za'a ajeni idan na koma ba....ya karasa hada kayan sannan ya kwanta.
*******
Faisal bawan Allah yana kwance Muhammad na tausansa, yana bashi hakuri akan yabi komai ahankali ya dena damuwa kada ciwon zuciya ya kamashi"
Faisal yace Muhammad ahakan ma Ina godewa Allah saboda radadin soyayyar ta yana fita ahanakli, ban sani ba ko Dan na Sanya wa raina zanyi sacrificing love dinta"
Muhammad yace ka cigaba da hakuri Inshallah Allah zai baka wacce ta fita nan ba da dadewa ba.
Yace Allah yasa.
**********
The next day was a brand new day for Hauwa'u Junaid saboda jinta takeyi kaman yaune ta fara gani aduniya, for more than 2month Bata gani, lallai ta dandana wata rayuwar, ayanzu ta kara experiencing wani abu acikin rayuwarta, ahakan ma tana godewa Allah Daya sa ta fara gani, gashi dai sanadin soyayyar Hafiz ne amma dama komai zai faru da bawa akwai sanadi,toh shiyasa tun farko ta fawallawa Allah komai tasan shiya sanya mata makanta, Kuma gashi ya cire mata Alhamdulillah ta furta ahankali lolacin data ke kokarin yafa veil ta fita ta samu kowa afalo haka sukaita tsokanan ta, itama tana ramawa kasancewar ta bamai shariya akan magana ba, duk yadda kayi mata magana zata amsa sai dai if she isn't in the mood.
Hafiz ya kira Faisal yace zasu iya fitowa su samesu a airport saboda komai yazama ready,, sannan ya fada masu su ka kama hanyar airport.
Bayan sun isa airport ne suka kira Hafiz suna tambayar sa Ina yake, shi kuma yana musu kwatance,har suka zo inda yake,
Juyowa kawai yayi idanunsa suka sauka akan Hauwa'u tafiya take innocently ya dade da karantarta aduk lokacin da zaka hango ta tana tafiya alokacin zaga hango 💯 natsuwar Hauwa'u saboda bata kalle kalle, infact kanta da idanuwanta kasa suke kallo, Hafiz yai murmushi"
Ya mikawa su Faisal hannu suka gaisa ya gaida Momma" sannan ya kalli Jiddah wacce ta kawar da kanta gefe sai da tadau lokaci kafin tace Ina kwana Yaya Hafiz"tana yi tana hararar shi playfully ta gefen ido, ya gano ta sarai hakan yasa yai murmushi ya girgiza kai sannan yace Lafiya lau Autan Momma,kin tashi lafiya?
Ta gyada kai tana watsa da yatsun hannunta"
Yace to Masha Allah"
Suna nan zaune a reception aka fara kiran suna har aka zo kansu duk suka shiga, kowa ya samu seat, seat din granny da Momma daya, sai su faisal sannan kujerar Jiddah, ta zauna tana cewa yauwa nikadai ne a roll Dina, tana yiwa Yaya Faisal gwaliyooo 😛
Faisal ya kalle ta unbelievable how on Earth zata zauna a waje ita daya, sai kace jirgin babanta 🙄 ya make dariyar shi ganin yadda ta zauna very balanced, juyawa yayi bai ce mata komai ba bayan kowa ya gama shiga ne sai ga Hafiz ya taho yana cewa kusanya seat belt dinku, ya ajiye bag dinshi a sama daidai kujeran Jiddah, Yana dukar dakai ya ga yarinya ta zauna tayi balance😂 gyaran murya yayi yace, Hauwa'u dan gyara na zauna"
Wani irin kallo 🤔tai masa sannan tace bani kadai bace anan?
Hafiz ya girgiza kai yace No
Jiddah ta zumbure bakin ta kama kunkuni ita meyasa za'a sanya mata wani ya matse ta"
Hafiz kallon mamaki kawai yake mata aranshi yace Ashe dai old Jiddah ce 😂  har yanzu fah bata canja ba, murmushi yayi sannan ya soma kokarin zama bayan ta matsa.
Yana zama tana tashi, tace wait wai kai zaka zauna daman"?
"Yes nine"ya bata amsa atakaice"
Jiddah ta kumbura fuska tace Yaya Muhammad dawo nan, ni zan zauna da Yaya Faisal"
Amma sam Muhammad yace bata isa ba dole awajan zata zauna ya juya yace wa Hafiz, na baka amanar lil sis"Hafiz ya gyada kai yana murmushi yace inshallah zan rike amana" ta juya ta fadawa Momma"
"Momma tace kinga Jiddah bana son rigima fah, kizauna awajan please bamu da lokaci kinga suna shirin kunna jirgin.
Hakanan drama queen 😉 ta zauna tana hararar sa, ta zaro belt zata sanya ta kasa, yana kallonta, sai ya sanya hannunshi ya janyo belt din to which garin janyowa fuskarsu suka hadu suna jin numfashin juna, sun jima suna kallon kallo kafin da kyar ya sanya belt din ya koma ya zauna..
Jirgin ya soma tashi Jiddah ta rufe idanuwanta to which bata San yadda akai ta kama hannayen Hafiz ta rike ba har sai da Jirgin ya daidaita kafin ta dawo cikin hayyacinta.....tayi saurin dauke hannayenta acikin nashi suka hada ido, sai kawai ta galla masa harara har da murguda masa baki, Sosai abinda takeyi yake burgeshi, ya rasa meyasa baya ganin laifinta ko kadan, bai cemata kala ba, juyawa yayi ya cigaba da game a wayarsa.
Karfe hudu 4pm jirgin ya sauka a  birnin tarayyah Abuja, Hafiz ya juya zai tafi, ai charaf ta kama kasan rigarshi, tayi da fuska kaman me shirin yin kuka, tace kaman ya muhammad yace ya baka amana"kuma shine zaka wuce ka barni😪
Hafiz ya dafe kanshi yace am so sorry don't cry ba tafiya zanyi ba, zanje na aje bag dinane"
Jiddah tace toh ka cire min belt din sai mu tafi tare"
Haka ya cire mata sannan ta bi bayanshi suka fita tare, awaje suka samu su Momma suna jiransu.
Muhammad yace Momma why not muje kaduna kawai in yaso su Ummi sai suzo kadunan.
Momma No kiramin Abba.
Aka kira mata Abba, sai da suka gaisa tai mishi albishir sannan tace zasu wuce kaduna kawai, Abba yace ba damuwa suje kadunan suma zasu zo gobe inshallah,
"Momma tace to Allah ya kaimu
Ameen Abba ya amsa sannan yace abawa Jiddah wayar, ana bata ta fara hira dashi tana masa shagwaba iri iri har suka gaisa da Ummi da Ammi da Mama.
Suka samu motoci guda biyu suka hau Jiddah tana motar su Hafiz da Muhammad, basu wani jima ba suka iso kaduna har gida su granny suka raka su sannan suma suka tafi gwamna road.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now