18

171 17 6
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/18
Mallakin DielaIbrahim

___________________________________
India-Mumbai

Da sallama ya shiga dakin,bayan ya tura kofar idanuwansa suka sauka akan Jiddah wacce take kwance an rufe mata idanu da bandage,kamar dai mai bacci ya dade awajan tsaye saallaman sa biyu amma ba answer, hakan yasa ya nufi wajan straight ya samu kujera ya zauna ahankali ya sanya hannunta cikin nashi ya matsa kadan, to which sai da tayi motsi amma batayi magana ba.
"Hafiz yace HAUWA'U  I missed you, nayi missing masifar ki, nayi missing surutun ki da tsiwarki, Hauwa'u I totally missed everything about you, I have no clue on how or when I fall in love with you, I just found my self deeply inside it, Hauwa'u from the very first day I set my eyes on you nagane cewa "YOU ARE THE LADY I'VE BEEN SEARCHING FOR" sai kuma yayi shuru na dan second kafin yace ranar dana yi inviting dinki I actually waited for you so long ban bar wajan ba sai to 6pm,shima saboda Daddy baya da lafiya and alokacin nayi mana booking flights the next day muka bar kasar,Bayan na dawo nayi nemanki sosai amma ban same ki ba,,,Abu daya nake so na fada miki wanda zai fito daga cikin zuciyata Kuma zan fade shi koda kuwa ke bakya ra'ayin hakan....Uhmm ya sauke ajiyar zuciya sannan ahankali yace:
"Am deeply in love with you Hauwa'u"I love you with all my heart" yana kaiwa nan ya saki hannunta sannan ya tashi tsaye yace Ina so kibi abinda zuciyarki take so kada kiyi forcing dinta, Bissalam"
Juyawa yayi zai bar wajan sai yaji tace "Yaya Hafiz"( Jin sunan yasashi yana mamaki)
Ya juyo ahankali ya sake kallon ta yana son yaji ta kara kiranshi da wannan sunan, for how long suke tare da Hauwa'u bai taba jin ta kira sunanshi ba sai yau, yau dinma sai aka sakaya ya koma Yaya Hafiz, Yana cikin tunanin yaji tace Yaya Hafiz kadan zo please"
Ba shiri ya koma wajan ya zauna yace am back Hauwa'u"
"Jiddah ta soma wasa da yatsun hannunta sannan tace Dr.Rahul yace baza'a bude idanuna ba sai nan da kwana uku zuwa hudu, Yaya Hafiz Ina so ka zama mutum na farko da zan fara gani please ta hade hannayenta biyu alamar roko"
Sosai request dinta ya taba zuciyarshi ahankali yace HAUWA'U banga abinda zaki nema awaje na, na ki yi miki ba, da yardar Allah zan cika maki alkawarin ki.
Thank you"kawai ta fada sannan tayi shuru....ya dade zaune yana kallon ta kafin daga bisani ya fita waje fuskar shi cike da annuri, yasamu su Momma yai musu godiya sannan ya dubi Faisal yace oga baka gane niba ko?
Faisal yayi murmushi mai kayatarwa yace nagane ka mana, ai da ban gane ka ba, trust me bazan taba yadda ka ga Jiddah ba"but sanin ko kai waye awajan Jiddah shiyasa na barka ka shiga, Hafiz ya jinjina kai sannan yace toh Thank you for that.....ya samu waje ya zauna su Faisal da Momma na tambayan shi ko an fara yiwa granny aikin, inda shikuma yace musu eh an fara Amma ita kwana daya zatayi abude idanun,sukace to Allah yasa ayi a sa'a
Ameen Hafiz ya amsa, suna nan zaune sai ga Dr.Rahul Jay ya fito.
Yana fitowa kuwa, Hafiz da Faisal suka sameshi inda Dr. yayi musu bayanin angama aiki lafiya lau saura kuma budewa.
Faisal,Hafiz da Muhammad suka fita zuwa masallaci Momma kuma anan tayi sallan ta.
The next day haka suka hadu suna ta debe wa Hafiz kewa har aka bude idon granny, successfully aka bude sai gashi kuwa tana gani tangaran kuma tace mishi ta dena Jin ciwo ko kadan, ranar haka su Momma suka taru a ward din granny sai faman wasa da dariya sukeyi, Sosai Hafiz ya sake dasu kuma bai fito ya fada masu alakarshi da Jiddah ba atunaninshi basu sani ba, moreover yana da zurfin ciki, Momma kuwa tana lura dashi yakan leka ward din Jiddah jefi jefi idan ya fakaici idanun su, Kuma hakan bakaramin dadi yake yi mata ba dukda taso Jiddahn ta ta auri Faisal Amma bazatayi forcing Jiddah akan abinda bata so ba, shiyasa itama hankalinta ya karkata zuwa ga Hafiz din.
Wasa wasa shakuwar Hafiz da Faisal ko ince su ukun ma baki daya, shakuwar tasu ta zama abin sha'awa idan kaji yadda suke hira sai ka rantse sun dade da sanin juna.
"Hafiz yaso ya tambayi Faisal ya akayi Jiddah ta makance Amma yakasa sai kawai yayi shuru da bakinsa shi dai addu'a yake Allah yasa ta warke saboda ya cika mata alkawarin ta."

*************
Ranar Sunday
Itace ranar da za'a bude idanun Jiddah, Momma tun cikin dare ta tashi take ta faman Addu'o'i, kaman kuwa sun hada baki da Hafiz da granny suma dai tun 12am na dare suke faman Addu'o'i har wayewar asubahi.
Karfe takwas 8am tai musu a hospital, suna zazzaune cikin dakin suna jira lokaci yayi a bude idon, wayar Hafiz ya soma ringing,"ya daga Ogan sune cikin wayar akace Com.Hafiz Abubakar kana ina?
Hafiz yace oga ina hospital!
Please kazo yanzu akwai important issues ne.
"Ya ilahi!cewar Hafiz hankalinshi ya tashi,yace sir bazaka bari sai anjima ba,
"Yanzu nake son ganinka,yana kaiwa nan ya kashe wayar"yabar Hafiz da tunani barkatai aranshi, ranshi ya baci sosai...ya waiga ya kalli Faisal sai ya tsuke fuska yace oga nane yake nema na Kuma yanzun nan..... Faisal ya dan saci kallon Jiddah sai yaga kaman su take kallo dukdama baya da tabbacin taji abinda suke fada, duk da baisan plan dinsu ba Amma ganin yadda Hafiz ya dage akan yana nan za'a bude idannunta hakan yasa yace to ka jira a bude mata kafin ka tafi bro"Hafiz yace bari na samu Dr. tukun,yasamu Dr.Rahul yace Dr. please idan babu matsala kada abude a jirani yanzu zanje na dawo"
Dr.Rahul yace saura 1and half hour yanzu abude idon zaka iya tafiya amma kayi bitting time ka dawo da wuri so that kada muyi delay wani reaction ya fara shiga idon kuma.
Hafiz ya gyada kai cikin sauri sannan ya tafi bayan yayiwa Faisal da Muhammad sallama.
****
Jiddah na zaune ta jingina da pillow Momma na gefenta, tace Momma saura hour nawa abude idon?
"Saura hour daya da minti goma"
Jiddah ta gyada kai sannan ya Kuma cewa Momma naji kamshin turaren Yaya Hafiz dazu, amma ya banji muryar shi ba,
"Momma ta dubi Faisal tai masa alama da ido Ina Hafiz yaje?
Faisal yace yaje ya dawo"
Ahankali Momma ta kama hannun Jiddah tace Yaya Hafiz ya fita waje yanzunnan, Amma zai dawo kafin abude miki idanun.
Jiddah ta gyada kai tana gyara zamanta tace cikin sigar shagwaba Momma Yayanah fah da Ya Muhammad?
Momma tace gasucen zaune suna jira time yayi suga ana bude idanun little kanwar su.
Jiddah ta zumbure baki tace Momma kice su zo muyi hira"
Hakanan Momma ta girgiza kai ta waiga tace Muhammad kanwar ku na nemanku.,Muhammad yayi murmushi to which granny taga mugun kaman da sukayi da Jiddah, da sauri tace "Handsome" Amma Momma Muhammad yana kama da Jiddah sosai,"Momma tace eh ai Jiddah sak kamannin Muhammad ta dauko harda bakin fata "sai dai ta fishi kyau cewar Faisal ya fada alokacin fa yake kokarin zama a kujera kusa da Jiddah yana cewa My little girl hope you are fine?
ta noke kafada ta zumbure baki,
Ohohooooo shagwabar da ba'ayi na kwana biyu ba itace take shirin motsawa yau kuma?cewar Muhammad.
Faisal yace eh toh ina ruwanka ma!
Muhammad ya fashe da dariya sannan yace wannan mijin ki ya Shiga uku da shagwaba, nikam ma bana son mace mai shagwaba"
Jiddah ta zumbure baki kaman mai shirin yin kuka, ta bubbuga kafafu sannan tace Momma kina jin Yaya Muhammad ko"
Momma tace Jiddah hooooo to yi kuka ke da abin shagwaba baya kare miki, kai kuma ta nuna muhammad wlhy ka kiyayeni, kar ka sa na nemo maka mata wacce tafi Auta shagwaba!
Take Jiddah ta fara masa gwaliyooo dukda babu idanu amma se neman tsokana"
Granny tace nayi wa Handsome Mata ai, na bashi jikata Lema don da ita suka dace"
Sai alokacin Jiddah ta tuna cewa Muhammad yana son Leemarh, ita tama manta tace mishi ai granny din Leemarh ce Hafiz Kuma yayanta ne"
"Muhammad yadan shafa kanshi Yana murmushi yace to grannyn mu godiya nake sosai" Amma Ina fatan bata shagwaba kamar waccen mai kama dani din?
Granny tace ai ni gani nake ma kaman ciki daya suka fito wajan shagwaba da autan ci, saboda komai nasu iri daya ne.
Lokaci Daya Faisal ya kama dariya yana cewa Allah na gode maka, yauwa granny don Allah bamu address din muna komawa Nigeria zamu zo ayi maganar aure 😂
Momma tace gafara cen Elder brother baiyi aure ba taya kani zaiyi"
Muhammad yace ahhh tohh momma fada masa dai"
Haka sukai ta faman hira abinsu har Dr.Rahul ya shigo yace ku shirya saura 20min abude,
Ina Yaya Hafiz?Jiddah ta sake tambayar su"
Momma ta rasa me zatace mata sai granny tai charaf tace Jiddah yaje pharmacy siyomin magani yanzu zai dawo.
Ajiyar zuciya ta sauke,Dr.Rahul ya soma fara aikinsa na shirye shiryen cire mata bandage din yana yi yana duba agogo ,har karfe 12 saura min 10(goma), Dr. Yace we can't wait for him let get started nurses,"wani irin Kara Jiddah ta saki wanda ya razana dukkansu, tace da likitan kar ya kuskura ya fara sai Hafiz ya dawo"
Dr.Rahul da mamaki ya tsaya kallonta ya kalli Faisal yace wannan experiment din idan bamu cire shi akan lokaci ba wani reaction zai iya crossing ya bata mana results, so kuyi mata baya ni please saboda sai an cire ne zamu san ko aikin namu yayi.
Lallashinta Momma da Faisal suka somayi wanda da kyar ta bari aka fara cire bandage din, ta rigada ta sadakar da cewa ba Hafiz bane mutum na farko da zata fara gani don haka tuni zuciyarta ta fara mata zafi saboda karayar da tayi tana cewa meyasa Hafiz ya daukar mata alkawarin da bazai iya cikawa ba, moreover bai damu da lafiyar taba tunda gashi ya tafi, bai dawo ba kuma har time ya wuce.
Dr.Rahul yana ta cire bandage din ahankali har yazo round na karshe sannan yace don't open your eyes until I said so" Jiddah ta gyada kai shi kuma ya cigaba da cire wa...................😊bye✋

********************
Vote
Comment

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now