09

236 29 2
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/09
Mallakin DielaIbrahim

***********
Juma'at Mubarak🕌to you all👏
********
The following morning " Jiddah" bata jira yaya faisal ba tayi wucewarta hospital....ko daya fito yasamu momma zaune a palour gaishe ta yayi sannan ya nufi dakin Jiddah sai dai bai sameta ba ya fito ya duba kitchen nanma bata nan, Momma na kallonshi yana ta dube duben sa bata ce masa kala ba. Sai da ya gaji ya dawo palour yace Momma where's Jiddah?
Momma ta amsa masa kai tsaye "she left early today"
Faisal ya dan zare ido kadan alamar mamaki yace shine bata jirani ba Momma and kuma kika barta ta tafi ita kadai"
Momma ta dan kalle shi sannan tace ni kaina sai data gama shiri,sallama tamin kawai kuma ko abinci bata ci ba.......""ohhh Jiddah what wrong with her! Momma hada min breakfast dinta na kai mata, bai kamata ta fita batareda tasa wani abu a cikin ta ba.
"Uhmm indai Jiddah ce kada ka damu kanka "tana fita ta kirani tace zata ci abinci inshallah idan ta Isa hospital din"
Ya sauke ajiyar zuciya sannan yace Momma hada min nakai mata, fushi takeyi dani kuma ni bana so tana fushi dani.
Hakanan Momma ta tashi ta nufi kitchen ta hada breakfast a food flacks mai kyau ta mika masa hade da cewa good luck.
"Thank you Momma"sannan ya tafi cikin sauri.

Ranar batayiwa kowa magana ba ko Fatima ma tayi magana har ta gaji ta rabu da ita, itanan fah aganinta hakan ne zaisa taki haduwa da Hafiz Amma it turn out to be bad day for her as she thoughts..
Tana zaune a Phlebotomy babu patient sosai ranar,kawai sai gashi an kawo mata form har uku, guda biyu taje ward ta ansa sample daya kuma taje A&E, ta shirya komai a tray ta tafi with full of confidence and excitement, ward tafara zuwa ta gama sannan ta nufi A&E tana shiga gabanta ya fadi sakamakon jin kamshin turarenshi Wanda tun ranar da suka fara haduwa taji kamshin and from that day inta hadu dashi saitaji thesame scent na perfume din, ko data shiga bata tsaya kalle kalle ba sanin cewa yana cikin ward din sai kawai ta nufi wajan doctor ta nuna masu form tazo ansan blood sample take suka nuna mata patient din, tabi da idanunta direct inda matar take pointing.
Zaune yake kusa da patient din yana rubbing hannun patient,
ta maida idanunta kan patient din wanda yake kwance sanye da kakin sojojin army idanunsa a rufe, ta sake duba form din wajan da aka rubuta rank anan taga rank dinshi patient din wanda captain ne....ahankali ta nufi wajan fuska daure kaman bata taba dariya ba dan dimple din dayake fitowa ma ko shi ba'a gani, tana zuwa wajan sallama ta farayi Assalamualaikum!
Ya dago kai yana kallon ta muryar ta kadai yaji ya gane itace, amsa sallamar yayi ciki sannan ya maida kallonsa ga tray din hannunta ita kanta ma ba kallonshi takeyi ba patient ma take kallo abinta.....Hafiz yayi murmushi ya mika hannu ya amsa tray din, Handgloves ya sanya ya dauki tourniquet ya daure hannun patient din sannan ya soma kokarin Sanya masa 2ml syringe, "Jiddah tana kallon sa batace mashi komai ba, tana ganin yadda yadda aiwatar da aikin perfectly dama ya iya jan jini,har ya gama ya rubuta sunan a containers din sannan ya mika mata batareda yace komai ba..ganin ya gama ta amsa tray din zata tafi sai taji yace "Hauwa'u" come let me send you to my office please!"
Jiddah taji magana kaman daga sama,ita batasan dalilin daya sa yake kiranta da Hauwa'u ba although sunanta ne amma ayanzu rabon da wani ya kirata da sunan har ta manta sai dai Jiddah, gashi sunan yayi suiting din bakinshi sosai saboda aduk lokacin daya kira sunan saitaji wani abu aranta ta waiga tana cewa me?
"Yes you"ya bata amsa.
Haushi taji sosai aranta kaman  taki zuwa, hakanan ta dawo ta same shi aranta tana cewa badan halinka ba, don Allah nayi.....Shikam ko a kwalar rigarsa tana isowa yace mata taje office dinshi, zataga wata mata, please ki taimaka mata ki kaita Lab dinku FBS za'ayi mata, kice mata aiki ne yamin yawa anan and you will take care of everything.
Hakanan ta tafi tana tura baki gaba, har dawani cewa I'll take care of everything aikuwa zaigani, ko data kusan kaiwa ahanya ta iske course mate dinta, habawa sai kawai tabi su suka koma Lab dama ta taho da tray din samples din tana zuwa takai cikin Lab sannan ta koma wajan zaman ta, ta fara ansan samples,
Fatima ce tashigo tana ce mata, An kawo mata sako yana common room, batareda ta saurari me Jiddah zata fada ba tayi wucewarta.
'Jiddah tunda taga reaction din Fatima tasan lallai ta batawa besty rai, tayi sauri ta gama ta dau excuse kasancewar ba ita kadai bane a phleb din, zuwa tayi bench din Fatima ta janyo hannunta suka tafcommon room sai da suka zauna sannan tace" bestyna,teemah na,fushi kike da Jiddah?
Fatima tayi banza da ita tana danna wayarta, Jiddah ta fizge wayar sannan tayi fuskan tausayi tace please am sorry!
Fatima tace ya wuce ai karki damu bani wayana.
"Jiddah ta make shoulder tana cewa sai kin saki ranki tukunna"
Fatima tace na saki, bani
"No smile please"
Fatima ta bude hakwaranta ta hade su waje guda sannan tayi dariya kaman haka😬
Jiddah ta zare idanu😲tana cewa is this a smile haba bestyna bansanki da fushi ba fah!
Fatima ta harareta cikin wasa taja kunnanta tana cewa naughty girl zaki sake....Jiddah tayi kara kadan sannan tace am sorry ma'am fatima I'll never do it again"ta fada tana kallon ta "sai Fatima tace nooo not ma'am it's sister oyaaah say it har lokacin tana rike da kunnan" da sauri Jiddah tace am so sorry sister Jiddah ta fada tana hade hannayenta waje guda..........
Take kuma suka fashe da dariya suka rungume juna, "Jiddah na cewa Yaya Faisal ne ya bata min rai jiya" yau kuma bana so na hadu da wancan dan iyayin amma sai da na ganshi wallahi "what a bad day for me"
Fatima tace" really a bad day gaskiya" tayi dariya sannan tace ai Yaya Faisal breakfast ya kawo maki kuma yace in tabbatar kin ci saboda bakiyi breakfast ba....and shi kuma wancan kada ki damu dashi ba tashi muke ba kinji" Jiddah ta gyada kai tanamurmushi sannan tace Allah sarki Yaya Faisal ya wanke kanshi tunda ya kawo min abinci kaman yasan ina jin yunwa,Ina abincin toh?
Fatima ta dauko suka zauna sukaci golden yam with egg sauce, samosa sai kunun tsamiya, suna ci suna hira harda shewa suna gamawa suka bar common room din.
Fatima ce ta fara yin gaba Jiddah na baya bata ankara ba taga mutum tsaye gaban ta yana kallon cikin idanunta.
Jiddah kaman zata juya ta koma cikin common room amma ba hali, hakan yasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta....azuciyarta kuma ta tanadi maganganun da zata watsa masa matukar ya fada mata ba dadi. minti biyar kacal yadauka yana kallonta batareda yace kala ba, "Jin shurun yayi yawa yasa ta dago kai ahankali ta kalle shi, sai daga ita din yake kallo.......tace malam lafiya?
"Hafiz yace me kika gani ya tambaya?
"Jiddah ta tura baki gaba tana cewa ka tsareni da ido kaman kabani ajiya na cinye"
Dariya sosai tabawa Hafiz amma sai ya daure fuska  sannan yace me nace miki dazu, ba aikenki nayi ba?
"Yes aike na kayi amma ai ahanya ta na zuwa aka aiko kirana shine na taho abuna"tana magana tana juya idanu
"Hafiz yana kallon yadda takeyi da karamin bakinta, idan tana masifa ba karamin kyau takeyi ba tuni ya shagala da kallon kyakkawar fuskarta, "Jiddah ta kutsa zata bar wajan sai taji magana kusa kusa da kunnan ta yace "am not done with you yet" stay back!
"Jiddah taji maganan har cikin jinin jikinta amma sai ta basar ta wuce without saying a word,binta yayi da kallo har ta kure wa idanunsa,ayayinda zuciyarshi take mashi wani magana daban.....yana tambayan kansa meyasa yakejin farin ciki aduk lokacin daya ganta, meyasa zuciyarshi ke tunzura shi akan impossible to be possible, could this thing that am doing called LOVE or what? No no nooooo it can't be possible yayi saurin barin wajan ya koma office ya taho da Mom yana bata hakuri akan aiki ne sukai mashi yawa Amma yanzu he is here for her!
Har suka isa Lab din yamata komai aka bata form ya shigar da ita phleb, Jiddah ce kadai so aje form din yayi tareda gyara kujera yana cewa Mom zauna anan,
"Mom ta zauna hade da kallon Jiddah wacce idanuwanta a rufe suke batamasan da mutane awajan ba don da alama bacci takeyi.
"Hafiz yayi knocking kujeran Jiddah" firgigit ta fadi lokaci daya taji nauyin matar,....sai kawai ta tsinci kanta dacewa "Ina kwana Mama""Jiddah ta kira ta da Mama ne saboda tasan matar ta Isa ta haifeta" ta gaishe ta cike da ladabi idanuwanta da fuskarta suna kallon kasa" to which hakan datayi shi ya birge Mom yarinyar ta shiga ranta lokaci daya ta saki murmushi tana amsa gaisuwar tace lafiya lau, ya aiki.
Alhamdulillah Mama ya karfin jiki?
"Jiki Alhamdulillah Daughter"(Mom ta tsinci kanta da kiran Jiddah as Daughter)
Jiddah tace Mama me za'ayi miki ta tambaya batareda ta kalli Hafiz ba saboda ba taso ta shiga harkarshi ko kadan" Mama tace FBS za'ayi min zan samu yau kuwa?
Jiddah tace yes inshallah ai fasting blood Sugar baya jimawa zan rubuta urgently a form din and zan jira har ayi maki, Amma zaki iya jira ko"
Mom tayi murmushi tace me zai ha na Daughter I'll wait,thanks much dear
Jiddah tayi shuru saboda nau yin matar da take ji aranta"( Ni ko Diela nace su Jiddah dama ana ladabi irin haka kodai don taga sarukuwarta ne😂)"
"Hafiz dai ya zama Dan kallo, hakanan ya lura Jiddah bata ko kallon inda yake, ita kuma Mom saboda tasa mu yarinya shine ta manta dashi awajan"
Jiddah na gamawa ta ce Mama zaki iya jira a reception bari na shigar da forms din"
Okay Mom ta amsa adaidai lokacin data tashi tana yima Hafiz magana, tace son bari na jira sai na kai ma doctor ya duba kawai ayau koh,
Hafiz yace eh hakan yayi Mom, muje reception din ko mu jira acen.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now