02

564 42 1
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/02
Not-edited

____________________________________
Katsina State, Jibiya town
10th of August,1998

Da yammane misalin 5pm ruwan sama ne akeyi kaman da bakin kwarya, awannan lokacin ne muka nufi Katsina State cikin Jibiya town cen border din Nijar,
Nan muka leka General hospital wanda duk mutanen garin suke kira da Asibitin Hayin Gada, Asibitin Hayin Gada babban asibiti ne acikin Jibiya wanda yayi fice a wannan gari dakuma gefe gefen kauyukan dake kusa da Jibiya.

Bangaren dakin haihuwa nan muka dosa, Outside the ward alokacin ruwan saman ya dauke rana kuma ta fito lokaci daya tana shirin faduwa ta yamma wajan yayi haske kaman ba'ayi ruwa ba hakanan Kuma garin yayi lugub lugub ga sanyi mai dadi tuni kuma mutane suka fara harkan gaban su, anan na hango matar mai kimanin shekaru talatin cur aduniya dauke da tsohon ciki wanda gani daya zakai ma cikin dake jikin ta kasan irin zazzagowan dayayi, kaman zai fado kasa, tana ta faman tafiya, da alama exercise takeyi wanda sai zagaye building din takeyi cikin karfin hali da jajircewa, Bakar mace ce, doguwa amma zubin fulani take dashi tana kuma Sanye da maroon din hijab har kasa sai dan Atampha da ake iya hangowa daga kasan hijab din kallo daya zakai mata ka tabbatar da wahalan da tasha, kuma da alama she is in pain.
Kasancewar duk haihuwa haka take shan wahalan nakuda kafin ta haihu, sanin yanda nakuda ke zuwa Mata yasa Bata damuwa Amma wannan haihuwar yafi bata wahala,komai ya canja mata tsahon kwana biyu kenan tana fama sabanin wasu ayini guda suke nakudar tasu hade da haihuwa......ta cije baki tana kara dafa bayanta tana cigaba da tafiya......... wasu mata dake rumfar bishiyar bedi katuwa da alama jinya sukeyi, dukda anyi ruwa amma saida suka fito waje,se faman surutu sukeyi lokaci daya kuma suka dawo kan matar.

Wata Mata mai zubin yan kyauye zaune daga gefe take cewa, ohhh ni wannan yarinya tasha wahala yaufa zagayen data yi zaikai akalla sau goma sha, saboda tun safe takeyi tana hutawa, ke kam lami ba dole ba " inji wata agefen ta" tace nifa yanda naji tun jiya aka kawota cikin dare alokacin nurses sun dauka haihuwar ce to amma ko da suka dubata sai akace dasauran ta, domin bakin mahaifarta ta baikarasa budewa ba to shine fa har yau take ta fama....To meya hana taje gida tunda bakin mahaifar bata karasa budewa ba Cewar wata mata wacce ta kasa kunne tana sauraron su, Ohhhoo kema ae kyafada wallahi innice kam gida nayi don bazan tsaya naita  shan wahala ba. Yooo to wahala mana, inba wahala ba taya zanzo haihuwa, adubani acemani mahaifata bata bude ba, sannan kuma na cigaba da zaman asibiti Ina shan wahala.....Ohhhh ni shatu "wata stohuwa ta capke takuma katse masu hiran dasukeyi" waishin ku bakuda aiki sai dai ku zauna kuyita dimi da mutane, wallahi ko babu kyau abunda kukeyi, mike naku idan batai tahiyar ta gida ba, cen tajiyo abinta, kudai kujji da naku 'ya'yan da kuka kawo..Nan take wajan yayi tsit,kowa yakama harkan gabansa....dukdama basuji dadin katse masu hiran da akayi ba.

Cikin ciwo da dauriya ta zagaya tabayan building din...inda anan ta nufi wata bakar jeep, kana iya hango mutanen dake cikin motar.

Batakai ga karasawa ba wasu yara kyawawa maza guda biyu suka yo kanta da gudu suna fadin Ummi Ummi Ummi....rungumeta sukayi , ita kuma ta fara shafa bayansu ahankali tayi kewan yaran nata, ji takeyi kaman zata mutu tabarsu awannan lokacin, dauriya kawai takeyi, jansu tayi ajikin ta suka nufi motar.

Mama sannu ku,
Ah Ah ke keda sannu Halimatu, ai kinsha wahala nakudar yini guda sannu koh.
Yauwa Mama ki dauko kayan haihuwan muje ko......mama tace  okay muje toh.

Sai alokacin dayar matar dake zaune kusa da mama tace ya jikin Halimatu
Da sauki tace Ammi,Ammi please kikaramin rubutun mana don Allah....ta karashe maganar tana hade hannayenta waje guda alamar roko.

Ammi da bata son ganin 'yar tata cikin wahala daurewa kawai takeyi....ta dauko goran ruwan rubutu ta mika wa Mama sannan tace ta tabbatar tayi bissimillah kafin tasha..... Ammi ta janyo yaran da suke niyan bin bayan Ummin nasu tana cewa idan kuka bi Ummi to nurse zatai maku allura,ko kuna son allura ne?

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now