28

159 14 9
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/08

ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

__________________________________
Assalamualaikum
Barkanku dai Fans Ina fatan kuna lafiya" hope ban bata maku rai ba kunji shurun yayi yawa, Allah ya huci zuciyar ku, Allah ya sakama maku fa Alkahiri akan karanta story dina da kuke yi"
"Thank you once again"
************
Idan masu karatu basu manta ba mun tsaya a part 2/07 Asibitin Algarkawi inda masu karatu suna ganin dai gashi Jiddah zata samu cikar burinta, zata auri Hafiz Abubakar, sai dai abinda bamu sani ba shine dukkan abinda kuka karanta tun daga part 1/03 zuwa part 2/07 toh fah labari ne ake bamu wanda ba kowa ke bada labarin nan ba sai Hauwa'u Jiddah Junaid wacce take kwance a gadan asibiti, Barau Dikko Teaching Hospital dake kan titin yakubu gowon way cikin jihar kaduna.
Ina kaiku masu karatu😄 a labarin da kuka karanta muna shekara ta dubu biyu da goma sha tara (2019) wanda ayanzu kuma muna shekara ta dubu biyu da ashirin da daya (2021) January.
Asalin Labari😊muje zuwa dai bazaku bata ba matukar kuna biye da DielaIbrahim acikin littafin RAYUWAR JIDDAH to ahankali zaku fahimci inda Diela ta dosa.

____________________________________
BARAU DIKKO TEACHING HOSPITAL (Nursing home)
3rd January,2021

Jiddah zaune saman gadon marasa lafiya ta jingina da pillow kan karfen gadon an rufe mata jiki tun daga kafarta har zuwa saman kirjinta, hannayenta ne a waje sai fuskarta, dukdama suna da yawa a ward din, Amma babu ruwan wani da wani kasancewar an rufe wajan da karfe mai hade da labule.

Jiddah ta zubar da hawayen da suka zubo mata masu zafi ta kalli Fatima wacce take ta faman jijjiga baby girl tana kuka" ahankali Jiddah  tace little Jiddah takiyin shuru gashi ban karasa bawa "DielaIbrahim" labarin danake bata ba, ta kuma cewa Fatima kawo ta nan kiga, ta amshi babyn da aka kira da little Jiddah, sannan ta soma jijjiga babyn tana cewa Dadynta ya fiki iya raino Fatima da Yaya Faisal ne da yanzu kuwa tayi shuru nan da nan Little Jiddah tayi shuru abinta harda bacci ma tayi ajikin Jiddah.

Anan na fahimci ashe Fatima da Faisal sunyi aure sa'annan har sun haifi 'ya mace kuma suka sanya mata "Hauwa'u Jiddah"sunyi ma Jiddar mu takwara😃
Nidai Diela Ina tabin wajan da idanu nakasa yin tambayar komai sakamakon kaina daya d'aure, saboda yadda labarin yazo min na kuma kasa fahimtar labarin, na soma tambayar Jiddah Ina cewa ,  -Shin meya faru dun daga wannan ranar, "Jiddah"
- Ina Hafiz?
- Ina Momma
- Ina Ummi da Abba
- Ina Ammi da Mama
- Ina Muhammad, Leemarh, Saifullah da granny Ina Da.......kafin na karasa tambaya ta, Jiddah tai saurin toshe min baki da hannunta tace Shihhhiiiiiii 🤫
Tamabayoyinki suna da amsoshi kuma nan bada jimawa kadan ba zaki samu amsoshinki.

Muna nan zaune sai mukaji sallaman mutane sun shigo cikin ward din, Jiddah tace yauwa kalli ce Diela" ko dana kalli wajan sai naga mutane dayawa suna tahowa inda muke, Jiddah tace tsofaffi guda ukun dake gefe sune 
Ammi, Mama da Granny"
Kalli gefe kuma kinga wa dincen da suka rike hannu Mom da Ummi kenan bayan su kuma Daddy (Abban Hafiz) gefen Daddy kuma Saifullah da Muhammad sai Lady din data rike baby boy ahannu itace Leemarh rana daya akayi auran dana Fatima (sunan babynta Junaid" wato sunan Abba aka sanya Masa), sai waccen dattijuwar mace mai innocent face itace Momma gefenta kuma Mai sanye da kakin police force shine Yaya Faisal d'ina" Jiddah ta sauke numfashi ahankali ta kalle ni(Diela) tai murmushi tace nasan har yanzu baki fahimta ba ko, acikin tambayar da kikaimin mutum biyu ne babu awajan Abba da kuma Yaya Hafiz "masoyina" na gyada kai abuna Ina sake rubuta abinda kunnuwa na suke jiye min.

Muna nan zaune suka iso wajan nan na gaggaisa da kowa sannan suka fara raha atsakaninsu, a hirin nasu na fahimci sun matukar damu da halin da Jiddah take ciki wanda har yau Ni DielaIbrahim bansan miye asalin abinda ke damun Jiddah ba, haka dai naji Ummi da Mom da Momma suna rige rigen Wanda zai kwana da Jiddah, a iya fahimta ta na fahimci kowa dai so yake ya kyautata wa Jiddah, kuma kowannensu so yake ya sanyata farinciki har daga karshe Ammi ta yanke wanda zai kwana da ita  bakowa bace illah Momma, abin mamaki ko ince abin sha'awa ganin Momma nayi tana murna harda rungume Jiddah da Ammi tana sumbatar forehead dinsu" wai dan saboda zata kwana ta kula da d'iyar ta, bayan kowa ya tafi ne wajan ya rage Momma,Faisal, Fatima sai Saifullah da Leemarh sai dare zasu tafi subar Momma ta kwana da Jiddah, Awannan lokacin duk suka fita waje sukayi excusing dinmu kasancewar Ina bukatar a karasa min labarin kuma nasan masu karatu sun kagu suma suji abinda ya faru.

*Too short amma kuyi hakuri*

Ku kasance da DielaIbrahim a update masu zuwa inda zakuji karashen labarin "RAYUWAR JIDDAH "

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

FANs har yau dai Ina mai baku hakurin rashin jina akan lokaci, wayata ce ta samu matsala, toh danayi fixing komai kuma sai naga yakamata na karasa labarin duka.

Nima Ina son naga Ina update kullin Amma phone d'ina yana dan matsala ne.... Ina so ku cigaba da hakuri kuna bibiya ta insha Allahu zaku ringa jina ❤️

Thank you🙏❤️

RAYUWAR JIDDAH ✔Kde žijí příběhy. Začni objevovat